Sai ilimin boko ya zama kyauta kafin a samu mafita ga tabarbarewar kasar nan – Balarabe Musa

A karshen makon jiya ne tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, ya amshi digirin girmamawa na Dokta daga Jami’ar Jihar Gombe, wakilinmu ya tattauna da shi kan harkokin ilimi da makomar kasar nan:Aminiya: Kana daga cikin mutum uku da Jami’ar Jihar Gombe ta karrama da digirin girmamawa, yaya ka ji da wannan lambar […]

Sai ilimin boko ya zama kyauta kafin a samu mafita ga tabarbarewar kasar nan – Balarabe Musa
Sai ilimin boko ya zama kyauta kafin a samu mafita ga tabarbarewar kasar nan – Balarabe Musa

A karshen makon jiya ne tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, ya amshi digirin girmamawa na Dokta daga Jami’ar Jihar Gombe, wakilinmu ya tattauna da shi kan harkokin ilimi da makomar kasar nan:
Aminiya: Kana daga cikin mutum uku da Jami’ar Jihar Gombe ta karrama da digirin girmamawa, yaya ka ji da wannan lambar yabo aka ba ka?
Balarabe Musa: A gaskiya na ji dadi kuma duk mutumin da ka ga an ba shi irin wannan lambar yabo sai ya zama fitacce, idan ka saurari lokacin da ake karanta tarihin rayuwata dk gwagwarmayar da na yi a kasar nan wanda a can baya an so a rika ba ni irin wannan lambar yabo amma na ki amincewa na ce sai na kai shekara 70 kafin na fara karba kuma yanzu haka shekarata 78.
Aminiya:  Me ya sa ka ce ba ka son irin wannan lambar yabo sai ka shekara 70?
Balarabe Musa: Na fadi haka ne saboda a ganina idan mutum ya kai wadannan shekaru ne ya zama cikakken mutum da ya kamata ya kintsu idan ma a da ba kintsattse ba ne. Kuma wannan ne karo na biyu da na karbi irin wannan kyauta, Jami’ar Jihar Katsina ta taba ba ni digirin girmamawar, wannan na biyu ne.
Aminiya: Akan yi zargin cewa wasu na bi ta bayan fage ne su ba da na goro ganin mafi yawan lokaci a kan ba ’yan siyasa da masu kudi, me za ka ce?
Balarabe Musa: Kamar  yadda na gaya maka tun farko su suka neme mu, kuma dukkanmu da aka ba wannan digirin girmamawa ba wanda ya ba wannan jami’a wani abu, domin ba mu da wani amfani da za mu iya yi wa wannan jami’ar  an ba mu ne kawai bisa dacewa kuma ganin rashin dacewa na irin yadda wasu jami’oi ke ba wasu mutane irin wannan lambar yabo ne saboda mukaminsu ko kudinsu ya sa na ce ba zan fara karbar irin wannan lamba ba sai na kai shekara 70, kuma mu uku da aka ba digirin ni da Dokta Musa Babayo Talban Katagum da Farfesa Jonathan Nok, duk  mun cancanta, saboda ficen da muka yi ne kawai ya sa a ganina suka nemo mu suka karrama mu domin kamar ni har yanzu ba ni da kudi a banki, gidana ma daya ne har na yi Gwamna kuma duk abubuwan da na mallaka na mallake su ne a 1979 a matsayin tsohon ma’aikacin gwamnati kafin na zama Gwamna.
Aminiya: Dokta idan muka tabo batun tabarbarewar tsaro wace hanya kake ganin za ta zama mafita ga kasar nan?
Balarabe Musa: Mafita kawai ita ce sai shugbanni sun mayar da ilimin zamani daga firamare zuwa sakandare ya zama kyauta kuma tilas a kan kowane dan Arewa, sannan ne za a samu mafita domin
Kudu ta yi wa Arewa fintinkau wajen sha’anin ilimi na sama da shekara 40, kuma ilimin boko ya zama lalura, muddin ba ka da shi sai dai ka zama dan kallo a komai ake yi a kasar nan, ganin dan Arewa bai da ilimi kamar dan Kudu saboda wannan bambanci na shekaru masu yawa shi ne zai sa babu yadda za a yi a zauna lafiya da dan Arewa don ana ganin zai zama lalura dalili ba zai yarda ya zama bawan wani ba, kuma ba zai yarda a bullo da wani tsari da zai hana masa hakkinsa a matsayin dan Najeriya ba. Amma idan aka ba kowane dan Najeriya dama ya samu ilimi daidai kwazonsa ba nuna bambanci tsakanin dan Kudu da dan Arewa ba za a samu wannan baraka da take faruwa a wannan kasa na Boko Haram ba. Kuma ga wani abu da ’yan Arewa za su sani idan aka kawo ilimi kyauta kuma tilas da yadda aka wulakanta tarbiyyar nan ta almajiranci za a yi magance ta, domin almajiran da suke bara a kan tituna ba su wuce shekara 16 ka ga duk suna aji karatu ne na firamare zuwa sakandare kuma hakan zai sa a ga kowa ya samu dama ya ba ’ya’yansa ilimi. Duk da haka za a iya samun matsala da ’yan Arewa saboda an kawo ilimin bokon ne ta hanyar da tun farko babu Allah a cikinsa, amma idan aka hada ilimin boko da na addini zai sa a cire shakkun da ’yan Arewa ke da shi na an kawo musu bakon abu. A da lokacin muna yara an taba kawo wannan tsari amma daga 1970 ne aka canja tsarin ya bar tilas ya zama zabi, wanda haka ne ya kawo matsalar nan ta Boko Haram.  Sannan a lokacin da Obasanjo ya karbi mulki bayan kasha Murtala ya kawo wannan tsari, amma bai karbu a gun ’yan Arewa ba saboda suna ganin an kawo musu tsari ne wanda babu Allah a ciki sai maganar akida da siyasa kuma da hakan batun ya shiririce.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya