Sai Buhari ya yi tankade da rairaya a bangaren man fetur al’amura za su gyaru – Gambo Tuge

Kwamared Gambo Tuge, shi ne Jama’in Tsawatarwa na kungiyar Direbobin Dakon Man Fetur ta kasa, (PTD) kuma tsohon Shugaban kungiyar na Jihar Kaduna, a tattaunawarsa da Aminiya ya fasa kwai kan dalilan da suka sa matatar mai ta Kaduna ba ta aiki, inda ya ce, sai Shugaban kasa mai jiran gado Muhammadu Buhari ya yi […]

Sai Buhari ya yi tankade da rairaya a bangaren man fetur al’amura za su gyaru – Gambo Tuge
Sai Buhari ya yi tankade da rairaya a bangaren man fetur al’amura za su gyaru – Gambo Tuge

Kwamared Gambo Tuge, shi ne Jama’in Tsawatarwa na kungiyar Direbobin Dakon Man Fetur ta kasa, (PTD) kuma tsohon Shugaban kungiyar na Jihar Kaduna, a tattaunawarsa da Aminiya ya fasa kwai kan dalilan da suka sa matatar mai ta Kaduna ba ta aiki, inda ya ce, sai Shugaban kasa mai jiran gado Muhammadu Buhari ya yi tankade da rairaya kafin al’amura su gyaru a bangaren man fetur:

Aminiya: Tun yaushe ka fara harkar man fetur?

Gambo Tuge: Na fi shekara 20 ina wannan harka, lokacin da matatar Kaduna ke aiki gadan-gadan, lokacin ana sayar da duk ababen da ake tacewa kai -tsaye. Lokacin duk Arewa suna samun mai ne a wannan matata ta Kaduna. Kuma sai mota 500 su yi lodin man fetur da kanazir da dezel da man jirgin sama da kwalta da sauransu. Amma abin mamaki shi ne yadda wannan gwamnati mai barin gado ta Dokta Goodluck Jonathan, Minista Diezani Madueke ta jagoranci cin mutuncin Arewa inda aka hada da gurgunta harkar man fetur a matatun man Najeriya musamman ta Kaduna da ke nan Arewa. Domin an yi shekara biyu matatar mai ta Kaduna ba ta samu danyen man fetur ba. Mutane da yawa sun rasa hanyar cin abincinsu saboda gurgunta matatar da aka yi, kamar a daffo-daffon daukar man da ake turawa daga Kaduna, irin su daffon Maiduguri da Yola da Jos da Gusau da Kano da Suleja da kuma Minna. Wadannan daffo-daffo ba su taba yin lodin man fetur ba a shekara biyar da suka wuce. Dalilin shi ne akwai ’yan lelen da ake ba su mai sannan su kuma sa sayar da muguwar tsada ga al’umma. Wadannan ’yan lelen su ne suka yi karfi sannan suke shigo da tataccen man fetur cikin kasa, kuma ake ba su tallafi, wato ka ga riba-kan-riba ke nan. Wato an bata matatun man kasar nan ne don a rika shigo da mai, maimakon su ’yan lelen su gina matatun mai na kansu.
Don haka muna rokon zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya duba yadda ake cin amanar kasa a matatar man fetur ta Kaduna. Domin lallai ana cin duddugen kasa, inda wasu ’yan kalilan ke cin riba alhali gwamnati na kallo kiri-kiri. A yanzu duk wanda ya je matatar mai ta Kaduna zai ga kamar an yi yaki an gama, don ba wata harka a harabar matatar kamar yadda ake yi a da. Abin da kawai ya rage a yanzu shi ne yadda ake zuwa a sawo mai daga Kudu a wurin ’yan lele, wato manyan ’yan bumburutu sannan a yi dakonsa zuwa Arewa a sayar. Sannan masu lasisin harkar mai ba su da wani katabus sai dai yadda aka yi da su. Su wadancan ’yan bumburutu ke cin karensu babu babbaka. Abin da ake yi a Kamfanin Man fetur na kasa ya wuce minsharrin ya kai mahalaka.
Aminiya: Kamfanin Chiyoda na kasar Japan ya gina matatar mai ta Kaduna, amma aka ba Kamfanin Total na Faransa don ya yi masa garambawul, shin haka ya dace?
Gambo Tuge: Bai dace ba, domin kamar ka dauki malamin makaranta ne ka ba shi fidar mara lafiya a asibiti ka ce a tashi lafiya, sai dai a yi uwa-kwance-da-kwance. Domin haka lallai muna son a samu canji kan yadda al’amura suke tafiya a bangaren mai.
Aminiya: Don me wasu gidajen mai suke sayar da mai fiye da Naira 87?
Gambo Tuge: In da matatun mai na aiki, duk wanda ya kara kwabo fiye da kudin da gwamnati ta kayyade ba zai sayar da mai ba, domin ba wanda zai saya. Amma a wannan marra in dilan mai ya sayo mai fiye da Naira 100 a kasuwar bayan fage a Kudu, dole ya nemi riba. Amma in da matatun na aiki, duk mai gidan mai zai sayar yadda gwamnati ta kayyade, sannan ya kawata gidan man don ya ja ra’ayin masu saye. Amma in har dilan mai zai sayo a bayan fage, lallai shi ma ya sayar fiye da Naira 100 wasu har Naira 130.
Sannan saboda matatar Kaduna ba ta aiki ne ake sayar da kananzir ga ’yan lelen sanna su kuma su sayar ga masu gidan mai. A da mota daya tana lodin kananzir sau biyu a wuni. Amma a yanzu sai ka je Legas, Warri ko Fatakwal ka sayo a bayan fage sannan ka yi fitonsa zuwa Arewa, bayan ka sallami ma’aikata da ’yan taratsi kuma ga rashin kyan hanya da sauransu.
Aminiya: Me ya sa ba a daukar kwalta a matatar mai ta Kaduna?
Gambo Tuge: Dalili shi ne matatar man fetur ta Kaduna ba ta aiki. A baya ana neman masu sayen kwaltar har ana yi musu ragi, amma yanzu manyan ’yan bumburutu ke sayowa daga waje, lallai ana cin duddugen Najeriya da Arewa.
Aminiya: Yanzu wata nawa ke nan ba a tace mai a Kaduna ba?
Wata tara ke nan, in ta yi aiki na wata daya, sai ta daina kamar na wata tara. Haka ake tangal-tangal har tsawon shekara biyar.
Aminiya: A takaice kana nufin ma’aikatan kamfanin man na karbar albashi a bulus ke nan?
Gambo Tuge: Babbar matsalar ita ce yadda ake daukar ma’aikata da yawa a matsayin ’yan wucin-gadi ba na dindindin ba. Su wadannan leburori ne ke yin aikin sannan ma’aikata suna cin bulus. Kuma sai tura manyan ma’aikata ake yi kasashen waje ba gaira-ba-sabar don su yi kwas da sauransu, bayan kamfani na tsaye.
Aminiya: Shin Ministar Man fetur ta taba zuwa rangadi a matatar ta Kaduna?
Gambo Tuge: Minista Diezani Madueke ba ta taba zuwa matatar mai da ke Kaduna ba, sai dai a gan ta a kafafen wata labarai.
Aminiya: Mene ne mafita?
Gambo Tuge: Janar Muhammadu Buhari ya taba yin Ministan Man fetur da kuma Shugaban Hukumar Rarar Man fetur ta kasa (PTF), muna kira da ya binciki almundahanar da ake tafkawa a kamfani da matatun mai na kasa. A yi tankade da rairaya sannan a samar da masu kwatanta gaskiya su yi aikin. Ya dace ya yi aiki ne da masu gaskiya, domin kowa na cewa yana tare da shi, ya kamata ya kula sosai.
Aminiya: An gano mai a kasar Nijar, kana ganin ya dace a ci gaba da bincikar man fetur a Arewa?
Gambo Tuge: In dai har za a gano man fetur a Nijar, ya dace a binciko da kuma hako na Arewa, wannan zai hana yadda ’yan Kudu ke yi wa ’yan Arewa kallon hadarin kaji. Ya kamata a gayyato wadanda suka hako na Nijar don su hako na Najeriya.
Aminiya: Manyan motocin daukar mai da dama kan yi hadari, ya dace masu tuka motocin dakon man su rika jigila da daddare?
Aminiya: Laifi ne a cikin kundin tsarin mulkinmu direba ya tuka mota shake da mai da daddare. Domin ba hanyoyi masu kyau da kuma ga yawan ’yan fashi a hanya. Domin an taba sace motoci da mai a shataletalen Mando da ke Kaduna aka sayar a Kagoro, mai gidan man ya fallasa wadanda suka sayar masa da man amma hukuma ba ta yi komai ba. Sannan an saci wata a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtuwa.
In da akwai hanyoyi masu kyau masu hanya hurhudu daga Kaduna zuwa Legas, da ba a rika samun matsalar dakon man fetur ba. Amma gaskiya ita ce a gyara matatar mai ta Kaduna, a kuma gina wasu sababbi. Mun yi yawo a duniya, mun ga kasashe yadda suke cin ribar arzikinsu na man fetur, ya dace mu ma Najeriya mu guji zama na-baya-ga-dangi.