Sai an karanci tarihin Annabi za a fahimci addini yadda ya kamata — Sheikh Ibrahim Khalil
Malamin ya ce wajibi ne malamai da masu neman ilimi su ba wa karatun sirar Annabi muhimmanci.
Fitaccen malamin addini a Najeriya, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce duk wanda bai karanta kuma bai fahimci sirar Annabi Muhammad (SAW) ba, ba zai iya fahimtar addinin Musulunci daidai yadda ya kamata ba.
Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin shirin A Wata Mahanga, wani shiri da wasu masana daga Arewacin Najeriya suka ƙaddamar domin wayar da kan al’ummar Hausawa da sauran al’ummar Arewa kan muhimman batutuwan da suka shafi addini da zamantakewa.
- Rasha ta harba makamai masu linzami fiye da 40 kan Kyiv — Zelensky
- An ceto mage daga ɓaraguzan gini bayan girgizar ƙasa a Venezuela
Malamin ya ce wajibi ne malamai da masu neman ilimi su ba wa karatun sirar Annabi muhimmanci, domin a cewarsa ita ce tubalin fahimtar addini da kuma gyaran tunanin matasa.
“Duk wanda bai karanta tarihin Annabi (SAW) ba, to ba zai iya ɗabbaƙa addini yadda ya kamata ba,” in ji shi.