Sai ’Yan Najeriya sun roki Buhari ya sake tsayawa takara – Oba Adedotun
Alake na lardin Ebga wanda shi ne basarake mai daraja ta daya a lardin da ke Jihar Ogun, Oba Adedotun Gbadebo ya bayyana cewa ’yan Najeriya za su nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya takarar Shugaban kasa a karo na biyu a 2019.Alaken ya yi wannan ikirarin ne a lokacin bukukuwan da masarautarsa ta shirya, […]
Alake na lardin Ebga wanda shi ne basarake mai daraja ta daya a lardin da ke Jihar Ogun, Oba Adedotun Gbadebo ya bayyana cewa ’yan Najeriya za su nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya takarar Shugaban kasa a karo na biyu a 2019.
Alaken ya yi wannan ikirarin ne a lokacin bukukuwan da masarautarsa ta shirya, domin murnar cikarsa shekaru 10 bisa karagar mulki; bukukuwan da aka kammala a ranar Alhamis din da ta gabata.
Oban, wanda babban jami’i ne da ya yi aiki da mataimakin Shugaba Buhari a lokacin mulkin soji, wato Tunde Idiagbon, ya yi kira ga masu sukar Gwmnatin Buhari da su sarara kadan, su kuma ba shi lokaci domin a cewarsa, shugaban mutum ne mai yin aikinsa a tsanake ba tare da gaggawa ba, kana da sannu zai cika dukkannin alkawuran da ya yi wa ’yan Najeriya a lokutan yakin neman zabe.
“Shugaba Buhari mutum ne mai zurfin tunani, sai ka yi ta yi masa magana na tsawon lokaci ba tare da ya ce maka ci kanka ba, ba kuma ya ko kale ka ya yi maka murmushi ba amma yana jin duk abin da kake nufi ya kuma fahimce ka sarai. Duk mutum mai zurfin tunani zai yi wuya ya yi ba daidai ba. Don haka ina sanar wa masu gajen hakuri cewa, matukar sun sarara sai sun roke shi da ya sake tsayawa takara a shekarar 2019 saboda sai ya mayar da kasar nan bisa turbar da muka dade muna fata.” Inji Oba Adedotun, wanda ya kara da cewa, Shugaba Buhari zai magance matsalar tattalin arziki da ta zamantakewar al’ummar kasar nan.
A karshe, ya yi kira ga Gwmnatin Tarraya da ta daga martabar cibiyar lafiya ta Gwmnatin Tarayya da ke Idi-Aba a Abekuta zuwa asibitin koyarwa kamar yadda aka yi a Jihar Benuwe, shekaru 10 da suka wuce.