Sai bayan zabe Jonathan zai karrama ’yan kwallon Flying Eagles
Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi alkawarin karrama ’yan kwallon Najeriya Flying Eagles da suka lashe gasar cin kofin Afirka na matasa (African Youth Soccer Championship) a karo na bakwai a Senegal a ranar Lahadin da ta gabata. Sai dai mai taikawa Shugaban a wajen hulda da ’yan jarida da kuma aika sakonni Dokta […]

Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi alkawarin karrama ’yan kwallon Najeriya Flying Eagles da suka lashe gasar cin kofin Afirka na matasa (African Youth Soccer Championship) a karo na bakwai a Senegal a ranar Lahadin da ta gabata.
Sai dai mai taikawa Shugaban a wajen hulda da ’yan jarida da kuma aika sakonni Dokta Reuben Abati ya ce shugaban zai karrama ’yan kwallon ne bayan an kammala zabubbukan da ke tafe.
Abati ya ce tuni shugaban ya aika wa kungiyar sakon taya murna da kuma na fatan alheri bisa namijin kokarin da suka yi na lashe kofin a karo na bakwai. Kuma yana sa ran da zarar an kammala zabubbukan da ke tafe za a sa ranar da za a karrama su a Abuja.
Abati ya ce, tuni shugaba Jonathan ya shiga sahun miliyoyin ’yan Najeriya wajen nuna farin cikinsu a kan ’yan kwallon Flying Eagles musammanin gannin yadda suka daukaka martabar kasar nan a idon duniya.
Shugaban ya yi alkawarin mara musu baya wajen ganin ya biyan dukkan bukatunsu kafin da kuma lokacin da za su halarci gasar cin kofin duniya na matasa na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) da zai gudana a watan Yunin wannan shekara a New Zeland.
Najeriya Flying Eagles dai ta samu nasarar lashe kofin ne a karo na bakwai bayan ta lallasa Ghana da ci 1-0 a wasan karshe.