Sai Jega ya sauka za a tsaftace zabe a Najeriya

Idan ana son tsaftace zabe dole sai Jega ya sauka! Domin a duk zabbubukan da ya jagoranta an samu kura-kurai, bugu da kari ko zaben gwamnoni, watau tsakanin mutane 36 sai da aka yi magudi to ta yaya za a gudanar da zabubukan da za su gama kasa kamar Najeriya. Haka na kara nuna mana […]

Sai Jega ya sauka za a tsaftace zabe a Najeriya

Idan ana son tsaftace zabe dole sai Jega ya sauka! Domin a duk zabbubukan da ya jagoranta an samu kura-kurai, bugu da kari ko zaben gwamnoni, watau tsakanin mutane 36 sai da aka yi magudi to ta yaya za a gudanar da zabubukan da za su gama kasa kamar Najeriya. Haka na kara nuna mana cewa zai yi wuya a yi zabbubukan da za su samu karbuwa!
Idan aka samu mutane masu hakuri da son gaskiya, ba sai an tura dan sanda ko masu sa ido ba, amma saboda rashin gaskiya har daga kasaahen waje ake turo ‘yan sa ido idan za a yi zabe, duk da ba su da magani don su kan karkata ga ra’ayin kasashe da addinansu ba wai gaskiya ba!
Idan an yi gaskiya ne kowa zai gamsu da sakamakon, amma a halin da ake ciki yanzu da zarar an ce ma an yi zabe duk wanda ya fadi sai ya ce bai amince ba, sai kotu! Dole mu yadda wani ya fi wani, yatsu ba daya suke ba, akwai dogaye, akwai mai kiba, akwai ‘yar manuniya!
Rashin tsaftace zukata yasa ake gardamar da bata da ma’ana a sunan dimokuradaiya. Yayin da ko an raba zabubbukan zuwa jiha daya a kullun sai an sami kura-kurai, kai ko an ce za a yi gida-gida ne. bugu da kari zabubbukan kananan hukumomi sun tabbatar mana da dabi’ar ‘yan Najeriya.
Idan aka ce za a dauki tsarin nan na a kasa a tsare a raka a jira, za a iya yin yaki tare kona ofishin hukumar zabe Idan muka dauki zaben da aka yi a Anambara a kwanan ya tababbatar da irin kwamacalar da ake a sunan zabe, kuma ba yadda za a yi a ce hukumar zabe ba ta sane game da irin danyen aika-aikar da aka tafka.
Duk da an jigbe jami’an tsaro a filin dagar a kowace karamar hukuma, kuma an gudanar da zaben a tsanake, haka bai hana a yi mugun magudi ba, kuma shugaban hukumar (INEC) Jega ya  nuna ba laifinsa ba ne, to laifin wane ne? Duk da an yi aiki da kwamfuta, amma a gaza gane sunayen mutane, da walakin! Haka na kara nuna cewa tuna yanzu wasu sun san an kulla makarkashiya a zabubbukan da za a yi a 2015.
Ya kamata a san matsayin hukumar zabe INEC, idan an gaza zabe a jiha daya tak, to yashe za a gudanar da zabubbukan jihohi sama da ashirin a rana daya, lokaci guda? Idan kullum ana kuskure, yashe za a kware, tun da aka fara zabe a sunan dimokuradiyya, kullun tafka magudi ake, kuma abin sai gaba yake yi!
Duk da an tabbatar da cewa jam’iyya mai mulki na amfani da karfin iko wajen aiki da jami’an tsaro, kudin gwamnati wajen tafka mugun magudi. Haka ana hana ‘yan adawa amfani da kafofin yada labarai, bugu da kari a wasu jihohi ana hana ‘yan adawa gudanar da tarruruka!
Shi yasa ake kallon hukumar zade mai dadin baki, domin kullun nuna wa take a shirye take don tukarar zabubbuka, amma sai ga shi zaben gwamnoni 36 ya garara samun inganci, balle na miliyoyin mutane!
Wai me zai hana a yi zaben shiya-shiya, ta yadda ba za a yi hayaniyya ba!, Ko na ma jiha-jiha. Wasu  manazarta na ganin hukumar zaben mai zaman kanta (INEC) ba ta zaman kanta, zaman PDP take yi, kuma gwamnati take wa aiki. Akwai matsalar tsadar gudanar da zabe, domin a 2015 biliyoyin Naira da za a yi amfani dasu a rana zabe sun fi kasafin wasu kasashe!
A zargi INEC da daukar ashana don kyastawa tarayyar Najeriya wuta! Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na da hakki kan kowace irin makoma Najeriya ta sami kanta a 2015. daya daga cikin abubuwan da suke tabbatar da cewa demokurdaiyya ta tafiya yadda ya kamata shi ne zaben
cikin gida. Yayin da aka yi watsi da wannan damar ake ba ubangidanci fifiko a siyasar da ake walau jam’iyyun adawa da wadanda ke mulki.
Ya kamata a fassara bayanan INEC zuwa manyan harsunan Najeriya kamar Hausa da Igbo da Yarbanci, sannan a sayi filaye a gidajen Radiyo da jaridu don a fadakar da mutane game da hakokinsu, domin sai ka iske ‘yan siyasar su kansu ba su san hakkokin wadanda suke jagoranta ba, ko kuma dalibin kimiyyar siyasa a jami’a bai san cewa shugaban kasa yana ba harkokin kasashen waje muhimmanci fiye da na cikin gida ba, kuma shugaban kasa baya da isashen lokacin da zai rika bin jihohi!
Shi aikinsa ya gana da gwamnoni, ga zama da majalisar ministoci, jakadu, malamai, ‘yan kwangila, baya da lokacin iyalansa ko abokai! Hakkin gwamnoni ne su nemawa matasan jihohinsu ayyukan yi, tare da kirkirar kamfanoni da hayyoyin samun kudin shiga. Yayin da sai ka iske sanatoci da ‘yan majalisu, wasu na tunanin aikinsu shi ne su samo kudi su raba a mazabunsu! Wasu ‘yan majalisar da gwamnoni sun mayar da harkokins u fada, inda ake zaman fadanci da ubangidanci, sun dauka gwamna suke wa aiki! Maimakon wakiltar ra’ayoyin mutane.
Duk ma’aikatan hukumar zabe ba su bukatar a sake ba su wata dama, shi ke nan an ga kamun ludenku, ku tafi a zauna a fito da wadanda za su jagoranci zabubukan kasar a matakan shugaban kasa da gwamnoni, ta yadda gwamnonin tare da aiki da alkalai su tabbatar da an yi zabubbukan kananan hukumomi!
‘Yan siyasa sun gane ‘yan Najeriya na da tsoro, ko dan sanda ba makami aka gani a unguwa, ko aka tura sai ya razana mutane, balle in an watsa barkonon tsohuwa sai mutane su tarwatse nan take! To idan an harba harsashi wa za ka gani? Duk da shirye-shiryen da ake yi akwai yuwuwar kowa zai ce bai amince da zaben ba!
Buhari Daure
Muryar Talaka +2347035986444 [email protected]

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno