Sajoji sun kaddamar da juyin mulki a Gabon
Sojojin kasar Gabon sun hambarar da gwamnatin mulkin Shugaba Ali Bongo. Rahotanni na bayyana cewa, iyalan gidansa sun shafe shekara 50 suna mulkin kasar mai arzikin man fetur. Sojojin kasar da ke yankin yammacin gabar tekun Afirka ta tsakiya sun ce sun kaddamar da juyin mulki ne “domin dawo da demokradiyya”. Su karbe iko a […]
Sojojin kasar Gabon sun hambarar da gwamnatin mulkin Shugaba Ali Bongo.
Rahotanni na bayyana cewa, iyalan gidansa sun shafe shekara 50 suna mulkin kasar mai arzikin man fetur.
Sojojin kasar da ke yankin yammacin gabar tekun Afirka ta tsakiya sun ce sun kaddamar da juyin mulki ne “domin dawo da demokradiyya”.
Su karbe iko a babbar tashar talabijin ta kasar da karfe 4 na asuba agogon kasar (Karfe 3 GMT), kuma sun karanta wata gajeriyar sanarwa da ta bayyana cewa sun kafa “Majalisar Ceton Kasa”.
Shugaba Ali Bongo ya dare bisa karagar mulki a 2009 kuma ya shafe fiye da wata biyu yana jinya a wajen kasar.
Kamar yadda rahoton BBC ya sanar.