Sai da na koma cin busasshiyar shinkafa a hannun sojoji saboda azaba – Bazoum

Ya kuma ce wajen da yake ko lantarki babu tsawon mako guda

Sai da na koma cin busasshiyar shinkafa a hannun sojoji saboda azaba – Bazoum

Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum

Hambararren Shugaban Kasar Nijar, Mohammed Bazoum, ya ce sojojin da suka yi masa juyin mulki sun ajiye shi a wani kebantaccen waje sannan suka tilasta masa cin busasshiyar shikafa.

Idan za a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Yuli ne sojojin suka hambarar da gwamnatin Bazoum sannan suka dakatar da amfani da Kundin Tsarin Mulkin kasar nan take.

Gidan talabijin na CNN ya ambato Bazoum a cikin jerin wasu sakonni yana shaida wa wani abokinsa cewa “an hana shi kowanne irin ’yanci a matsayinsa na dan Adam” tun ranar Juma’a, sannan ya ce babu wanda yake ba shi abinci da magani.

A cewar hambararren Shugaban, mako daya ke nan yake rayuwa a wajen da ko lantarki babu, kamar yadda yake a sauran sassan kasar tun bayan da Najeriya ta yanke wa Nijar wuta.

Bazoum ya kuma ce dukkan kayan marmarin da aka samar masa yanzu sun lalace, inda yanzu ya koma cin busasshiyar shinkafa da taliya.

Sai dai duk da killace shin da aka yi, Bazoum na ci gaba da samun damar yin alaka da abokansa.

Idan za a iya tunawa, ko dazu da yamma sai da Sarkin Kano na 14 ya sami ganawa da shugaban Mulkin sojan kasar, Abdulrahmane Tchiani a Yamai babban birnin kasar.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa a kashin kansa Sanusi ya tafi ganawar, kodayake ya sanar da Shugaba Tinubu kafin ya tafi.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa