Sai na nuna shaida ake yarda ni ba mace ba ce – Saurayi mafi kyau a duniya

Wani labari da ya ta da kura a shafukan sadarwa na zamani, da har kafar sadarwa ta Oddity Central ta wallafa da ke cewa, wani saurayi dan shekara 22 dan kasar Malesiya da yake da siffar mace ya ce ba a iya gane shi namiji ne sai ya gabatar da shaida. Saurayin mai suna Abdussalam […]

Sai na nuna shaida ake yarda ni ba mace ba ce – Saurayi mafi kyau a duniya

Wani labari da ya ta da kura a shafukan sadarwa na zamani, da har kafar sadarwa ta Oddity Central ta wallafa da ke cewa, wani saurayi dan shekara 22 dan kasar Malesiya da yake da siffar mace ya ce ba a iya gane shi namiji ne sai ya gabatar da shaida.

Saurayin mai suna Abdussalam Firdaus yakan ruda jama’a da dama wajen tantance shi mace ce ko namiji.

An ce akwai lokacin da ’yan sandan da ke gadin wani filin kwallon kafa a kasar, suka dakatar da Abdussalam Firdaus lokacin da yake son shiga saboda sun gaza tantance shi namiji ne ko mace har sai da ya fito musu da katin shaida kafin su amince shi namiji ne, kamar yadda kafar ‘Briefly.co.za’ ta sanar.

Abdussalam ya ce, lokacin da jami’an tsaro suka gaza tantance “Ni namiji ne ko mace abin ya ba ni mamaki matuka. ’Yan sandan ba su yarda cewa ni namiji ba ne lokaci da na bayyana kaina a gabansu, don haka suka bukaci in fito da katin shaidata,” inji shi.

’Yan sandan sun ce, “Gabatar da jinsi a wajen binciken ’yan sandan dole ne, saboda dan sanda namiji ya binciki jikin dan uwansa namiji yayin da ’yar sanda mace za ta binciki mace” don haka suke kokarin tantance kowane jinsi.

Abdussalam, ya rage sumarsa shekarun da suka gabata don a tabbatar da cewa shi namiji ne, amma duk da haka wadansu mutane suna ganin kawai yana yaudarar jama’a ne, kuma hakan ya sa wadansu suke kiransa da “tomboy” wato mace mai shigar maza.

Wani da yake bin shafinsa na Tiwita ya shawarci Abdussalam ya ajiye gashin baki ko gemu don tabbatar da cewa shi namiji ne.

Sai Abdussalam ya mayar masa da martani cewa ya yi bakin kokarinsa amma hakan ya ci tura, wani lokacin sai fuskarsa ta yi muni.

Abdussalam, ya samu karbuwa da sha’awa tare da yin martani kan batun da ke alaka da muhawara a shafukan sadarwa na zamani daga wajen dubban masu bibiyar shafinsa na sada zumunta. Don haka wadansu suke kiransa kyakkyawan namiji a duniya ko wanda ya fi kowane namiji kyau a duniya. Wannan kyau na saurayin halitta ce da Allah Ya ba shi.

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo