Sai an kau da kai ake sare tofa
Sanin kowane kasar nan ta kusa nutsewa cikin koramar rashawa da cin hanci da kuma ha’inci, wanda ya dade yana gudana, an kuma fahimci babu wani sashe ko wasu harkokinta da wadancan miyagun al’amuran ba su shafa ba. Amma wuraren da rashawa da ha’inci suka fi yin katutu su ne gidan soja da kuma ofisoshin […]
Sanin kowane kasar nan ta kusa nutsewa cikin koramar rashawa da cin hanci da kuma ha’inci, wanda ya dade yana gudana, an kuma fahimci babu wani sashe ko wasu harkokinta da wadancan miyagun al’amuran ba su shafa ba. Amma wuraren da rashawa da ha’inci suka fi yin katutu su ne gidan soja da kuma ofisoshin manyan jami’an gwamnatocin tarayya da na jihohi. Babbar hujjar da ta tabbatar da haka kuwa, ita ce, yadda binciken da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara ya bankado tsananin ha’inci da almundahar fitar hankali da manyan hafsoshin rundunonin mayakan kasar nan suka tafka, musamman ma zamanin gwamnatin da ta shude, wacce ta ba su damar sace makudan kudin da aka tanada domin sayen makaman tsare lafiya da dukiyoyin talakawan kasar nan, wadanda daga farko aka kiyasta a kan Dala miliyan dubu biyu da dari biyar, amma sai daga bisani aka fahimci sun kai Dala miliyan dubu 15, kwatankwacin abin da gwamnatocin Najeriya suka kasafta, suka kuma batar a shekarar da ta gabata.
To idan kuwa haka ne ta yaya za a zaci cewa manyan hafsoshin mayakan kasar nan za su kare kasar daga kowane irin zalunci, na nan cikin gida ko kuma daga ketare, tun da dai su ma manyan azzalumai ne da zaluncinsu ya cutar da kasar, yake kuma kokarin kai ta ya baro? Anya kuwa irin wadannan manyan hafsoshin za su iya hukunta na kasa da su idan suka aikata ha’inci, kuma me za su ce da su idan har sun gane cewa su macuta ne?
Batun da ake ta yi na cewa wasu manyan hafsoshin rundunar mayakan sama sun yi almubazzaranci da wasu makudan kudin da suka yi rara wajen biyan albashin sojoji, ya isa a ce za a tuhumi manyan hafsoshin rundunonin soji, tun daga kan Janar Tukur Buratai har ya zuwa mai anini guda, don a tabbatar da gaskiyar lamarin. Ana dai iya cewa furuce-furuce da kuma kudurin Shugaba Buhari na ganin bayan rashawa a kasar nan da kuma takura wa wadanda suka daure mata gindi zai iya samun nasara ko kuma a gamu da akasin haka ta hanyar da ya tunkari batun zargin mallakan gidajen da aka ce Janar Buratai ya mallaka, tun da dai shi ma da kansa ya ce ya san da su, kuma nasa ne na kashin kansa. Hujjar da yake tinkaho da ita cewa, masu tayar da waccan maganar gidajen abokan hamayyarsa ne, wadanda ba su jin dadin nasarar da yake samu a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram, ladifiya ce ainun, kuma ba za ta fisshe shi ba, muddin ba cikakken bayani ya yi ba game da asali da salsalar dukiyar da ya sayi gidajen da su ba, duk kuwa da cewa ya bayyana kasancewarsu mallakansa ne yayin da yake fayyace abubuwa da kaddarorin da ya mallaka a matsayinsa na Kwamandan rundunar mayakan hadin gwiwar kasashe don yaki da Boko Haram da kuma bayan zamansa Hafsan Hafsoshin sojin kasar nan.
Babbar tambaya game da haka ita ce: a ina wani hafsan sojin da bai ajiye aiki ba, balle a ce ya karbi kudin giratuti na sallama daga aiki, sa’annan kuma yana karbar fenso, zai samu zunzurutun kudi haka, har Dalar Amurka miliyan guda da rabi, sai ka ce wani hamshakin dan kasuwa? Idan ban da albashinsa na wata-wata , wace sana’a kuma yake yi? To a ina ya samo su? Aikin soja abu ne da ke bukatar tsage gaskiya da rikon amana ta kowane fanni, kuma an tabbatar da cewa babu wani soja, karami ne ko babba, wanda ake ganin ya fi karfin bayar da cikakken bayani don kare kansa daga zargi, ko da kuwa shi ne Dogon Yaro, wanda ya fi kowa kwazo da bajimta fagen daga.
A wasu manyan kasashen duniya an sha samun lokutan da aka zargi manyan hafsoshin sojinsu, aka kuma yi musu hukunci mai tsanani saboda an tabbatar da zargin da aka yi a kansu game da aikata wasu abubuwan da ba su-ke-nan-ba. Shi ya sa shugabannin wadancan kasashen ba su yi wasa da zargin da ake yi wa manyan hafsoshinsu, domin kuwa sukan dage wajen ganin sojoji sun kame kansu daga barin aikata abin da zai zubar musu da mutunci, ko ya kai ga cin amanar kasa. Irin abin da ya kamata a ce Buhari na tabbatarwa ke nan, watau ya tsaya kai da fata, kamar yadda yake yi a wannan marrar, wajen yaki da ha’inci da zalunci da kuma masu assasa su kai tsaye, ba tare da bata wani lokaci ba. Haka nan tsohon Firayiministan kasar Singapore, Lee Kuan Yew ya yi ta dambarwa da ministocin kasarsa da kwamandojinta, wadanda ya tabbatar azzalumai ne, maciya amana, har sai da ya tsarkake kasar daga kazantar rashawa da ya kai ta ga yin kaurin suna. To amma wasu na ganin cewa yakin da Shugaba Buhari ke yi da rashawa na tafiyar sanda, domin a cewarsu akwai zargin da aka yi wa makararrabansa da aka ki bincikawa, kuma wacce aka yi wa Janar Buratai ta isa a ce an fara daukar matakan bincikawa don hankalin kowa ya kwanta.
Babu wani mahaluki a kasar nan da ya kai Shugaba Buhari kyamar rashawa da kuma fafatawa da ma’abotanta, kuma kowa ya san cewa ya lashi takobin magance illolin da ta haddasa a kasar nan, sa’ilin da yake neman amincewar talakawa don ya jagoranci kasarsa, sun kuma amince masa ba tare da turarrabin komai ba. To ashe kuwa idan haka ne babu wani dalilin da zai sa ya yi sako-sako da yakin da ya faro da rashawa da masu assasa ta, musamman ma wajen tunkarar na kurkusa da shi da ake zargin cewa da su a cikin badakalar tsiyata kasar nan.
Talakawa dai sun zura masa ido don ganin yadda zai yi da wadanda aka caccafke da kuma yadda dangantakarsa da wasu na hannun damansa za ta ci gaba da kasancewa bayan zargin ha’inci da zaluncin da aka yi musu daidai da alwashin da ya sha cewa, ba zai kyale dukkan azzalumin da aka zargo ba, ko da kuwa na hannun damansa ne. Shi ya sa wasu ke cewa wajibi ne ya fara da kawar da kariyar da Ma’aikatar Tsaro ta hanzarta bayarwa ga Janar Buratai game da sayen gidajen Dubai da ta ce ya yi da albashinsa, ya kuma sa a yi cikakken bincike na gaskiya, domin ba ita ce za ta ce da kudin albashinsa da ya ci ya rage ne ya sayi wadancan gidajen ba, tun da ba ita ce ke kashe masa su ba, ba kuma ita ce ke da susun da ya tara rarar kudin a ciki ba. Yanzu dai kallo ya koma sama, jama’a kuma cewa suke, ‘kaka-tsara-kaka.’