Sai dan jarida ya zama abokin kowa zai rika samun bayanai – Grace Alheri
Daya daga cikin fitattun ’yan jarida mata kuma ma’aikaciyar sashin Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka Grace Alheri Audu ta ce aikin jarida yana da muhimmanci ga al’umma sai dai jama’a da su kansu ’yan jaridar na bata aikin. Ko mene ne dalilinta idan aka biyo mu za a ji: Abubakar Ibrahim a Washington DC […]
Daya daga cikin fitattun ’yan jarida mata kuma ma’aikaciyar sashin Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka Grace Alheri Audu ta ce aikin jarida yana da muhimmanci ga al’umma sai dai jama’a da su kansu ’yan jaridar na bata aikin. Ko mene ne dalilinta idan aka biyo mu za a ji:
Abubakar Ibrahim a Washington DC
Aminiya: Da farko wace ce Grace Alheri Audu?
Grace Alheri: Da farko dai sunana Alheri amma na kara da Grace lokacin da nake makarantar firamare a garin Dutsin-ma a Jihar Katsina. Wato wata babata ce ta tafi da ni can lokacin tana aiki a asibiti a yankin, ana kiran ma’aikatan asibiti a lokacin da O.C, (Officer in Charge).To lokacin makaranta daya ne tak a Dutsin-ma da wannan asibiti, kana akwai gidan burodi guda daya.Kafin in tafi Dutsin-ma na iya tuka keke, sai Babata ta saya mini keke duk inda za a aike, ni sai in tafi a kan keke. Lokacin yaro namiji ya tuka keke abin kallo da sha’awa ne balle a ce mace. To ka san halin yara da tsokana da sun gan ni bisa keken nan sai su rika kira Alheri Bread, domin gidan burodin nan sunansa Alheri Bread, ni kuma sunana Alheri, domin tsokana ba su tashi cewa Alheri Bread, sai sun gan ni, duk inda na shiga ina bisa kekena sai ka ji yara suna Alheri Bread! Alheri Bread! Wannan abu na bata mini rai, sai ya zamanto ba na son wannan suna ko kadan shi ne sai na kara da sunan Turanci wato Grace, yana nufin Alheri. To yadda sunan Grace ya fito cikin sunana ke nan, amma sunan da aka rada mini shi ne Alheri.
Aminiya: To, kamar shekaru nawa ke nan, kuma yanzu kina da kamar shekaru nawa?
Grace Alheri: Gaskiya ban sani ba, domin lokacin da aka sa ni a makarantar firamari ma ban isa shiga ba, an dai sani ne daga baya ma dole babar tawa ta mayar da ni wajen mamata, domin wannan suna da yara suka matsa mini (da kira) don haka ban kammala firamare ba na bar Dutsin-ma dole ta mayar da ni wajen mamata a Malumfashi, nan ma ban gama ba sai na koma Dass (a Jihar Bauchi) domin mahaifiyata mutumiyar Dass ce. Ina iya bugun kirji, in ce ni cikakkakiyar ’yar Arewa ce, domin kakana Bakano ne ya zo, ya zauna a Malumfashi, Babana Bakatsine, mamata ’yar Bauchi, ni kuma na yi aure a Jihar Filato.
Aminiya: To a ina kika gama firamare?
Grace Alheri: Na gama makarantar firamare a Dass, daga nan sai na wuce makarantar sakandaren kwana ta Kabo da ke Jihar Kano, wata makarantar Mishan ce. Duk inda na fada maka din nan ina da alaka da su, ba inda ban yi karatu ba. Domin ka ga ina makarantar sakandare ta Kabo sai aka maishe ni makarantar Horar da Malamai ta Kaltungo wato (TC) ta maza da mata ne a wancan lokacin, sai dai kafin mu kare aka sake shawara cewa a raba maza da mata, sai aka mayar da ita ta mata zalla wato (WTC) kuma a lokacin har an nada ni shugabar dalibai mata, wato (Head Girl).
Aminiya: To daga WTC Kaltungo sai ina?
Grace Alheri: Da na gama nan, sai na tafi ECWA Seminary na yi digiri a nazarin addinin Kirista, sai na tafi Jami’ar Jos na yi digiri na biyu a kan addinan gargajiya na mutanen Afirka, sannan na sake komawa Jami’ar Jos na yi wani digiri na biyu a kan dokokin kasashen duniya da difilomasiyya.
Aminiya: Daga wane lokaci ne kika fada aikin jarida?
Grace Alheri: A yayin wannan digiri na biyu ne sai na tafi Kwalejin Koyon Aikin Talabijin da ke Jos, na yi takardar shaida kan aikin talabijin, sai kuma na je Cibiyar Koyon Aikin Jarida ta Najeriya (NIJ) na yi Diploma kan aikin jarida. Kuma na yi diploma a harkar sarrafa kwamfuta. Wannan aiki na jarida na shige shi a 1994 a gidan rediyon ELWA, lokacin babana dan jarida ne, ina ma iya cewa ya fi ni aikin jarida.
Rediyo ELWA wani rediyo ne mai zaman kansa na Kirista da ke Jos, to digirin farko da na yi a kan addinin Kirista, akwai kwasa-kwasan da suke da nasaba da aikin jarida, tun daga nan na fara aikin jarida, domin lokacin idan na zo hutu ina aikin wucin-gadi a wannan gidan rediyo, sai dai ba a biyana, wato kamar ina koyon aiki ne a kashin kaina.
Aminiya: To da kika kare ina kika koma, ko yaushe aka dauke ki aiki?
Grace Alheri: Aikin farko da aka dauke ni, shi ne a wata mujalla mai suna TODAY’S CHALLENGE, na yi aiki a wannan mujalla har na kai matsayin Mataimakiyar Edita a cikin shekara guda, sai na koma koyarwa a makarantar sakandare, ina koyarwa sai aka ba ni aikin koyar da darasin aikin jarida na wucin-gadi a Jami’ar Jos, lokacin an bude sashin koyar da aikin jarida. To, ina cikin koyarwa a sakandare ne bayan na yi shekara biyu sai na bari na koma gidan Rediyo da Talabijin na Jihar Filato (PRTb) a 1999. Na fara a fannin talabijin a matsayin mai karanta labarai da dauko rahoto, har na kai matsayin Mataimakiyar Darakta kafin na bari.
Aminiya: Da kika kare sai kika koma ina, ko kina ciki ne kika fara aiki da Muryar Amurka?
Grace Alheri: Ina ciki ne na fara, kuma abin da ya faru shi ne lokacin da aka yi rikicin Jos, gidan Rediyon Muryar Amurka ba su da wakili a Jos, wanda ke kula da wannan bangare, Allah Ya jikan rai, Yalwa Gabi yana Taraba, sai ya zamanto idan abu ya faru ba su da wani mutum a kasa, shi ne sai aka zo aka yi mini magana cewa don Allah ko zan yi wannan aiki? Sai na ji cewa ai wannan koma-baya ne domin duk wadanda ke irin wannan aiki mutane ne da ina cikin wadanda suka yi musu intabiyu aka dauke su aiki, yanzu kuma a ce in koma cikinsu ina aiki? Aka yi ta rokona, sai na hakura na karbi wannan aiki na zamowa wakiliyar wannan gidan rediyo, to, ka ji yadda na shigo bOA.
Aminiya: To kin kai tsawon shekara nawa kina ’yar rahoto?
Grace Alheri: Na kai shekara biyar ko fiye kafin a kawo ni nan Amurka. Na zo nan a shakarar 2005 a matsayin cikakkiyar ma’aikaciya
Aminiya: Kin taba cewa kin taka rawa a harkar siyasar ’yan jarida mata wato NAWOJ, wace rawa kika taka?
Grace Alheri: To, madalla ka yi min susa a inda yake mini kaikayi, ba shakka muna da hannu dumu-dumu cikin harkar wannan kungiya, domin na yi shugaban kungiyar ’yan jarida mata ta Jihar Filato kuma na yi shugaban kwamitin zabe na kungiyar ta kasa, ka ga wannan hoto mun dauke shi ne a Jihar Akwa Ibom lokacin mun je zabe.
Aminiya: Ganin ke mace ce kuma wannan aiki yana bukatar lokaci ga cin rai, yaya kike hada shi da aikin gida musamman renon yara?
Grace Alheri: Gaskiya ne, to amma gaskiya idan na ji mata suna wannan aiki suna kuka, wallahi haushi suke ba ni, shi ya sa idan an tashi ba mu wani abu ko rabon mukamai sai a rika mayar da mu baya.
Aminiya: Me ya sa kika ce suna ba ki haushi?
Grace Alheri: Wato da yawanmu ba mu tsara yadda za mu gudanar da harkokinmu, wato lokaci kaza ga abin da zan yi lokaci kaza wannan zan yi, shi ya sa sai ka ji ana ’yan koke-koke cewa abubuwa sun cukuikuye wa mace, in fada maka gaskiya duk karatun da ka ji na lissafa maka, na yi ne a gidan miji kuma ina da ’ya’ya, amma daidai da rana daya ba aikin da ya sha min kai saboda aikin gida, komai zan yi nakan tsara shi. A gidan mijina na kammala digirina na farko, duk ’ya’yana ina cikin wannan aiki na haife su kuma ba na makara zuwa aiki ko a ce ban je ba. Ina da aure ina koyarwa ina karatun digiri na biyu kuma cikin wadannan abubuwa ba wanda ya sha min kai, zan tafi in yiwo karatu in zo in koyar kana in tafiyar da ayyukan gida ba tare da wata matsala ba. Saboda haka wannan aiki na jarida ba abin da yake hana mace yi sai idan ba ta tsara shi yadda ya dace ba.
Aminiya: To wane kalubalen ke cikin wannan aiki na jarida a matsayinki na mace?
Grace Alheri: To, na farko dai ba zance ba kalubale ba, amma ban yarda a ce abu kaza bai yiyuwa a cikin harkar nemo labarai, shi ya sa idan na ji wasu abokan aikinmu ko wakilanmu na kokawa kan batun a tashi a je a samo labarai, sai inji su kawai, saboda na yi na gani. Na farko dai a matsayinka na dan jarida ya kamata ka zamo abokin kowa musammam abokan aikinka da mutanen gari ta yadda idan wani abu ya samu kana zaune wani zai kira ya ba ka bayani, ko kuma cikin abokan aikinka wani zai kira ka. A lokacin da nake wakiliya a jihohi 10, ni kadai nake tuka mota zuwa cikin daya daga cikin wadannan jihohi, abotarmu da Shehu Saulawa na BBC da Ado Abdullahi Hazad na Rediyon Jamus ta kut-da-kut ce, idan akwai aiki wani garin tare muke tafiya sai a ajiye motocin mutum biyu a shiga ta guda, saboda haka dan jarida ya kamata ya yi kyakkyawar alaka da abokan aikinsa.
Aminiya: Ba ki ganin lokacinku ya sha bamban da na yau?
Grace Alheri: A’a, ’yan jarida yanzu sun fi samun abu cikin sauki domin lokacinmu ba wayar salula, yanzu ga shi wannan hirar da muke yi da kai ta salular ake nadar ta, ka ga ashe yanzu komai ya fi sauki bisa ga da, kuma kullum kara fito da dabarun aikewa da bayanai ake yi fiye da baya.
Aminiya: Da yake an buga da ke gida kuma yau ga ki nan Amurka wasu bambance-bambance kika gani tsakanin aikin jarida a Najeriya da Amurka?
Grace Alheri: Bari in fara da batun da ya shafi hulda da jama’a, idan ka san yadda za ka yi hulda da jama’a sai aikinka ya zo maka da sauki, yadda za ka samu mutane ka yi hira da su a nan daidai yake da yadda za ka same su kana gida, sai dai kawai a gida kana da damar ka je ka samu mutanen gaba da gaba, amma a nan duk wanda za ka yi magana da shi, sai ta waya. To na gida ya zarta ka domin shi zai iya samun bayanin hayaniya a inda ake abu na hayaniya, ya sa mai sauraro ya ji yana kallon abin da ke faruwa a cikin zuciyarsa kamar yana kallo amma kai da kake nan ba ka da wannan damar. To wani abu kuma idan kana wakili kana iya ba da labari guda ka yi amfani da muryoyin mutum 10, amma a nan ba za ka iya haka ba, domin ina ka gan su. Sau tari sai ka ga bayanan da kake so ba za ka same su ba.
Aminiya: Sau tari idan ’yan jarida suka nemi manyan mutane a Najeriya domin hira da su a kan abin da ya shafi manufofin gwamnati sai su noke, amma ku idan kun kira su daga Amurka cikin rawar jiki sai su amince, ba ki ganin wannan kalubale ne ga ’yan jaridar Najeriya?
Grace Alheri: A’a, ai duk inda dan jarida yake mutane na sonsa, aikin yana da farin jini kuma yana da bakin jini, amma farin jininsa ya fi yawa a ganina. Kuma batun samun mutane a yi hira da su ko a nan sai ka ga wasu sun kira wasu suna son su yi hira da su amma sai su ki, amma idan na kira da wuya mutum ya ce mini a’a, domin na san me zan fada masa ya yarda ya yi magana. Misali a zaben shekarar 2011 na tafi Najeriya wajen aikin zabe sai na tafi gidan rediyon Freedom, to akwai wani babban mutum ba zan fadi sunansa ba, gidan rediyon Freedom sun dade suna nemansa ya zo su tattauna da shi bai amince ba, amma ina zuwa da na yi magana da shi cikin ’yan mintoci sai ga shi a gidan rediyon, sai abokin aikina Umar ya ce haba ranka ya dade yau shekara nawa muna nemanka amma ka ki zuwa sai da anti Grace ta zo yau sai ga ka, to ba ni ba ne, a’a iya hulda da mutane ne. Ka san da wa kake son ka yi hira kuma ka san abin da za ka fada masa ya yarda domin ya yi hirar da kai. Kuma ai dan jarida shi ma wani dan siyasa ne, dole ya kware wajen iya hulda da iya magana da mutane ta yadda duk lokacin da ya bude baki zai yi magana mutane za su yi sha’awar su saurare shi.
Aminiya: Ba ki ganin kun fi ’yan jaridar Najeriya dama, domin da mutum ya ji Grace Alheri zai so ya yi hulda da ita, domin duniya na jin Grace, sabanin’yan jaridar gida?
Grace Alheri: Na yarda da wannan, amma ban da wadanda ke aiki a kafofin labarai na kasashen Turai, kai ma da kake wakilin bOA kana da irin wannan dama, tunda ana jinka, domin na yi wannan aikin na san yadda yake a nan da can gida Najeriya, domin kai wakilin bOA yadda ake daukar ka ya fi shugaban wani gidan rediyon gida, saboda kana zuwa wuri ka ce kai wakilin bOA ne ko BBC ko Radio DW, sai a fi karrama ka da shugaban tashar PRTb, idan kun je neman labari guda.
Aminiya: To yaya batun amsar na goro a wannan aiki?
Grace Alheri: To, ni abin da ban yarda da shi ba ke nan, kuma har kwanan gobe ina alfahari da wannan shi ne ban yarda da maula ba wajen aikin jarida. Yadda za a je wajen aiki ka ga ’yan jarida na maula, wani lokacin ma idan ba a ba su ba, har su kai ga tambaya, na gode na fi karfin zuciyata game da wannan abu. Shi ya sa yau da yawanmu ba su da alkadari da martaba a idon mutane, musammam masu kudi da ’yan siyasa. Misali lokacin da aka sa dokar ta-baci aka dakatar da Gwamna Dariye a Filato na yi hira da mataimakinsa bayan mun gama sai ya ja aljihun teburinsa ya fito da kudi zai ba ni, sai na ce masa a’a ranka ya dade na gode. Sai ya ce ni na ba ki ba roka kika yi ba. Na ce masa a’a ranka ya dade sai wani lokaci, sai ya ce da ma an ba ni labarinki idan mutane sun yi miki alheri, ba ki amsa ki daina haka nan ba roka kika yi ba, su ne suka ga dama suka ba ki. To, ka ga gobe idan na nemi hira da shi ko ba shi da kudi zai amince domin ya san ba maula zan zo yi ba. Kuma wani abu shi ne idan kana karbanr kudin kana ji, kana gani labarin da za ka yi ya amfani al’umma, amma saboda mutum ya taba ba ka kudi, sai ka rubuta labarin ba yadda ya dace ba.
Aminiya: To, a nan Amurka akwai irin wannan karbar abin hasafi?
Grace Alheri: Sosai, akwai wannan damar a nan, sai dai idan hukuma ta ji ko ta gane, to ka kwana da sanin kun yi ban kwana da wannan aiki, domin ana biyanka gwargwadon hali ba abin da zai fi karfinka na rayuwa, albashinka ya ishe ka ci da sha kai da iyalanka. Tara dukiya ya danganci irin tattalinka, don haka ba ka da wata hujja sai dai idan kai mai hadama ne, kuma wannan matakin bai tsaya ga ma’aikacin jarida kawai ba. Akwai wani wakilin CNN mai zuwa kasashen Afirka yana aiki, musamman Najeriya sai ya yi wani labari da ba a ji dadinsa ba, sai ’yan Najeriya suka dana masa tarko ana zuwa aka tabbatar ya karbi na goro, nan take aka yi waje da shi. To a nan muddin aka gane kuma ga hujja ka karbi na goro ko wane aiki kake yi za a kore ka, wannan shi ne ya fi sauki fiye da duk wani abu. Kuma ba a duba girman abin da ka karba, Dala 10 bai da bambanci da rabin Dala ko Dala miliyan.
Aminiya: Ba ki ganin ma’aikatan sun sha bamban domin a Najeriya, sai ki ga ba kayan aiki, ba albashi, kana kana ji kana gani a take maka hakki?
Grace Alheri: Wannan gaskiya ne, to amma abin da mutane a can gida ba su sani ba shi ne idan kana hakuri da dan abin da ake biyanka, kana iya kyakkyawar rayuwa ba sai ka hada da kamuya-muya ba. Domin a nan din ga kayan aiki, ga albashi, to amma duk abin da za ka yi cikin albashin nan ne, domin nan komai za ka yi kudi ne, sai ka ga ga ka da kudi cike a rubuce amma da ka sa hannu ka fara sarrafa su, sai ka ga sun kare cikin kankanen lokaci wato ana hannu-baka hannu –kwarya a ba ka da hagu a amshe da dama, to idan ka auna sai ka ga wata sa’a har ma gwamma kana gida, sai dai nan akwai wutar lantarki, akwai ruwa, akwai asibiti, ba yajin aikin malamai, kome na tafiya kan tsari, don haka rayuwa ta fi sauki ta fannin abubuwa more rayuwa fiye da gida.
Aminiya: Shin a nan mutum na iya hada aikin gwamnati da wata sana’a?
Grace Alheri: Gaskiya da kamar wuya sabanin gida, nan zai yi wahala, sai idan sana’ar ta mako-mako ce, amma a gida Najeriya ma’aikaci na iya aiki, kuma yana wata sana’a ko kasuwanci, wata sa’a ya kawo kayan sayarwarsa wurin da yake aiki, idan ma ya saba wa doka to ba a hukunta shi.
Aminiya: Da za a ce ki ba ’yan jaridar Najeriya shawara me za ki ce musu?
Grace: Na farko a cire kwadayi wanda shi ne dalilin da ya sa mutumcinmu ke zubewa a aikin nan, aiki ne mai kyau, amma muna neman mu lalata shi, abin da ya sa kimarmu ke raguwa a idon jama’a. Babbar shawarata ’yan jarida su koma ga aikinsu su rike shi da martaba a rage maula, idan ba za a bari gaba daya ba, abu na faruwa yanzu za ka ga gidan talabijin na CNN ya baza shi kowane ne abin ya shafa ba ruwansa, amma mu cikin rahoto 10 da wakili zai aiko maka, idan ka sunsuna labarin da kyau sai ka ga an kauce wa ainihin labarin, kila ba a son a bata wa wanda abin ya shafa saboda abin da ya bayar ko zai baya. Muddin suka rufe ido suna aikinsu (yadda ya kamata) to martabarsu za ta kankama a idon jama’a. Ita ma kungiyar ’yan jarida ta tsaya tsayin-daka ta tabbatar tana bin hakkin ’yan jarida yadda ya kamata ba wai shugabanci da baki ba. Aikin jarida aiki ne mai ban sha’awa, aiki ne na taba rayuwar mutane mai tursasa wa mahukunta sake matsayi ko manufar gwamnati da ake ganin za ta yi wa jama’a illa ko kawo musu nakasu, to, amma yau mutane nawa ne ke sha’awar wannan aikin. Misali batun ’yan matan Chibok din nan ko tashe-tashen bama-bamai, idan dan jarida ya dauki matsaya, to ya sayar da martabarsa ko na aikin.
Aminiya: To me za ki ce game da kayan aiki?
Grace Alheri: Maganar kayan aiki ka zo nan Amurka ka ga abin da ke kasa, na gaba ya yi gaba, kasashenmu na Afirka kafin mu kamo su ba a cewa bai yiwuwa saboda ikon Allah ya fi gaban komai, amma idan aka cire ikon Allah, to sai dai a yi shiru. Kuma tunda can ne Allah Ya ajiye mu sai mu yi amfani da abin da muke da shi domin kada ya zo ya zame mana hujja a kanmu, duk da yake ba mu ne muka kirkiro su ba, yau akwai facebook, akwai twitter, akwai whatsup da sai ka yi doguwar tafiya zuwa inda za ka samu intanet, amma yau akwai na tafi-da-gidanka da ake cewa moderm.
Aminiya: Akwai kafofin watsa labarai na gwamnati da masu zaman kansu da suke kwashe watanni ba su biya albashi ba, wace shawara za ki ba ’yan jaridan da suka samu kansu a cikin wannan yanayi?
Grace Alheri: Gaskiya wannan akwai rauni kwarai da gaske, shi ya sa a baya na ce kungiyar ’yan jarida tana da rawar takawa, domin gidan jaridar zai ba ka takardar shaidar aiki ba albashi a ce ka yi ta kanka ba karamar illa ba ce ga al’umma. Domin sai ma’aikatan wadannan kafofin labaran su yi abin da suka ga dama ta fannin aikin jarida, suna gurbata abubuwa kuma ko sun ga gaskiya sai su kauce domin su samu na goro. Don haka kamata ya yi kungiyar ’yan jarida ta tabbatar ko dai a rufe ire-iren wadannan gidajen jaridu ko a dauki matakin da ya dace, domin sun kafa ginshikin rashin gaskiya.
Aminiya: Ko za ki bar ’ya’yanki su yi aikin jarida?
Grace Alheri: To ai ba ka sani ba, lokacin ina digiri na biyu na tafi neman bayani a Hukumar UNICEF domin ina rubuta kundin digiri na biyu a kan ’yancin yara ne sai daga nan na rikide na zama ’yar uwarsu wato Partner, sai ina shirya shiri domin yara wanda ya shafi aikin jarida a gidan talabijin na PRTb, inda yara suke hada shiri suna karanta labarai kamar ma’aikata ana nunawa kuma ’ya’ya na suna cikin wannan har aka rika ce wa dana, ga shi ka iya karanta labarai har ka fi manya ko aikin jarida za ka yi, sai ya ce sam “Ni dai ina yi ne saboda wannan shiri.” To amma yau yana harkar hada shirye-shirye ne a gidan talabijin da rediyo da fina-finai wanda danjuma ne da danjumai. Kuma cikin yaran da muke shirin nan yau akwai biyu sun zame ’yan jarida. Kuma akwai ’yar yayata daga wannan shirin da yanzu haka tana aiki da Rediyon Najeriya a Legas. Ke nan a gidanmu muna da ma’aikatan jarida mataki uku daga Babana zuwa ni kaina yau, kuma ga ’ya’yanmu su ma sun shiga wannan aiki, to ka ga ashe ba wai batu zan bar su, su yi ba ne, a’a suna ma yi