Sakaci na cikin dalilan da ke janyo cin hanci a manyan makarantu – Dokta Shettima
Shugaban Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Nasarawa a Jihar Nasarawa, Dokta Shettima Abdulkadir Sa’idu, ya ce nuna halin-ko-in-kula a wurin aiki tare da karya dokokin aiki su ne ke janyo cin hanci a manyan makarantun kasar nan.Dokta Shettima ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabin maraba a wurin taron kara […]
Shugaban Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Nasarawa a Jihar Nasarawa, Dokta Shettima Abdulkadir Sa’idu, ya ce nuna halin-ko-in-kula a wurin aiki tare da karya dokokin aiki su ne ke janyo cin hanci a manyan makarantun kasar nan.
Dokta Shettima ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabin maraba a wurin taron kara wa juna sani kan yaki da cin hanci da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shirya tare da hadin gwiwar kwalejin a karshen makon jiya. Dokta Sheetima Sa’idu ya ce “Abin damuwa ne kiraye-kirayen da muke ji daga wasu jama’a cewa cin hanci da rashawa da ke aukuwa a manyan makarantu ya wuce misali kuma yana bukatar a dauki matakin gaggawa a kai. Ba komai ne ke janyo wannan lamari ba, sai sakaci da aiki da karya dokoki.”
Dokta Shettima ya ce wasu daga cikin dalilan da suke janyo cin hanci sun hada da rashin zuwa wurin aiki a kan kari da shaye-shaye a lokacin aiki da rashin gaskiya da rikon amana da makamantansu.
Saboda haka sai ya yi kira ga ma’aikata su canja halayensu domin dalibansu su samu abin koyi mai kyau daga gare su.
Ya ce hukumar makarantar za ta ci gaba da karrama ma’aikatanta masu kwazo da nuna bajinta. Kuma ya yi gargadin cewa za su ci gaba da ladabtar da duk ma’aikacin da aka samu da sakaci da aiki.
A jawabin shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Mustafa Magu, ya ce hukumar ta shirya taron ne don ta wayar da kan ma’aikatan makarantar kan illar cin hanci.
Ibrahim Magu wanda shugabar sashin wayar da kan jama’a ta hukumar, Hajiya A’isha Larai Musa ta wakilta ya yaba wa shugaban makarantar kan hadin kan da ya ba su wajen ganin an cimma nasarar gudanar da taron.
Ya ce Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Nasarawa ita ce ta farko wajen yaki da cin hanci a bangaren ilimi a kasar nan.