Sai dai APC ta kore ni, amma ba zan daina tsage gaskiya ba —Ndume

Tun tuni da ma tashin farashin man fetur ya haddasa hauhawar kayan masarufi abin da ya sanya magidanta da yawa cikin mawuyacin hali.

Sai dai APC ta kore ni, amma ba zan daina tsage gaskiya ba —Ndume

Sanata Ali Ndume wanda ƙusa ne a Jam’iyyar APC ya ce zai ci gaba da faɗa wa Shugaba Bola  Tinubu gaskiya, ko da hakan zai janyo a kore shi daga jam’iyyar.

Ali Ndume ya ce: “Kowa ya san abin da ke faruwa a ƙasar nan. Kowa yana ji a jikinsa. Kuma ba laifi ba ne in gaya wa shugaban ƙasa don a kawo gyara.”

Sai dai ga dukkan alamu, ko Shugaba Tinubu bai ga laifin waɗannan kalamai ba, to ran Jam’iyyarsa ta APC ya ɓaci, abin da ya sanya ta fitar da sanarwa tana yi wa Sanata Ndume gargaɗi.

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa, Sanata Ali Ndume, babban ɗan jam’iyya ne kuma sanata sannan yana da ƙima sosai a idonta da kuma jama’a, don haka in ji ta, bai kamata duk lokacin da za a ambace shi, sai a ce ya yi wani abu da zai tozarta jam’iyya ba.

Ta ce an an jiyo Sanata Ndume a baya-bayan nan yana iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu yana zagaye da mashawarta waɗanda ba nagari ba, ko kuma ’yan hana ruwa gudu da ke toshe hanyar da za a je, a ba shi shawara tagari.

Ko kuma su suke bashi shawarwari waɗanda ba nagari ba, yake aiki da su, kamar yadda mai magana da yawun Jam’iyyar APC, Malam Bala Ibrahim ya bayyana.

A watan Yulin da ya wuce ma, sai da Jam’iyyar APC ta nemi Majalisar Dattijai ta cire Sanata Ali Ndume daga muƙaminsa na mai tsawatarwa a majalisar saboda an zarge shi da sukar gwamnatin Shugaba Tinubu.

Daga bisani dai sanatan ya nemi afuwa, amma har yanzu ba a mayar da shi kan muƙamin mai tsawatarwar ba.

Sanata Ali Ndume ya ce yana magana ne a bainar jama’a saboda ba ya samun damar ganin Shugaban ƙasar, balle ya je ya faɗa masa halin da al’umma ke ciki.

Ya ce na rubuta har sau biyu, na yi ma waɗanda suke kusa da shi magana. Kuma maganan da na yi gaskiya ne, Kundin Tsarin Mulki ya ba ni damar haka.

A cewarsa, haƙƙi ne a kansa, ya ba da shawara a matsayinsa na dattijo.

Sai dai Jam’iyyar APC ta ce mutum babba mai ƙima kamar Sanata Ali Ndume, bai kamata a ce ana yamaɗiɗi da sunansa a matsayin wanda ke ƙoƙarin tozarta martabar jam’iyya ba.

Amma Ndume ya ce a duk bayanansa babu inda ya aibata wani, kuma babu inda ya soki jam’iyya ko shugaban ƙasa.

Ya ce duk maganar da ake yi matuƙar dai game da shawara ce, to yana nan a kan matsayinsa.

Sanatan ya ce ya bi duk hanyar da zai iya bi don ganin ya samu damar ganin Shugaban ƙasa saboda ya bayyana masa halin da ’yan Nijeriya ke ciki amma bai yi nasara ba.

”Maganar cewa ni babban ɗan jam’iyya ne wanda zan iya ganin Shugaban ƙasa, ba haka ba ne,”in ji Ndume.

Ya ce yana magana ne domin sauke nauyin al’umma da ke kansa a matsayinsa na mai wakiltar jama’a.

Tun tuni da ma tashin farashin man fetur ya haddasa hauhawar kayan masarufi abin da ya sanya magidanta da yawa cikin mawuyacin hali.

Sanata Ali Ndume dai ya yi iƙirarin cewa wasu makusanta sun tokare Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma sun hana shi sanin mawuyacin halin da al’ummar ƙasar suke ciki.

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa