Sai an shekara 120 kafin Najeriya ta samu wadatattun likitoci

Ko da duk likitocin Najeriya su zauna a kasar su yi aiki sai an shekara 120 ba su wadata ba.

Sai an shekara 120 kafin Najeriya ta samu wadatattun likitoci

Ministan Ilimi, Adamu Adamu.

Ministan Ilmi, Malam Adamu Adamu, sai an shekara 120 daga yanzu kafin Najeriya ta samu wadatattun likitocin da take bukata, ko da kuwa duk likitocin kasar za su cigaba da aiki a cikin gida.

Ministan ya fadi haka ne a lokacin bikin rantsar da daliban farko na Jami’ar Kimiyyar da Fasahar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FUHSO) da ke Otukpo a Jihar Binuwai.

Wakiliyar ministan a taron, kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Arc. Sunny Echono, ta ce, “Bisa la’akari da yadda abubuwa ke tafiya a halin yanzu, sai Najeriya ta shekara 120 kafin ta iya samar wa kanta da yawan likitocin da take bukata, ko da kuwa duk likitocinmu za su zauna su yi aiki a cikin kasar.”

Ya kara da cewa samar da irin wannan jami’a ta kimiyya da fasahar kiwon lafiya zai zama ginshiki wajen kara yawan likitocin a Najeriya ta hanyar horarwa, bincike da kirkire-kirkire don samun ingantaccen ilmi.

A jawabinsa, Shugaban Jami’ar, Farfesa Innocent Ujah, ya ce FUHSO ita ce jami’ar gwamnatin tarayya ta farko a kimiyya da fasahar kiwon lafiya a Najeriya.

Ya kara da cewa, kafa jami’ar kamar cika wani babban buri ne da aka dade ana fatar ganin cikarsa.

A karshe Gwaman Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya ce yana alfahari da kafa jami’ar a jiharsa, sannan ya ba da tabbacin gwamnatin jihar za ta hada gwiwa da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya wajen tabbatar ingancin jami’ar.