Sai mun nemi izinin ’yan bindiga muke noma —Bafarawa

Bafarawa ya zargi ayyukan ’yan bindiga da haddasa tsadar kayan abinci.

Sai mun nemi izinin ’yan bindiga muke noma —Bafarawa

Attahiru Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koka da cewa sai al’ummar mahaifarsa sun nemi izinin ’yan bindiga suke iya noma gonakinsu.

Da yake magana a kan tsadar kayan abinci a Najeriya, Bafarawa ya danganta matsalar da rashin tsaro, yana mai cewa ’yan bindiga ne ke zabar gonakin da ake nomawa a mahaifarsa da ke karamar hukumar Isa.

Tsohon tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’ivvar DPP, ya shaida wa ’yan jarida labarai ranar Litinin cewa shi kansa dole ya hakura da noma gonarsa mai fadin hekta 10,000 saboda rashin tsaro.

“Ina da gona mai fadin sama da hekta 10,000 a Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, da nake noman masara tun a shekarar 1979, amma yanzu ban isa inje ba saboda ’yan bindiga,” in ji shi.

A Bafarawa, “matsalar tsaro ce ta kawo tsadar kayan masarufi saboda manoma ba sa iya zuwa su noma gonakinsu.

“A baya na taba jan hankalin gwamnati game da yiwuwar tashin farashin kayan abinci  saboda wannan matsalar amma suka ki sauraron shawarar.”

A karshe ya yi ba da shawarar hadin kai tsakakin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi wajen magance matsalar tsaro, musamman a yankin Arewa.

A cewarsa, “Gwamnatocin jihohi kadai ba za su iya ba sai da taimakon gwamnatin tarayya.”

Hakazalika, ya yi kira ga shugabanni da su farka daga barcinsu domin magance matsalar kafin ta gagari kundila.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta