Sai da katin shaida dan Arewa zai yi kasuwanci a Imo

Gwamnatin Jihar Imo za ta tantance daukacin ’yan Arewa da ke hada-hadar kasuwanci a jihar tare da ba kowannensu katin shaida, a cewar Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar kan al’amuran da suka shafi ’yan Arewa, Faisal Lawal.Faisal, wanda ya bayyana wa Aminiya haka a Owerri babban birnin jihar, ya ce ana gudanar da […]

Sai da katin shaida dan Arewa zai yi kasuwanci a Imo
Sai da katin shaida dan Arewa zai yi kasuwanci a Imo

Gwamnatin Jihar Imo za ta tantance daukacin ’yan Arewa da ke hada-hadar kasuwanci a jihar tare da ba kowannensu katin shaida, a cewar Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar kan al’amuran da suka shafi ’yan Arewa, Faisal Lawal.
Faisal, wanda ya bayyana wa Aminiya haka a Owerri babban birnin jihar, ya ce ana gudanar da tantancewar ne a karkashin kulawar ofishinsa, don tabbatar da cewa kowane dan Arewa da ke kasuwanci a jihar an san da zamansa, sannan ya ce wannan shirin zai shafi har masu aikin gadi a daukacin fadin jihar.
Wannan shirin tantancewar, a cewar mataki na musamman ga gwamnan, yana karkashin wani shiri da gwamnan jihar ya yi ikrarin fito da shi ne mai taken: “Ku san makwabtanku,” kuma al’amarin ya biyo bayan wani bom da aka gano a wani coci ne da ke Owerri.
Ya ce ana tantance mutanen ne domin sanin sunan mutum da jiharsa ta asali da irin kasuwancinsa, tare da sa hannun shugaban kungiyar masu sana’a irin tasa da wurin da yake yin sana’ar. Inda ya bayyana cewa da zarar an kammala tantancewar za a bai wa mutum katin shaida mai dauke da hotonsa da sa hannun shugaban kungiyar masu sana’a irin tasa da kuma sarki.
Ya bayar da tabbacin cewa a karshen wannan aiki, kowane dan Arewa zai kasance an tattara bayanai a kansa. Sannan ya tuno da gargagadin da Gwamnan Jihar Rochas Okorocha ya yi wa ’yan kasuwa ’yan Arewa kan su daina shiga jihar da kayansu cikin dare.
Lawal Faisal ya ce, ’yan Arewa da dama suna zaune a wannan jihar fiye da shekara 100 da ta wuce, don haka ya bayar da tabbacin cewa kowane dan Arewa yana da sana’ar da yake yi, sabanin a ce yana yi wa al’umma ta’addanci.
 Alhaji Shehu Kwanti,  shugaban ’yan Arewa mazauna Jihar Imo ya bayyana wa Aminiya cewa yi wa ’yan Arewa, mazauna jihar da ke gudanar da sana’o’in yankan farce da wanke takalma da kuma sauran hada-hadar kasuwanci, katin shaidar da zai nuna inda mutum ya fito da irin sana’ar da yake yi har ma da jiharsa ta asali da ya fito ba shi a cikin tsarin mulkin Nijeriya.
Duk da cewa ya ki yarda ya fadi yawan kudin da ake karba hannun mutum kafin a ba shi takardar da zai cika, wato fom, amma ya tabbatar da cewa ’yan Arewar suna tururuwa suna yin katin domin su tsira da mutuncinsu.
Shugaban ya kuma nuna damuwarsa da yadda ’yan asalin jihar ta Imo ke kyarar ’yan Arewa, “Suna fada mana sunan da bai dace da mu ba, sannan kuma suna nuna mana kyama wurin shiga motar haya da sauran mu’amaloli”. Inji shi.
Dangane da sauran kabilu baki da ke zaune a jihar, irin Yarbawa da sauransu, ko ana yi musu katin, sai ya ce, “Wannna rajista iyakar Hausawa ’yan Arewa kadai ake yi wa. Mu Hausawa kadai aka tirsasa wa mu yi wannan rajista, su ba a ce musu su yi ba, babu ruwansu”.
A karshe shugaban ya bukaci hukumomi su magance wannan matsala, wadda ya kira da wata sabuwar hanya ta takala domin rikici ya barke a tsakanin al’ummomin Arewa da Kudanci.
Sai dai kuma lauyoyi, sun bayyana ra’ayoyi mabambanta game da cancantar wannan tantacewa ko matsayinta a hurumin doka, bisa la’akari da tsarin da gwamnatin Jihar Imo ta fito da shi na tantance ’yan Arewa da ke kasuwanci a jihar, saboda tsoron ko suna da alaka da ’yan kungiyar Boko Haram.
A hirar da Aminiya ta yi da wani Babban Lauyan Najeriya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa shirin tantancewar ya saba wa doka, saboda kundin tsarin mulkin Najeriya yana tabbatar da ’yancin walwala, sannan ya kawar da kowace irin wariya. Don haka ya ce, za a iya amincewa da shi, in da za a gudanar da shirin a tsakanin daukacin mazauna jihar ne. “Za ka iya tantancewa ka yi rajista ta bai-daya, amma ba za ika iya ware wani rukuni don yi musu rajista kawai ba. Kundin tsarin mulki ya bayyana karara, don haka nuna wariya ga wani rukuni na al’umma ya saba wa doka. ’Yan arewa ba su kadai ba ne ake zargi, akwai ’yan Kudu, har ma da baki ’yan kasar waje da ake zargi da kai harin kunar bakin wake,” inji shi.
Shi ma wani kwararren lauya a kan tsarin mulkin kasa da ke Abuja, Barista Waziri Yusha’u Mamman ya bayyana shirin kafa dokar tantance ’yan Arewa a matsayin karan-tsaye ga kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda tsarin dokar kasa ya haramta.
Barista Yusha’u ya ce a cikin tsarin kundin mulkin Najeriya akwai wadansu dokokin da gwamnatin tarayya ce kadai ke da hurumin yi, a yayin da wadansu dokokin kuma da ake yi musu lakabin na hadaka, gwamnatocin jihohi ma na da hurumin kafa su don samar da zaman lafiya ga mazauna jihohinsu, sai dai dokar za ta rataya ne a kan dukkan mazaunin jihar, wanda a cewarsa doka ta 2 da ta 3 da ta 4 suka ba da damar kafawa.
“Amma kafa doka da za ta ware wadansu ko wani  dan Najeriya a yi musu ko a yi masa wata doka, ko hukunci saboda kawai ya fito daga wata al’umma ko kabila ko jiha ko asali ko jinsin halitta (sed), ko addini ko ra’ayin siyasa, ba tare da dokar ko hukuncin ta shafi wasunsa ko wasunsu ba, ko kuma nasa ya fi tsanani a kan na sauran, ba daidai ba ne kuma ya saba dokar kasa, kamar yadda sashi na 42, karamin sashi na daya a cikin kundin mulki na Najeriya na shekara ta 1999 ya nuna karara”, inji Barista Mamman.
Masanin tsarin mulkin ya kuma nisanta tsarin dokar shari’ar Musulunci da wadansu jihohin Arewa suka kafa  a jihohinsu a shekarun baya don aiwatarwa a kan al’umman musulmai kawai daga fadawa cikin wannan tsarin, inda ya ce tsarin dokar shari’a dokar kasa ce ta amince da shi, sabanin wanda ake magana a kai, wanda dokar ke hani da shi. “Shi wanda kake magana a kai, babu shi a dokar kasa, kuma kasancewar ba zai shafi wadansu jama’ar ba, kamar Yarbawa ko ’yan kabilar Igbo, illa ’yan Arewa kawai da suka je ko suke da zama a jihohin, a fili yake cewa ana kyamarsu ne ko ana zargin daukacinsu da kasancewa a cikin wani abin da ake ki, kuma hakan ya saba wa dokar kasa”, inji shi.    
Shi kuwa Cif Henry Akunebu, cewa ya yi wannan shirin tantancewar mataki ne na tabbatar da tsoro, inda aka ware wadanda ake ganin aikata laifin kai harin kunar bakin wake a tattare da su.
A cewarsa: “Matukar cewa ba za mu iya hana kowa zama a kowane bangare na kasar nan ba, to za mu iya ware masu aikata laifuka, ko mu afka cikin matsalar tsaro a duniya. Gwamna a matsayinsa na babban jami’in tsaron jiharsa, hakki ne da ya rataya a kansa ya bayar da cikakkiyar kariyar tsaro ga jihar”, inji shi.
Sakamakon wani bom da aka gano a cocin Libing Faith da ke Owerri, babban birnin jihar, sai gwamnati ta bayyana aniyarta ta tantance ’yan asalin Arewa da ke kasuwanci a jihar, don kare jihar daga ’yan Boko Haram.