Sai da na daina bara na samu arziki —Nakasasshe
Abdullahi ya ce ya je wasu kasashe bara amma bai samu arziki ba sai da ya daina bara.
Abdullahi Nuhu wani nakasasshe ne wanda ya ce sai da ya bar sana’ar bara da yake yi a baya sannan ya samu alheri mai yawa a rayuwa.
Abdullahi da ake wa lakabi da Kamara, ya ce sana’ar bara ta kai shi wasu kasashe a nan Afirka kamar Ghana da Togo, amma duk bai samu alherin da ya samu daga baya ba.
- Irin ‘wulakancin’ da masu haihuwa ke fuskanta daga malaman asibiti
- Ya auri kanwarsa da ta bace tun tana jaririya
- ’Yan bindiga sun kashe daliban Jami’ar da suka sace Kaduna
- Harin ’Yan bindiga: Saudiyya ta ba da tallafin abincin $1.2m a Zamfara
Mai shekara 48 da ke da aure da ’ya’ya 3, ya ce iyayensa sun taho da shi Abuja tun yana da kamar shekara 15 a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida.
Dan asalin unguwar Dakata a Karamar Hukumar Nassarawa cikin Birnin Kano, Malam Abdullahi, ya bayyana mana abin da ya sa shi da wasu nakasassu suka yi watsi da sana’ar ta bara.
“Silar zamanmu a waje guda wani bawan Allah ne mai suna Fasto Joshuwa Ingila da ya gayyacemu zuwa taron murnar aihuwarsa.
“Ba na mancewa a lokacin ana kamar 3 ga watan Azumi, sai ya ce mu Musulmi ne ga Azumi, ya ce hoto za mu yi mu tafi.
“Bayan nan da za mu wuce sai ya mana kyautar kudi Naira miliyan 1 da rabi mu kamar 10 da muka je.
“Mun yi ta shawarwari kan abin da za mu yi da kudin, amma a karshe sai muka yanke shawarar sayan fili kasancewar mun gaji da yawon haya da muke yi, wasunmu kuma suna kwana ne a dakunan baca.
“Bayan wani lokaci kuma, sai muka kafa kungiya mai suna Nasara tare da zaben shugabanni a tsakaninmu inda aka zabe ni a matsayin.
“Ba mu kai ga yanke shawarar inda za mu sayi fili ba, sai wata kungiyar tallafa wa al’umma mai suna Community and Social Debelopment Project ko CSDP ta tuntube mu kan shirinta na tallafa mana.
“Sharadin shi ne mu ne za mu nemi fili mai girma da fadin mita 400, sai su kuma su
kakkafa mana abubuwan alheri a wajen da zai hada da cibiyar koyar da sana’o’i da wurin
kwanan jami’ai da dalibai da masallaci da dai sauransu.
“A nan sai faduwa ta zo daidai da zama, koda yake kudinmu ba zai kai ya sayi makeken fili irin wannan ba.
“Amma sai suka yi mana alfarma muka sayi mai girman mita 100 da fadin mita 50 don mu samu
damar cin gajiyar tallafin da suke bayarwa wanda ke da nasaba da bankin duniya.
“Nan take kungiyar ta CSDP ta sako mana Naira miliyan 7 da dubu 900 a asususun ajiyarmu don gudanar da ayyukan.
“Mun gina manyan dakuna na wajen koyar da sana’a guda 2 – daya na maza daya na mata, sai kuma ofisoshi guda biyu.”
Malam Abdullahi ya ce cikin kudin sun sayi injin surfe da na nika da dawainiyar dauko su daga Kano da kuma aikin killace wurin da aka kafa su a kan kudi Naira miliyan 1 da dubu dari biyu da sittin.
Sai dai ya ce an samu matsala wajen sautun na’urar tafuraita da ta dabi’i da kuma injin janareta da suka bayar a kan Naira dubu 950.
Ya ce wanda aka ba aikin ya ha’incesu kuma har an kai ga kai lamarin gaban kotu amma ba tare da nasara ba, inda a karshe suka bar lamarin ga Allah.
Ya ce akwai kuma wata kungiyar Da’awa mai suna Hasbunallahu da ta dauki nauyin gina musu masallaci a wajen da ya hada da bangaren maza da mata, sai kuma fara aikin gina dakuna 3 da kungiyar ke yi bayan ta fahimci cewa abin hannunsu ya kare.
Ya ce kungiyarsu da ke da mambobi kamar 150, tana da jami’ai kamar 5 da ke karantar da su
ilimin addini da na boko, sai kuma masu koyar da sana’o’i na dinki da na yin takalma da kanikanci da kuma gyaran lantarki.
Ya ce a yanzu sun yi watsi da yin bara, sai dai idan wata bukatar gaggawa ta bijiro suna
gabatar da takarda a masallatai da kuma wasu majami’a da ke tallafa musu.
Shugaban na kungiyar, ya bukaci Ma’aikatar Kula da Yankin Birnin Tarayya Abuja da ta kai musu dauki kan daukar nauyin malamansu da kuma ingata bangaren koya musu sana’a da hakan zai yi daidai da shirinta na hana yin bara a gefen tituna.
Ya ce cibiyar na taka rawa wajen kulla aure a tsakanin masoya masu nakasa a wajen ko wani waje na daban.
Ita ma da take zantawa da Aminiya, wata mai nakasa mai suna Amina Yahaya wadda ke matsayin jagorar mata ta kungiyar, ta ce ta amfana sosai da zama a wajen inda ake koyar da su ilimin addini da na boko da kuma sana’a.
“Na zo nan Abuja ina da kamar shekara 17 har na yi aure tare da samun karuwa ta yara hudu a yanzu.