Sai mun kada PDP a zabe mai zuwa – Mataimakin Gwamnan Neja

Mataimakin Gwamnan Jihar Neja kuma jagoran Jam’iyyar APC a Jihar Alhaji Ahmad Musa Ibeto, ya lashi takobin kayar da Jam’iyyar PDP a zabukan da za a gudanar cikin watan da muke ciki da kuma na kananan hukumomin da za a gudanar a jihar nan gaba. Alhaji Ahmad Musa Ibeto ya lashi takobin ne yayin da […]

Sai mun kada PDP a zabe mai zuwa – Mataimakin Gwamnan Neja
Sai mun kada PDP a zabe mai zuwa – Mataimakin Gwamnan Neja

Mataimakin Gwamnan Jihar Neja kuma jagoran Jam’iyyar APC a Jihar Alhaji Ahmad Musa Ibeto, ya lashi takobin kayar da Jam’iyyar PDP a zabukan da za a gudanar cikin watan da muke ciki da kuma na kananan hukumomin da za a gudanar a jihar nan gaba.

Alhaji Ahmad Musa Ibeto ya lashi takobin ne yayin da yake yi wa dimbin magoya bayan Jam’iyyar APC jawabi a ofishin dan takaran Gwamnan Jihar na Jam’iyyar Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello wanda aka fi sani da Abu Lolo da ke Minna.
Ya bayyana takaicinsa ganin cewa al’ummar jihar da na kasar nan sun samu kansu a halin kuncin rayuwa duk da dinbim arzikin da Allah Ya albarkaci kasar nan da jihar da su.
Mataimakin Gwamnan ya ce, “Ina tabbatar muku cewa lokaci ya yi da al’ummar jihar nan za su dandani canji mai ma’ana wanda za su san cewa ana damawa da su. Na kasance cikin wannan gwamnatin da wa’adinta ke karewa a bana daga shekarar 2007. Abubuwa ba su tafiya yadda nake sha’awa, shi ya sa na nuna sha’awar tsohuwar Jam’iyyata ta PDP ta tsayar da ni takarar Gwamna amma aka nuna mini da sauran abokan takara rashin adalci.”
Ya ci gaba da cewa, “Tun lokacin da ake gudanar da zaben ne muka koka wa kwamitin zaben, amma ya yi biris da kokenmu. Haka mun rubuta takardar koke zuwa uwar jam’iyya ta kasa, bayan da muka gabatar a nan Minna, duk suka sa kafa suka shure lamarin. Da jama’a suka ga haka ne suka nemi in canja sheka zuwa inda suke ganin zan iya bayar da gudunmawa kuma a saurare ni. Dalili ke nan muka yi shawara da abokan tafiyata muka cimma matsayar tsunduma cikin wannan jam’iyya mai albarka. Don haka, mun ja daga za mu shiga wannan zaben babu gudu babu ja da baya.”
A jawabin Alhaji Abubakar Sani Bello, ya tabbatar wa Mataimakin Gwamnan kuma jagoran jam’iyyar cewa sun yi imani kwarewarsa a fannin siyasa ba kawai zai yi musu tasiri wurin samun nasarorin zabe kawai ba ne, zai taimaka musu su yi wa jama’a irin shugabancin da suka dade suna muradin gani, duk da cewa sau biyu suna zagayen jihar suna tozali da jama’a suna neman su kada musu kuri’u a zabukan da ke tafe.
Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce muddin suka samu nasara za a yi tafiya tare don ci gaba jihar ta kasance a sahun gaba wajen bunkasa walwala da tattalin arzikin jama’a.