Saka wa kai marar fasali
Fadar Shugaban kasa ba ta musanta rahotannin da ke cewa saboda faduwar Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Shugaba Jonathan da Mataimakinsa Namadi Sambo da ministoci da mukarraban Shugaban kasa da wasu ’yan majalisar dokoki, sun ba wa kansu wasu kudaden alawus na sallama da suka kai Naira biliyan uku da miliyan 240 ba. […]
Fadar Shugaban kasa ba ta musanta rahotannin da ke cewa saboda faduwar Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Shugaba Jonathan da Mataimakinsa Namadi Sambo da ministoci da mukarraban Shugaban kasa da wasu ’yan majalisar dokoki, sun ba wa kansu wasu kudaden alawus na sallama da suka kai Naira biliyan uku da miliyan 240 ba.
Bayanan alawus din sallamar suna kunshe ne a wani kasafi na musamman kuma ba su shafi kudin sallama da albashi da Hukumar Rabon Arzikin kasa da Tsara Albashi (RMAFC) ta tanada ba.
Rahotanni sun ce, daga ranar da suka sauka daga mulki a ranar 29 ga Mayu, 2015, Shugaba Jonathan zai karbi ninki uku na tsurar albashinsa na shekara wato Naira miliyan 3 da dubu 514 da 705. Ke nan alawus din sallamarsa zai kama Naira miliyan 10 da dubu 554 da 115. Kudin sallamar Jonathan bai hada da sauran hakkokinsa da tsarin mulki ya ba shi a matsayinsa na tsohon Shugaban kasa ba.
Kudin sallamar Mataimakin Shugaban kasa Sambo ma nanki uku ne na tsurar albashinsa na shekara wato Naira miliyan 3 da dubu 31 da 572 da kwabo 50, hakan na nufin kudin sallamarsa zai kama Naira miliyan 9 da dubu 94 da 717 da Kwabo 50. Kamar Jonathan da Sambo, sanatoci ma za su samu ninki uku na albashinsu na shekara a matsayin alawus din sallama. Sanatocin da ba za su koma majalisa ba za su karbi jimillar Naira miliyan 462 da dubu 19 bayan karewar wa’adinsu a ranar 5 ga Yuni, 2015. Wannan na nufin kowannensu zai samu Naira miliyan 6 da dubu 79 da 200. Kimanin sanatoci 76 ne ba za su koma majalisar ba, imma saboda ba su tsaya takara ba, ko an kada su a zabe.
A Majalisar Wakilai, mambobi 290 ne ba za su koma majalisar ba a Majalisa ta 8 da za ta fara aiki bayan gwamnatin Buhari ta kaddamar da ita a ranar 5 ga Yuni, 2015. Kowanensu a cewar bayanan zai samu Naira miliyan 5 da dubu 955 da 637 da Kwabo 50.
A gefen ministoci, gaba dayansu za su karbi Naira miliyan 253 da dubu 967 da 215 da Kwabo 50. Akwai ministoci 42 a gwamnatin Jonathan, kowannensu zai karbi tsakanin Naira miliyan 6 da dubu 79 da 200 zuwa Naira miliyan 5 da dubu 872 da 740.
Mukarraban Shugaban kasa da suka hada da mashawarta na musamman da manyan masu taimaka masa da mataimaka na musamman za su karbi jimillar Naira miliyan 754 da dubu 207 da 125, kowanne an ninka tsurar albashinsa na shekara, sau uku.
Kudin sallama da kudin da aka amince a ba mai rike da mukamin siyasa a lokacin da wa’adin aikinsa ya zo karshe a tsare yake kuma na cikin takardar nada shi. Don haka a amince da kara masa wasu kudaden bayan wadannan tanade-tanade saboda kawai shi wani jami’i ne da yake kan wani matsayi da zai karya doka ta amfani da damarsa ba abin amincewa ba ne a karkashin doka.
Irin wannan keta doka da wawurar dukiya sun sa dimokradiyyar Najeriya ta zama mafi tsada a duniya, sakamakon yawan masu rike da mukaman siyasa da ba su hassala komai da ake nadawa a shekara 16 da suka gabata. dimbin mukarraban Shugaban kasa da ake maimaita su a jihohi wulakanta ikon da aka ba shugabannin ne.
Tsarin mulki, wanda ya amince da ministoci 42, daya daga kowace jiha da saura daga shiyyoyin siyasa ne ya jawo wannan tabargaza. Akwai bukatar a yi gyara ga wannan tanadi ya zamo mafi dacewa da tsarin ministoci na tarayya. Yawan mukarraban Shugaban kasa abin kunya ne, kuma akwai shakku kan amfaninsu idan aka kwatanta da bukatun kasa. Kuma majalisar zartarwa mai karancin mambobi za ta fi alfanu tare da samun nasarar gudanar da shugabanci nagari.
Wata gazawa a alawus din sallamar, ita ce zamanta bai-daya, duk yadda inganci aiki ya kai duk tsawon lokaci a aiki ga kasa, kawai Shugaban kasa ne zai bushi iska ya yi nadin.
A dokokin aiki sai mutum ya kai shekara akalla 10 kafin ya cancanci garatuti, fansho kuma sai ya kai shekara 15.
Akwai hanyoyi da suka kamata a bi don su dace da masu rike da mukaman siyasa zababbu da nadaddu, wajen tsara musu kudin sallama daga dukiyar jama’a. Abu ne mai daga hankali duk da tanadin da aka yi musu a karkashin doka, jami’an gwamnati su bai wa kawunansu karin dimbin kudin alawus a kasar da ma’aikata kamar malaman makaranta da suka shafe shekara 40 ko fiye suna aiki, amma a wasu lokuta suna mutuwa a kan layin neman a biya su hakkokinsu ba tare da sun samu ba. Idan manufar bullo da alawus din ga ’yan siyasa ita ce don a hana su satar dukiyar jama’a, saboda sanin za a saka musu a karshen wa’adinsu, to wannan ya gaza cimma manufa. Domin rahotanni sun nuna irin dimbin watandar dukiyar gwamnati da aka yi a shekara shida da suka gabata.