Sai da muka shawarci doddanin tsafinmu sannan muka zabo sabon Ooni na Ife

Masu zaben Ooni na Ile-Ife sun bukaci al’ummar Jihar Osun da su ba sabon Ooni, Adeyeye Enitan Ogunwusi goyon baya. Jagoran masu zaben, Cif Joseph Ijaodo, Lowa Adimula na Ife, shi ne ya bukaci haka kana ya yi kira ga jama’ar jihar da su zauna lafiya, domin ba su zabo sabon Oonin ba sai bayan […]

Sai da muka shawarci doddanin tsafinmu sannan muka zabo sabon Ooni na Ife
Sai da muka shawarci doddanin tsafinmu sannan muka zabo sabon Ooni na Ife

Masu zaben Ooni na Ile-Ife sun bukaci al’ummar Jihar Osun da su ba sabon Ooni, Adeyeye Enitan Ogunwusi goyon baya. Jagoran masu zaben, Cif Joseph Ijaodo, Lowa Adimula na Ife, shi ne ya bukaci haka kana ya yi kira ga jama’ar jihar da su zauna lafiya, domin ba su zabo sabon Oonin ba sai bayan da shawarci doddanin tsafinsu da suke yi wa bauta.

Tuni dai Gwamnan Jihar, Ebgeni Ra’uf Aregbesola ya sanar da sunan Adeyeye Enitan Ogunwusi a matsayin Ooni na Ife wanda ya fito daga gidan masarauta ta Giesi a matsayin Ooni na Ile-Ife na 51.
Sarkin Hausawan Ile-Ife, Alhaji Mahmuda Lawal Madagali ya shaida wa Aminiya cewa zaben Adeyeye Enitan Ogunwusi a matsayin Ooni na Ife alheri ne ga ’yan Arewa mazauna yankin, domin shi mutum ne mai yawan jan su a jika. “Abin farin ciki ne gare mu, domin ya nuna mana tun kafin a ambace shi a wannan sarautar, domin komai zai yi yakan sa mu a ciki. Fatanmu shi ne, ya kamanta abin da wancan Oonin ya yi mana, domin mu tsakaninmu da shi sai addu’a.” Inji shi.
Daga nan ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna yankin da su ba sabon Oonin goyon baya, domin ganin an ci gaba da samun kyakkyawar alakar da ke tsakanin marigayi Oonin da sabon na yanzu, domin a cewarsa, a wancan lokacin sarakunan Arewa na jihohin Kano, Katsina ko Zariya da ma Sarkin Musulmi sukan zo Ile-Ife, kuma suke jin tamkar su ma a Arewa suke. A saboda haka ya yi fatan a ci gaba da samun irin wannan dangantaka.