Sai na bai wa matata cekin kudi take ba ni kanta —Magidanci

Magidancin na zargin matar sanay ’ya’yanta karbar kudi daga hannun kwartayenta

Sai na bai wa matata cekin kudi take ba ni kanta —Magidanci

Ma’aurata

Wani magidanci ya nemi kotu ta raba aurensu saboda matarsa tana tatsarsa makudan kudade kafin ta amince ya yi mu’amalar auratayya da ita.

Babbar Kotun Jihar Kwarra ta raba auren bayan sun shekara 28 da matarsa, wadda yake zargi da yawan kwartanci na wuce hankali.

Magidancin ya shaida wa kotun cewa matar, “Takan shardanta mini ba ta cekin kudade masu tsoka, kafin ta yarda in kusance ta; idan ban ba ta ba kuma ba za ta amince ba kwata-kwata.”

Ya shaida wa kotun cewa kwartoncin matarsa ya wuce misali, domin kwartayen nata na da yawa, kuma har ’ya’yanta take turwa karbar kudi daga wurinsu.

“Har kwashe kayanta ta yi daga uwar dakanmu ta je ta tare a dakin saukar baki.

“Ni kuma ba ta yarda in kusance ta sai idan na bata cekin makudan kudade, idan na ki kuma sai dai in hakura,” kamar yadda ya shaida wa kotu.

Ya ce tsabar rashin kamun matar tasa ya sa ta yi watsi da nayin da ke kanta a matsayin matar aure.

“Aurenmu ya riga ya rushe tunda har ta kai ga ni da ita ba ma iya zama mu tattauna abin da ya shafi rayuwarmu da ’ya’yanmu”, in ji shi.

Lauyan mijin, Mista Josiah Adebayo, ya gabatar wa kotun hoton tsiraicin matar tare da saurayinta da aka samu a cikin wayarta a matsayin shaida.

Don haka mijin ya bukaci kotu ta raba auren amma ta ba shi damar kula da ’ya’yan da tsakaninsu.

Amma martaninta, Roseline ta musanta tuhumar da ake mata, sannan ta zargi mijinta da bin matan banza.

Ta bayyana cewa ba ta kalubalantar bukatar mijin na kotu ta raba auren, amma tana so kotu ta mallaka mata wani bangare na gidansu da suke zama a Legas.

A cewarta, ita da mijin ne suka yi hadaka wajen gina gidan.

Da take yankiu hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a S.T Abdulqadri, ta amince da bukatar micin, tana mai cewa ta gamsu da shaidar da aka gabatar da ke tabbatar da zargin ke wa matar tasa.

Ta kuma karyata ikirarin matar na hakki a gidansu na Legas, da take so a mallaka mata wani bangarensa.

Amma kotun ba ta ba wa kowanne daga cikinsu hakkin riki yaran ba, saboda sun mallaki hankalin kansu, kowannensu ya fi shekara 20 da haihuwa.