Sai NCC ta tantance wa Kamfanonin Sadarwa dukkan sanfuri gabanin bayyana shi ga jama’a
Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta wajabta wa dukkan kamfanonin wayoyin sadarwa cewa gabanin bayyana kowane irin samfuri ga kwastomomi sai hukumar ta tantance shi. Dukkan samfurin talla sai an tantance shi bayan ya ratsa dukkan matakan tantancewa, Shugabar Gudanarwar sashe ta NCC, Madam Helen Obi ce ta bayyana haka a yayin tattaunawar da hukumar […]
Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta wajabta wa dukkan kamfanonin wayoyin sadarwa cewa gabanin bayyana kowane irin samfuri ga kwastomomi sai hukumar ta tantance shi. Dukkan samfurin talla sai an tantance shi bayan ya ratsa dukkan matakan tantancewa, Shugabar Gudanarwar sashe ta NCC, Madam Helen Obi ce ta bayyana haka a yayin tattaunawar da hukumar ta shirya a Makurdi na Jihar Benuwai a karshen makon da ya gabata.
Madam Obi wacce Manajan Gudanarwar sashen, Mista Ekisola Oladisun ya wakilta, ya kara da cewa, “Wannan hukuma ta amince da tantance dukkan samfuri ga kamfanonin wayoyin sadarwa kafin aikewa kwatotomomi tsarin.” Don haka wannan hukuma za ta rika tantance dukkan tsari da ta wajabtawa kamfanonin kawo wa gabanin bayyanawa kwastomomi don tabbatar da cewa abokan hulda sun samu kyakkyawan sabis.
Tattaunawar da aka shirya a Makurdi ya maida hankali ne wajen musayar ra’ayi da kwastomomi a matakin kasa, bisa yadda za magance matsalolin dake da alaka da wayoyin sadarwa, don tabbatar da cewa an ba su kariya, ilmi, karfafawa da kuma kaddamar da kamfe game da ayyukan da hukumar ta sanya gaba. Mista Ekisola Oladisun ya kara da cewa akwai alkalumma dake nuna yawan korafe-korafe kan kamfanin wayar sadarwa ta yadda za iya daukar matakan da suka dace ga dukkan wanda ya saba ka’ida.
Ya yi nuni da cewa karfafa kwastoma na daya daga cikin muhimman kudurorin humumar NCC a wannan shekara, wadda ta yi masa lakabi da “Shekarar Abokan Hulda” sannan ya zaburar da kwastomomi bisa cin gajiyar lambar nan ta 2442 don takatar dukkan sakonnin shirme a wayoyinsu ta hanyar aike STOP zuwa 2442, don tsaida sakonnin shiga samfuri kuma HELP zuwa 2442. Amma idan matsalolin suka ki tsayawa ko kuma ba a gamsu da yanayin ba, to suna iya shiga da korafinsu kai-tsaye ga hukumar NCC ta hanyar kiran 622 don daukar matakin da ya dace kan kamfanin da ya yi zambar.
Sannan ta jaddada cewa hukumar a karkashin jagorancin Farfesa Umar Garba Dambatta ta kaddamar da wannan shekara kacokam ga abokan hulda don bada kariya, ilmantarwa da kuma karfafawa ga abokan hulda a kokarin cika tsarinta na ajandoji 8 na hukumar NCC.
“Kamar yadda kila kuka sani, an tsara wannan taro ne don tabbatar da alfanun a cikin masana’antun Najeriya ta fuskar wayoyin sadarwa, da wannan dalili ne hukumar a karkashin jagorancin Farfesa Umar Garba Dambatta ta himmantu don maida shi tabbatacce.
Haka kuma a yayin da yake fashin baki kan fagen maganadisun dogayen karafan sadarwar wayoyi, ya ce Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tantance ta kuma tabbatar da cewa karafan sadarwar ba su da wata barazana ga lafiyar bil-Adama.