Sai bango ya tsage
Salam, Edita da fatan kana lafiya, a yau na shigo wannan fili ne domin in yi tsokaci game da daruruwan al’ummar da suka shafi Najeriya masu yi wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari muguwar fata bisa jinya da yake yi a birnin Landon na kasar Ingila. Hakikanin gaskiya sai bango ya tsage kadangare ke samun mafaka, […]
Salam, Edita da fatan kana lafiya, a yau na shigo wannan fili ne domin in yi tsokaci game da daruruwan al’ummar da suka shafi Najeriya masu yi wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari muguwar fata bisa jinya da yake yi a birnin Landon na kasar Ingila. Hakikanin gaskiya sai bango ya tsage kadangare ke samun mafaka, duba da yanda dubbai daga cikinmu ‘yan Arewa suka zamo bara- gurbi suka kasance marasa kishi da karancin tunani. Bugu da kari kuma suka zama butullu bisa ni’imar da Allah Ya yi mana ta kawo mana wannan dattijon wanda ke neman sadaukar da ransa wajen nema wa talakan Najeriya farin ciki da jin dadi, amma sai gashi abun kunya da bakin ciki dan Najeriya ne sahun gaba wajen aibata wannan bawan Allah don kawai bambancin siyasa ko wata manufa ta daban. A karshe inason mu sani cewa ba zamu taba ganin muhimmancin shugaba Buhari ba sai ranar da Allah Ya yi masa cikawa, aka rantsar da mukaddashinsa a matsayin shugaban kasa, wallahi a lokacin ne za mu gane shayi ruwane!
Kuma bama fatar ganin wannan bakar ranar, Ya Allah ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen rokonka da ka kara wa wannan bawan naka lafiya da kwarin gwiiwa, amin.
Sako daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan Bore (dan kishin talaka) karamar
Hukumar mulki ta Gusau Jihar Zamfara. 07086868025