Sai an bani Naira biliyan 1 zan bada shaida a kan Metuh-Jonathan

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar tilasta masa ya bayar da bahasi dangane da shari’ar da ake yi wa tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Olisa Metuh. Jonathan ya nemi kotun ta baiwa Metuh ummarnin bashi Naira biliyan daya na kudin tafiye-tafiyensa […]

Sai an bani Naira biliyan 1 zan bada shaida a kan Metuh-Jonathan

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar tilasta masa ya bayar da bahasi dangane da shari’ar da ake yi wa tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Olisa Metuh.
Jonathan ya nemi kotun ta baiwa Metuh ummarnin bashi Naira biliyan daya na kudin tafiye-tafiyensa da kudin daukar nauyin jami’an tsaronsa daga garinsu na Otuoke na jihar Bayelsa zuwa garin Abuja da kuma kudin dawainiyoyin da zai yi na tsawon lokacin da zai rika zuwa kotun a matsayinsa na shugaban kasar Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015.