Sai an yi kwas din zamantakewa za a yi aure a Saudiyya

Ma’aikatar Kyautata jin dadi da walwal ta Saudiyya za ta tursasa wa ma’aurata halartar kwas din aure, tun kafin su zama ma’aurata, kamar yadda jaridar Makkah daily ta ruwaito, inda majiyar jaridar ta bayyana cewa, a da akwai zabi ga mai son yin kwas akan kwarewar kan harkar zaman aure, a lokacin da ake gudanar […]

Sai an yi kwas din zamantakewa za a yi aure a Saudiyya
Sai an yi kwas din zamantakewa za a yi aure a Saudiyya

Ma’aikatar Kyautata jin dadi da walwal ta Saudiyya za ta tursasa wa ma’aurata halartar kwas din aure, tun kafin su zama ma’aurata, kamar yadda jaridar Makkah daily ta ruwaito, inda majiyar jaridar ta bayyana cewa, a da akwai zabi ga mai son yin kwas akan kwarewar kan harkar zaman aure, a lokacin da ake gudanar da kwasa-kwasan a cibiyoyi 459.

Ma’aikatar na shirin mayar da kwas din ya zama dole, snanan wadanda suka kamala samun horo a karkashin shirin za su smau shaidar kammala karatu. Kuma dole sai an gabatar da wannan shaidar kammala kwas din za a daura aure. Dalilinmu na yin haka shi ne, mu shawo kan yawan mutuwar aure a fadin daular (Saudiyya),” a cewar majiya.
Wannan shiri ya kunshi tarurrukan kara wa juna da ake gudanarwa a cibiyoyi 38, a karkashin kulawar kwmaitoci 390 na kyautatata jin dadin al’umma, da wasu kungiyoyin kula da kyautata aure d azamantakewar iyali a cikin al’ummomi; sannan shirin kyauta ne a duakacin fadin kasar. Wadannan tarururrukan kara wa juna ilimi za su bibiyi darussan da suka hada da mu’amala da addini da tsimi da tanadi da kyautata tunani da al’adu.
Shi kuwa mai Magana da yawun ma’aikatar, Khalid Al-Thubaiti cewa ya yi, kirkiro da wannan tsari, ya biyo bayan wani taro ne da majalisar ministan ma’aikatar ta gudanar, inda ma’aikatar ta yanke matsaya wajen kirkiro da shirin horarwa ga masu shirin yin aure.