Sai da na kusa zubar da hawaye ganin yadda aka yi wa Legas — El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce ya kusa zubar da hawaye bayan ganin irin ta’adin da aka yi wa jihar Legas

Sai da na kusa zubar da hawaye ganin yadda aka yi wa Legas — El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya ce ya kusa zubar da hawaye bayan ganin irin ta’adin da aka yi wa jihar Legas sakamakon zanga-zangar #EndSARS.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa takwaransa na jihar Babajide Sanwo-Olu ziyara a ranar  Alhamis.

El-Rufa’i ya ce Sanwo-Olu ya yi duk iya kokarinsa wajen ganin ba a samu tashin hankali a jihar ba, amma bata-gari sai da suka yi amfani da zanga-zangar wajen lalata kayan al’ummar jihar.

Ya ce “Na dauki tsawon lokaci ina duba hotunan yadda aka yi wa Legas barna, sai dana kusa zubar da hawaye ganin yadda aka lalata dukiyoyin al’ummar da su ke samar da ayyukan yi ga matasa.

“Bayyana bacin rai ga irin zaluncin ‘yan sanda ba laifi ba ne, amma lalata dukiyar al’umma ba komai bane face kawo nakasu da koma baya” inji shi.

El-Rufa’i ya nuna alhininsa ga iyalan ‘yan sanda da jama’ar gari da suka rasa rayukan ‘yan uwansu a sanadin rikicin zanga-zangar, tare da kira ga gwamantin tarayya ta kare faruwar hakan a gaba.

Shi kuwa a nasa bangaren, gwamna Sanwo-Olu, ya godewa El-Rufa’i bisa ziyarar jajantawar da ya kawo masa tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kawo karshen ayyukan wanda basa kishin ci gaban jihar.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa