Sakaci ne musabbabin tashin gobara a kasuwanni – Masana
An bayyana cewa rashin kulawa da sakaci da wadansu ‘yan kasuwa ke nuna wasu ne musabbabin mafi yawan gobarar da ke faruwa a kasuwannin kasar nan.‘’Akwai bukatar wayar wa da jama’a, musamman ‘yan kasuwa kai, a kan mahimmancin kashe kayan wuta da suke amfani da su a cikin shagunansu a kafin su tafi gidajensu na […]

An bayyana cewa rashin kulawa da sakaci da wadansu ‘yan kasuwa ke nuna wasu ne musabbabin mafi yawan gobarar da ke faruwa a kasuwannin kasar nan.
‘’Akwai bukatar wayar wa da jama’a, musamman ‘yan kasuwa kai, a kan mahimmancin kashe kayan wuta da suke amfani da su a cikin shagunansu a kafin su tafi gidajensu na kwana.’’
Muhamamdu Mustapha Rilwanu shi ne Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ya bayyana cewa,” Mutane suna barin kayan wuta a kunne ba tare da sun kashe ba. A wadansu wuraren kuma za ka tarar ana girke-girke a cikin kasuwanni. Haka kuma wasu sukan sha taba su yar da guntun a hanya ba tare da kashewa ba. To duk wadanan za su iya kawo tashin gobara.”
Game da matakin da ya kamata a dauka don guje wa abkuwar irin wanan gobara a nan gaba, shugaban ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su rika kula tare da kiyaye duk wadanann abubuwa da na lissafa a sama. Kafin mutum ya bar shagonsa ya tabbatar ya kashe duk wani abu na wutar lantarki da ke cikin shagonsa.
Haka kuma dole a daina girke-girke a kasuwanni. Masu shan taba suna yar wa a cikin kasuwanni muna kira gare su da su daina. A duk lokacin da mutum ya sha taba ya tabbatar ya kashe ta kafin ya yar. Haka su ma jama’a nauyi ne a kansu a duk lokacin da suka ga wani ya yar da tabar da ba ta mutu ba to su yi masa magana ko kuma su su kashe da kansu don gudun sake faruwar irin hakan a nan gaba” Inji shi.
Shi ma wani jami’in Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna, Umar D. Aliyu, ya ce gobara ta fi faruwa ne da daddare, shi ya sa ta fi barna. “ Misali, abin da ya faru a kasuwar Sabon gari na Kano abin damuwa ne matuka, domin gobarar ta faru ne cikin dare.’’
“ Shi ya sa muke jan hankalin jama’a da su rika lura tare da kawar da duk wani abu da ke iya janyo gobara, domin gobara daga kadan take farawa kafin ta zama wani abu babba. Ga misali, masu dafa shayi ko indomi ko kuma masu dafa abinci, a wadansu lokuta sukan mance ko su yi sakaci wajen kashe wutar murhu, wanda ga shi yanzu muna cikin yanayin zafi ne, abu kadan ke iya janyo gobara. Idan jama’a za su rika lura tare da kiyaye dokoki abin na iya raguwa. ‘Yan kasuwa akwai bukatar su rika barin hanyoyin mota da aka tanadar na shiga cikin kasuwa, ta yadda idan gobara ta tashi motar kashe wuta za ta samu damar wucewa. Domin rashin barin hanya tare da toshe hanyoyin mota a cikin kasuwannin na daya daga cikin matsalolin da muke fuskata. Sannan muna kara jan hankalin jama’a da su rika kashe wutar dafa abinci ko na shayi da suke amfani da su a cikin kasuwanni. Yin haka yana da mahimmanci matuka,” inji shi.
Shi ma Sulaiman Garba, wanda jami’an kashe gobara ne a Kaduna, kara yin kira ya yi ga ‘yan kasuwa da su daina kafa shaguna a ,kan hanya sannan su rika ba da goyan baya a duk lokacin da jami’an kashe gobara suka je yin aikinsu.
“Mukan samu matsala da jama’a a wadansu lokuta idan muka je kashe gobara, saboda wadansu suna taruwa ne kawai domin wata manufa tasu, kuma sai su nema hana mu yin aikinmu. Don haka kira da zan yi shi ne, jama’a su daure su rika bamu goyan baya tare kuma da bin dokokin kashe gobara ko hana tashin a cikkin jama’a. Sannan muna kira gare su da su rika ajiye kayan kashe gobara a kasuwanni, musamman wanda ake fesawa. Ajiye irin wadannan kayan aiki na matukar taimakawa. Saboda haka akwai bukatar ‘yan kasuwa su fahinci mahimmancin ko hadaarin da ke tattare da gobara ta hanyar kiyayewa,” inji shi.
Yadda hutun ista ya taimaka wajen jawo asara a kasuwar Sabon Gari
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata hatsabbibiyar gobar,a wacce har zuwa yanzu ba a gano musabbabinta ba ta tashi a kasuwar Sabon gari, inda ta kone fiye da kashi 80 na kasuwar. Kamar yadda Shugaban kungiyar ‘Yan kasuwa na Sabon gari Alhaji Alin Bagadaza ya shaida wa Aminiya. “duk da cewa ‘yan kasuwa suna kiyasta cewa sun yi asarar kimanin kayayyaki na Naira triliyan biyu, a magan ta gaskiya, Allah ne kadai ya san abin da aka yi asara a wannan gobara. Babu shakka ‘yan kasuwa sun yi asara kwarai da gaske.”
Shi ma sguhaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) Alhaji Sani Sidi, ya bayyana cewa akalla shaguna 3,800 ne suka kone a gobarar, haka kuma akalla mutane 15 ne suke kwance asibiti sakamkon samun raunuka da kuma shakar hayakin gobarar da suka yi.
Sani Sidi ya bayyana wanann gobara a matsayin babbar gobara da ba a taba yin irinta a kasuwannin kasar nan ba, sai dai ya yi wa ‘yan kasuwan alkwarin cewa kawanan nan za su samu taimako daga hukumarsa.
Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhamamd Sanusi II, wanda ya katse ziyarar aiki da yake yi a kasar Ingila ya dawo gida, kira ya yi ga gwamnatin Kano da ta binciki dalilin yawaitar tashin gobara da ake samu a jihar, tare da kokarin sake gina kasuwannin da ke jihar don zamanantar da su da kuma ba su kariya.
Sarkin ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da su rungumi tsarin gudanr da kasuwanci na inshorar Musulunci (Takaful), wanda zai ba su damar mayar da abin da suka rasa a lokutan da wata waki’a ta abku.
Tuni dai gwamantin Jihar Kano karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta kafa kwamiti mai mutum 9, karkashin jagoramncin Alhaji Alin Bagadaza da nuf in gano asarar da aka tafka a kasuwar da kuma hakikanin ‘yan aksuwan da gobarar ta shafa. Gwamnatin ta bai wa kwamitin wa’adin kwanaki biyar ya mika rahotonsa .
‘Yan kasuwa sun yi asarar dimbin dukiya da suka hada da kayayyakin sayarwa da kuma tsabar kudi wadanda suka ajiye a shagunansu.
Alhaji Usamatu Bala ya ce ya yi asarar tsabar kudi sama da Naira miliyan hudu a gobarar, sakamakon ajiye kudin da ya yi a shagonsa. “kasancewar ranar Juma’a ba aiki (hutun ista), don haka muka ajiye kudin da muka yi ciniki a cikin shago da nufin idan an gama wanann hutun mu dauki kudin mu kai banki, to sai kuma ga abin da Allah ya aiko.”
Wani dan kar zare da sauran kayan dinki, Alhaji Hafizu Gimba, ya yi asarar tsabar kudi kimanin Naira miliyan 80, baya ga kayayyaki da suka kone a wutar, wadanda kimarsu ta kai Naira miliyan dari biyu a rumfunansa guda 12, wadanda ke shake da kaya. Kamaryadda yaronsa karibu Isma’il Ibrahim ya shaida wa Aminiya.”
Alhaji Tanko Mai zare shi ma ya tafka asara, wacce yawanta ya kai kimanin Naira miliyan dari baya, ga tsabar kudi da suka kai Niara miliyan 20, wadanda dukkansu suka kone kurmus a wannan gobara.
Shi ma Alhaji danladi A.D Mai zare kayansa sun kone kurmus a shagunansa guda shida da ke cikin kasuwa. “Ina da shaguna guda goma a wannan kasuwa da suka kone kurmus, babu abin da aka iya dauka a shagon. Komai na shagunan ya kone wanda kiyasin kudinsu ya aki kimanin Naira miliyan dari”
Mista Jonah Oghechikwu, wanda yake sayar da kayayaykin lantarki da suka hada da talbijin da sauransu, ya ce, baya ga kayan da ya yi asara haka kuma ya rasa tsabar kudi na Naira miliyan 12. “Wannan gobara musiba ce kawai da Allah Ya kawo ta, wanda muke neman sauki daga gare Shi. Baya ga kayan da na rasa na kayyayaki haka kuma na rasa tsabar kudi har Naira miliyan 12 kasancewar babu aiki a ranar Juma’a. hakan ya sa ba mu kai kudi banki ba” Inji shi
Shi ma Alhaji Abdul’zeez Mai agogo yana daga cikin wadanda suka tafka dimbin asara, wani babban yaronsa dahiru ya bayyana wa Aminiya cewa, “ Ba za mu iya fadin cewa ga yawan asarar da muka yi ba, amma asarar tana da yawan gaske. Don akalla an yi asarar dukiya ta kusan biliyan daya”.
Alhaji Sani Mohammad Aminu wanda ke sayar da tangaraye, ya bayyana cewa ya yi asarra fiye da Niara miliyan 15 a shaguna guda uku da ya mallaka a cikin kasuwar. “Muna sayar da kayayyakin amfanin kicin a shaguna guda uku wadanda an wayi gari yau duk sun kone a wanan gobara, babu abin da muka dauka.’’
Mista Dunatis Obi dan kasuwa ne da ke sayar da takalma da jakunkuna, ya ce, “Na yi asarar dukiya ta kai ta Naira miliyan hudu a wanann gobara. A yanzu haka kudin da za mu ci abinci ba mu da shi.’’
Wani dan kasuwa mai suna Auwalu Ibrahim wanda ke sayar da kayayyakin da suka hada da bargo da tawul da lema da sauransu ya bayyana cewa ya yi asarar dukiya tsakanin tsabar kudi da kuma kayayyaki har na Nairamiliyan goma.
‘Yan kasuwan sun nemi gwamnati ta sa ido game da masu gadin kasuwa, domin ana shigowa kasuwa ana ba su cin hanci. “ya kamata gwamanti ta samar da tsaro na musamman a kasuwar nan, yadda za a rika sanya ido game da abubuwan da ke tafiya a kasuwar.
Alhaji Abdullahi Mai Gwal Kurna, yana daga cikin wadanda wannan ibtila’in gobara ya abkawa, ya ce, “A ranar da gobarar ta tashi aka kawo min kayan gwal na Naira miliyan dari uku da hamsin wanda kuma duk wutar ta kone su. Duk da cewa za a iya morar wasu daga ciki, wasu kuwa an riga an yi asararsu ba za su moru ba ko kadan. Kin san shi gwal idan wuta ta taba shi iyakaci ya yi baki wanda idan aka wanke shi zai koma kamar yadda yake a da, amma idan wuta ta yi masa yawa yakan narke ya zagwanye yadda ba za a iya mora ba,” Inji shi.
Yawancin yan kasuwar sun nuna farin cikinsu game da matakin da gwamnatin Jihar Kano ta dauka game da sake gina kasuwar.
Sarkin Kasuwar Sabon Gari Alhaji Nafiu Nuhu Indabo, ya bayyana cewa har yaznzu ba su gano dalilan da suka haddasa gobarar a kasuwar ba.
Gobarar Birnin Kebbi na da ban mamaki
Bashir Lawal Zakka, daga Birnin Kebbi
Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar Birnin-kebbi ta janyo asarar bilyoyin kudi. Ita dai wannan gobara, ta tashi ne da misalin karfe goma 12 na dare ranar juma’a da ta gabata, har zuwa misalin karfe 4 na asuba.
Alhaji Umaru dan-Gura Gwandangaji, shugaban “yan kasuwa na jihar Kebbi ya shaida wa wakilinmu cewa, wannan gobara Allah ne ya kaddara haka, saboda kasuwar ba ta da wutar lantarki ballanta a ce ita ce sanadiyar wannan gobara, amma kuma jama’a na tsammanin dalilin wannan gobara ta faro ne daga shagunan da ake ajiye gas na yi dafuwa. Domin a lokacin da gobara ta tashi babu wani mahaluki da ke cikin kasuwar ballanta nama a yi hasashen ko maisu shaya ne suka haddasa gobarar, watakila kuma ko ta hanyar jefar da wutar taba.
A bincika kila akwai makarkashiya – Sheikh Jingir
Salihu Makera da Hussaini Isah a Jos
Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci hukumomin kasar nan su gudanar da bincike sosai game da yawan aukuwar gobara a kasuwannin kasar nan musamman na Arewa domin gano musababbinta.
Sheikh Sani Yahya Jingir wanda ya shaida wa wakilanmu haka a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke Jos, ya ce yadda ake yawan samun gobara a kasuwannin abin dubawa ne, inda ya ce ya kamata a fara tunanin ko akwai wata makarkashiya ta karya tattalin arzikin jama’a musamman na Arewa ganin an kasa karya su ta amfani da Boko Haram.
Ya ce, “ A yanzu misali ga gobara ana ta kone dukiyoyin al’ummar Musulmi a birnin Kano da Gombe da Birnin Kebbi da sauran garuruwa. Sai abin ya zame mana kamar akwai wata tsarga. Yau za a ce kusan shekara 20 a sashi guda ake yin wannan gobara kuma a tsakar dare. Sannan gobara mai abin mamaki wuta ta tashi a kasa ganewa ashana aka kyasta mata ko me, sai dai a ji kara na tashi wani abu kamar bam yana tashi. Anya gobarar nan ta gaskiya ce ko ta mugunta ce?”