Sai da na ba yarinyar da ta yi mini kazafin fyade Naira miliyan 136 kafin ta yi shiru – Ronaldo

Fitaccen dan kwallon kafar nan na duniya Cristiano Rodaldo ya ce sai da ya biya yarinyar da ta yi masa kazafin  fyade zunzurutun kudi har Dala dubu 375 (kimanin Naira miliyan 136)  domin ta yi shiru a shekarar 2010.  Kathryn ’yar kasar Amurka da ta fito daga Jihar Las Begas ta zargi Ronaldo da yi […]

Sai da na ba yarinyar da ta yi mini kazafin fyade Naira miliyan 136 kafin ta yi shiru – Ronaldo

Cristiano Ronaldo

Fitaccen dan kwallon kafar nan na duniya Cristiano Rodaldo ya ce sai da ya biya yarinyar da ta yi masa kazafin  fyade zunzurutun kudi har Dala dubu 375 (kimanin Naira miliyan 136)  domin ta yi shiru a shekarar 2010.  Kathryn ’yar kasar Amurka da ta fito daga Jihar Las Begas ta zargi Ronaldo da yi mata fyade a shekarar 2009 inda ta kai shi kotu don ganin ya fuskanci shari’a kan keta mata haddi. Sai dai kamar yadda kafar labarai ta legit.Hausa ta ruwaito dan wasan na Jubentus ya ki amincewa da zargin inda lauyoyinsa suka nemi Kathryn ta janye karar daga gaban kotun Jihar Las Begas.

Lauyoyin Ronaldo sun  ce sun jima da biyanta makudan kudi da suka kai Naira miliyan 136 don a samu maslaha amma ba don Ronaldo ya aikata abin da take zarginsa da shi ba.

A cikin watan jiya ne hukumomin Jihar Las Begas suka ce babu wasu isassun shaidu da suke tabbatar da cewa dan wasan ya aikata laifin da ake zarginsa da shi. Wannan lamari dai na ci gaba da jan hankalin magoya bayan dan wasan, yayin da su kuma masu rajin kare hakkin dan Adam suke kokarin ganin an gurfanar da Ronaldo a gaban kotu don amsa tuhumar da ake yi masa.