Saima Mohammed ta amarce

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka daura auren fitacciyar jarumar fim din Hausa Saima Mohammed da angonta wani fitaccen dan siyasa a Jihar Kano Alhaji Aminu Labaran Baba.An daura auren ne a kofar gidansu amarya Saima da ke unguwar Gama Birgade a yankin karamar Hukumar Nasarawa cikin Jihar Kano.Rahotanni sun bayyana cewa […]

Saima Mohammed ta amarce
Saima Mohammed ta amarce

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka daura auren fitacciyar jarumar fim din Hausa Saima Mohammed da angonta wani fitaccen dan siyasa a Jihar Kano Alhaji Aminu Labaran Baba.
An daura auren ne a kofar gidansu amarya Saima da ke unguwar Gama Birgade a yankin karamar Hukumar Nasarawa cikin Jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da shagulgula da dama don murnar auren, inda aka karkare da walimar bikin a hotel din Protential da ke Jihar Kano.
Haka kuma an lura abokan sana’ar jarumar kadan ne suka halarci daurin auren tare da shagalin bikin, wadanda suka hada da Ali Nuhu da Jaruma Fati Bararoji da Zuwaira Abdusalam da sauransu.
Saima ta bayar da gudummawa mai yawa tsawon lokacin da ta dauka tana fitowa a fina-finai shekaru kusan goma sha biyar wajen ciyar da fina-finan Hausa gaba.
Fim din da ta fara fito a ciki wanda kuma shi ne ya haska ta shi ne fim din “kilu Ta Ja Bau” na Kamfanin Iyan-Tama Multi Media.
Idan za a iya tunawa jarumar ta dauki tsawon shekaru rabonta da fitowa a cikin fina-finai, inda ta bayyana wa manema labarai cewa ta mayar da hankalinta ne kan abin da ya shafi karatunta. Sai dai kwatsam masu kallo suka gan ta a wani fim din Jarumi Ali Nuhu mai suna  ‘Zuri’a’.