Sai da aka kashe Sardauna sannan aka gane alherin da ya shuka – dankaden Zazzau

Dankaden Zazzau kuma Hakimin Gabasawa, Alhaji Jibril Muhammed ya ce sai bayan da aka kashe marigayi Firimiyan Arewa Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato sannan jama’a suka fahimci alherinsa da ayyukan alherin da ya yi a zamaninsa. dankaden na Zazzau ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawarsa da manema labarai kan cika shekara 50 da […]

Sai da aka kashe Sardauna sannan aka gane alherin da ya shuka – dankaden Zazzau
Sai da aka kashe Sardauna sannan aka gane alherin da ya shuka – dankaden Zazzau

Dankaden Zazzau kuma Hakimin Gabasawa, Alhaji Jibril Muhammed ya ce sai bayan da aka kashe marigayi Firimiyan Arewa Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato sannan jama’a suka fahimci alherinsa da ayyukan alherin da ya yi a zamaninsa.
dankaden na Zazzau ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawarsa da manema labarai kan cika shekara 50 da kashe Sa Ahmadu Bello Sardauna a juyin mulkin 1966 a Kaduna.
Ya ce a lokacin da aka kashe Sardauna yawancin mutane suna ta murna, wasu ma har sun zuba ruwa a kasa sun sha. “Marigayi Malam Aminu Kano ne ya fito ya ce abin da ya faru ga marigayin ba abin murna ba ne, abin bakin ciki ne. Ya kuma ce wannan abin da ya samu Sardauna ba shi kadai ya sama ba, nan gaba sai ya shafi duk wani mutumin Arewa,” inji shi.
dankaden ya ce kashe sardauna mutane suna ganin kamar wani ci gaba ne amma daga baya an gane Sardauna shugaba ne da jama’ar Arewa ke matukar sonsa domin daga baya an gane alheri yake nema da su kuma an yi babban hasara da rasuwarsa.
“Tun bayan gwamnatin Sardauna babu wata gwamnati da za a ce ta yi kokarin taimaka wa talakawa, sai dama-dama gwamnatin Shehu Shagari. Lokacin Shagari wanda ba ya da gida ya yi gida, wanda ba ya da mota ya yi mota. Daga baya wadanda suke ganin su za su iya gyara Najeriya suka yi masa juyin mulki shi kuwa Shagari ya ja da baya har zuwa yanzun nan babu inda talaka zai ce ya samu ya huta,” inji shi.
Hakimin ya shawarci ’yan Najeriya, musamman shugabanni su yi koyi da halayen marigayi Sardauna na rikon amana da tsoron Allah tare da yin mulki cikin adalci ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.
Ya ce, akwai bukatar duk wani dan Najeriya ya rika tsoron Allah domin ko ba jima ko ba dade zai koma wajen Mahaliccinsa.
Game da ko za a iya samun mai halayen Sardauna a yankin Arewa sai ya ce “Gaskiya samun mai irin halayen Sardauna zai yi wuya, domin shi mutum ne mai kaunar Arewa da jama’arta. Ba kuma ruwansa da bambancin addini ko kabilanci. Sannan babu ruwansa da son tara dukiya.”
Ya ce a lokacin da aka kashe shi ina cikin tuka mota, na ga lokacin da aka dauko gawarsa da na matarsa a wata mota. A lokacin kafin ka ce kwabo kofar gidansa da ke ci da wuta ya cika da jama’a musamman mutanen Unguwar Shanu.
Ya shawarci matasa su daure su nemi ilimin addini da na boko domin su ne gishin zaman duniya da Lahira.