Sahun farko na maniyyatan Sakkwato sun sauka a Madina 

Jirgin kamfanin UMZA, ya tashi da misalin ƙarfe 6:21 na safe ɗauke da maniyyata maza 304 da mata 180 daga ƙananan hukumomin Tambuwal da Tureta da Wamakko da Sabon Birni da Isa da Shagari da kuma Dange/Shuni.

Sahun farko na maniyyatan Sakkwato sun sauka a Madina 

Rukunin farko na maniyyatan Jihar Sakkwato da za su gudanar da aikin Hajjin bana sun isa birnin Madina da ke Ƙasar Saudiyya.

Da sanyin safiyar Litinin ɗin nan maniyyatan, su 484 suka tashi daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sultan Abubakar na III da ke Sakkwato zuwa birnin Madina.

Jirgin kamfanin UMZA, ya tashi da misalin ƙarfe 6:21 na safe ɗauke da maniyyata maza 304 da mata 180 daga ƙananan hukumomin Tambuwal da Tureta da Wamakko da Sabon Birni da Isa da Shagari da kuma Dange/Shuni.

Da yake jawabi a filin jirgin kafin tashinsu, Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu Sakkwato, wanda mataimakinsa Idris Muhammad Gobir ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta samar da dukkanin shirye-shiryen da suka dace domin jin daɗi da tsaron lafiyar maniyyatan.

Ya buƙace su da su wakilci jihar yadda ya kamata, yana mai cewa al’ummar Sakkwato sanannu ne da ladabi da zaman lafiya da kuma biyayya ga doka a duk inda suka je.

Gwamnan ya tunatar da su cewa aikin Hajji tafiya ce ta ibada da ke buƙatar haƙuri da tawali’u da kuma bin koyarwar addinin Musulunci.

Haka kuma ya roƙe su da su yi addu’ar zaman lafiya da ci-gaban Jihar Sakkwato da Najeriya baki ɗaya.

Shi ma a jawabinsa, Amirul Hajj kuma Shugaban Kwamitin Hajji na Jihar Sakkwato, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyaɗi, ya bayyana gamsuwarsa da yadda shirye-shiryen suka gudana, yana mai cewa an kammala dukkanin tanade-tanaden da ake buƙata domin gudanar da aikin cikin nasara.

Dingyaɗi, wanda shi ne Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, ya ce an tura kwamitoci daban-daban domin kula da sufuri da ciyarwa da masauki da sauran ayyuka a Najeriya da kuma Saudiyya.

Ya ce jihar za ta gudanar da jirage guda biyar domin jigilar maniyyata 2,404 na bana.

A cewarsa, an kammala dukkanin shirye-shiryen filin jirgin da sauran dabaru domin tafiyar ta gudana cikin sauƙi.

Ya kuma buƙaci maniyyatan da su mutunta dokokin Ƙasar Saudiyya tare da gudanar da kansu bisa koyarwar addinin Musulunci, yana mai jaddada cewa tafiyar Hajji na buƙatar ladabi da haƙuri tun daga farko har ƙarshe.