Sai shugabanni da kowa an hada karfi za a yi zabe cikin lumana (2)

A karon farko cikin tarihin zabubbukan kasar nan, an samu zaunar da dukkan `yan takarar neman shugabancin kasar nan 14,a wani taron yini daya da akai a Abuja, inda bayan taron `yant akarar suka rattafa hannu akan sanarwar bayan taron mai taken‘Yar jejeniyar Abuja’, akan za su tabbatar da wanzar da zaman lafiya. Dukkan `yan […]

Sai shugabanni da kowa an hada karfi za a yi zabe cikin lumana (2)
Sai shugabanni da kowa an hada karfi za a yi zabe cikin lumana (2)

A karon farko cikin tarihin zabubbukan kasar nan, an samu zaunar da dukkan `yan takarar neman shugabancin kasar nan 14,a wani taron yini daya da akai a Abuja, inda bayan taron `yant akarar suka rattafa hannu akan sanarwar bayan taron mai taken‘Yar jejeniyar Abuja’, akan za su tabbatar da wanzar da zaman lafiya. Dukkan `yan takarar neman shugabancin kasar 14, ciki kuwa har da shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan na jam`iyyar PDP mai mulki a gwamnatin tsakiya da na babbar jam`iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari da sauran`yan takarar 12, sun amince da za su tabbatar da zaman lafiya a gaba ni ko lokaci da bayan zaben na bana da za fara nan da kwanaki 22, masu zuwa in Allah Ya kaimu.

Ofishin mai ba shugaban kasa shawara akan matakan tsaro dana mashawarci na musamman akan hulda da jam`iyyun siyasa,su suka shirya taron, ya yin da tsohon Sakataren kungiyar kasashe rainon Ingila, wato Cif Emeka Anyaokwu, wanda shi ya shugabanci taron, wanda bayan ya karanta sanarwar bayan taron, sai kuma ya rattafa hannunsa a zaman shaida kan `yan takararsu ka biyo baya. Tsohon Sakataren Majalisar dinkin Duniya Misata Kofi Anan ya kasance dan kallo.
Bayan dukkan `yan takarar sun amince da kudurori biyar da yarjejeniyar ta kunsa, kana suka sanya mata hannu. A takaicen-takaitawa kudurorin biyar sun hada da “Mu jam`iyyun siyasa da a ka ambata kuma muke takara cikin babban zaben 2015, muna shirye mu dauki matakan rigakafi, domin hana tarzoma a gabani ko lokaci ko bayan zabubbukan.”Sannan a shirye muke mu samar da yanayi na lumana da zaman lafiya ga zaben na 2015, tare da kara jaddada kudurinmu na bin tsarin mulkin kasar nan cikin shauki da tabbatar da hadin kai da kasancewar kasar nan a matsayin dunkulalliyar kasa.”
Yarjejeniyar ta ci gaba da tabbatar da cewa. “A shirye muke mukaucewa wata dabi`a ko halin da zai jefa harkokin siyasa da tsaron kasar nan a cikin hadari, kuma mun shirya domin fifita bukatun kasa akan bukatun mu, ko na jam`iyyun mu.” Muna sake jaddada kudurinmu na cikakkiyar biyayya ga ka`idoji da dokokin da suke kunshe a cikin kundin dokokin zabe a kasar nan. Don haka mun dauki alkawarin akan kanmu da jam`iyyumu.” Inji sanarwar bayan taron Yarjeniyar ta Abujar.
Ko shakka babu akwai bukatar a irin wannan lokaci a tabbatar da samar da irin wannan yarjejeniya tsakanin masu neman su shugabnci kasar nan, ba don kome ba, sai don irin yadda a wannan karon ne aka taba samun tsawon lokaci, har na kusan shekaru 16, ana gudanar da mulkin dimokuradiyya ba kakkautawa a cikin tarihin samun `yancin kan kasar nan yau sama da shekaru 54.
Sai dai kuma kash! A duk lokacin da kakar zabe irin wannan a karato, sai ka ji ana ta samun balahira nan da can, wadda kan haddasa asarar rayuka in tsautsayi ya gitta, da jikkata juna da kone-kone, sukan zama tamfar ado a cikin rigingimun siyasar kasar nan, a wannan karon ma ta kai har da hare-haren bama-bamai, duk da sunan sai an yi mulki ko ta halin-kaka. A kullum kuma tarihin zabubbukan na tabbatar da kara na-jiya da nay au akan sahihani. Alal misali zaben da aka fara ashekarar 1999, kowa ya yi ittifakin cewa ya fi na 2003, kyau.Haka na 2003, ya fi na 2007, wanda ya kawo marigayi tsohonshugaban kasa Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa kan karagarmulki, ya fi na 2011, matukar kyau da sahihanci. Ganin rashinsahihancin zaben 2007 ne ya sanya shigaba `Yar`aduwa ya kafaKwamitin tsohon Cif Jojin kasar nan Mai shari`a Lawal Uwaiswanda ya kawo gyare-gyare cikin kundin zaben kasar nan nashekarar 2010. Duk da haka sai da aka samu zanga-zanga azaben 2011 wadda ta fi kowace zanga-zangar zabe muni tun daaka fara wannan dimokuradiyya.
Yanzu maganar da ake, ana ta samun tashe-tashen hankula,akasari tsakanin magoya bayan jam`iyyar PDP, mai iko da gwamnatin tsakiya da na babbar jam`iyyar adawa ta APC, a gefe daya kuma da na jam`iyyar APGA da na APC a jihohi irin suRibas da Kaduna da Ebonyi da Filato da Gwambe. A dukkan wadancan tashe-tashen hankula da suka afku, zuwa yanzu duk da ba inda ake samu salwantar rayuka, amma dai rahotanni sun tabbatar da cewa bayan jikkata juna, an kuma samu kone-kone tare da bata kayayyakin jam`iyyun da na shugabanni ko magoya bayansu, kamar su ofis-ofis da kayayyakin yakin neman zabeirinsu motoci ko allunan `yan takara. A jihar Ebonyi, har kokarin jefa bom aka yi a ofishin jam`iyyar APC na Abakaliki, wanda in banda Allah Ya sa aka samu daukin `yan sanda cikin gaggawa da yanzu labari ya sha bamban, kamar yadda Kakakin Rudunan`yan sanda jihar Mista Chris Anyanwu ya shaida wa manema labarai.
Tabbas akwai bukatar samar da waccan Yarjejeniya ta Abujada tabbatar da aiki da ita, amma kuma kamar yadda su `yan siyasa da magoya bayansu da Malaman addinai da sauran masu ruwa da tsaki a cikin tafiyar da tabbatacciya kuma sahihiyar dimokuradiyya da ake fatan ta dore, da sauran jami`ai irin na Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa, wato INEC da jami`antsaro (dukkansu) dole sai kowa ya yi aikinsa tsakani da Allahkuma ba sa ni ba sabo.
Ba wai katobar magana ta `yan siyasa ko ta masu goyon bayansu ko ta malaman addini kadai ke haddasa tashe-tashen hankula kafin da lokaci da bayan zabe kadai ba. A`a rashin dimokuradiyya sahihiya cikin tafiyar da harkokin siyasar a kan kowane mataki da `yan siyasa ke yi shi ne ummal-aba`isin da yake kawo rigingimun siyasa a wannan dimokuradiyyar. Kamar yadda kowa ya sa ni har yanzu ba wata jam`iyya siyasa a kasar nan da ta yarda kuma ta ke aiwatar da tafiyarta a bisa tsarin dimokuradiyya ya yi tanadi, wato abar jama`a su zabi abin da suke so ba tare da karfa-karfa ba, kama daga zabubbukan fitar dagwani zuwa cin zaben baki dayansa. Muddin shugabanni za su rinka wannan karfa-karfa ta shigewa gaba su ce ga wanda zai tsaya takara ko ga wanda ya ci zabe alhali bai ci ba, to kuwa har yanzu akwai sauran rina a kaba, kuma hakan ka iya yin sanadin wargajewar dimokuradiyya din.
Su ma jami`an Hukumar zabe na INEC da na tsaro duk suna da nauyin da ke kansu, na tabbatar da gaskiya da adalci wajen bai wa wanda ya ci zabe nasararsa, ba a hada kai da su ba a mika nasara ga wanda bai same ta ba. Lallai kuma sai an rinka tabbatar da hukuncin da ya kamata akan dukkan jam`iyya da magoya bayanta da jami`an zabe da na tsaro da aka samu da laifin karya ka`idojin zabe. Don haka al`amarin na kowa da kowa ne, kuma sai kowa ya kama za akai ga nasara. Allah Ya ba mu ikon mu gyara amin summa amin.