Sai bayan ba na nan za a ga amfanina – Jonathan
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya bugi kirjin cewa ’yan Najeriya za su fara yaba masa ne idan ya bar mulki wani ya kama shugabanci. Shugaba Jonathan yana magana ne a gidansa da ke fadar Shugaban kasa na Aso Rock a Abuja a ranar Talata, lokacin da ya karbi bakuncin wani ayarin sarakunan gargajiya da shugabanni […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya bugi kirjin cewa ’yan Najeriya za su fara yaba masa ne idan ya bar mulki wani ya kama shugabanci.
Shugaba Jonathan yana magana ne a gidansa da ke fadar Shugaban kasa na Aso Rock a Abuja a ranar Talata, lokacin da ya karbi bakuncin wani ayarin sarakunan gargajiya da shugabanni da suka suka fito daga jiharsa ta Bayelsa.
Shugaban kasar ya ce bay a jin mamakin jerin soke-soken da ake yi wa gwamnatinsa. Kuma ya ce zai ci gaba da gode wa ’yan Najeriya kan damar da suka ba shi na yi musu aiki, inda ya kara da cewa, “za mu ci gaba da yin bakin kokarinmu.”
Ya ce shugabannin a duk sassan duniya sukan yi fama da caccaka da suka da kafofin labarai na intanet suke dada yayatawa, inda ya ce ana amfani da haka ne don wasu manufofin da ba su dace ba.
Shugaba Jonathan ya ce ya gane mutane ba su cika yaba wa shugabanni nagari a lokacin da suke kan mulki ba, inda ya nanata cewa yana da tabbacin idan wata sabuwar gwamnati ta zo, jama’a za su auna kuma su yaba wa nasarprin da ya samu.
Y ace, “Na sha fadi cewa b azan tsammaci samun yabo a yanzu ba, saboda yana da wuya mutane su yabi shugabannin da keg ado. Lokacin da ka sauka ne jama’a za su fara sanin haka. Lokacin da ka sauka, jama’a za su fara auna ayyukan da ka yi a zamaninka da na sauran, sannan su kwatanta ka da wanda ya karbe ka. Kuma galibi a wannan lokaci ne mutane za su fara fadin alheri game da kai. Kuma zan ci gaba da yin kokarin tabbatar da mun canja abubuwa.”
Shugaba Jonathan ya ce, “Muna kokarin samar da yanayin da ya dace don inganta tattalin arzikinmu duk da matsalolin da muke fuskanta a fannin man fetur da matsalar tsaro da muke da ita. Zan yi iyakar kokarina ta yadda lokacin da zan bar mulki za ku iya cewa lokacin da danmu yake wurin ya yi wa kasa aiki yadda ya kamata, ta yadda wata rana za a ba dan Bayelsa damar bauta wa ’yan Najeriya.”
Shugaban kasar ya ce, maimakon soke-soke su kawar da hankalinsa, zai ci gaba da yin kokarin bauta wa kasarsa.
Jonathan ya kuma ce bana za ta kasance kalubale ga kasar nan, saboda zaben da ke tafe. “Sabuwar shekara cike take da kalubale ga ’yan Najeriya saboda zabe da ke tafe a farkonta. Ko’ina zai yi zafi daga 2 ga Janairu.”
Tunda farko Gwamna Seriake Dickson, wanda ya jagoranci ayarin ya ce sun je fadar ce don nuna goyon baya ga Jonathan da iyalansa a daidai wannan lokaci na bukukuwa. Daga nan sai ya mika katin murnar Kirsimeti ga Shugaban a madadin jihar, inda ya ba shi tabbacin cewa mutanen jihar za su ci gaba da ba shi goyon baya.