Sakacin gwamnati ya jawo kasa magance rikicin Boko Haram cikin lokaci – Gwamna Gaidam

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce sakacin da gwamnatin baya ta nuna ne ya jawo aka kasa magance rikicin Boko Haram har hakan ya haifar da halin da aka shiga na karuwar ’yan kungiyar suka samu karfin da suka buwayi yankin Arewa maso Gabas da bangarorin wasu kasashen makwabta.Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana […]

Sakacin gwamnati ya jawo kasa magance rikicin Boko Haram cikin lokaci – Gwamna Gaidam
Sakacin gwamnati ya jawo kasa magance rikicin Boko Haram cikin lokaci – Gwamna Gaidam

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce sakacin da gwamnatin baya ta nuna ne ya jawo aka kasa magance rikicin Boko Haram har hakan ya haifar da halin da aka shiga na karuwar ’yan kungiyar suka samu karfin da suka buwayi yankin Arewa maso Gabas da bangarorin wasu kasashen makwabta.
Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi ga manyan hafsoshin tsaron kasar nan a ziyarar da suke kai jihohin da rikicin Boko Haram ya dabaibaye a karkashin jagorancin Mai ba Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Tsaro Manjo Janar Babagana Manguno (mai ritaya) a Damaturu.
Gwamnan ya ce duk wanda ya san tarihin kungiyar Boko Haram ya san ta fara tayar da kayar baya ne tun shekarar 2009 lokacin da ta kai hari a garin Kanemma a Jihar Yobe, amma Gwamnatin Tarayya a karkashin Jam’iyyar PDP ta gaza daukar matakin shawo kan lamarin da gangan tun kafin su kawo ga haka.
Don haka a cewar Gwamnan tunda a yanzu Allah Ya kawo gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya hakkake cewa karshen kungiyar Boko Haram ya zo, ganin yadda shugaban ya dauki lamarin tsaro da matukar muhimmanci.
Gwamna Gaidam ya yi godiya game da ziyarar da ya ce mai matukar muhimmanci da manyan hafsoshin tsaron suka kai ziyara jihar wanda shi ne na farko a tarihin jihar.
Ya ba su tabbacin cewa gwamnati da al’ummar jihar za su ci gaba da ba su goyon baya don samun nasara a kan ayyukansu, inda ya yi musu addu’ar Allah Ya ba su nasara a kan ’yan ta’addan.
Tun farko da yake jawabi Manjo Janar Babagana Manguno ya ce sun ziyarci jihar ne domin tattauna wannan matsala ta tsaro kan rikicin Boko Haram da ya tsaya a makogoron kasar nan da wasu makwabtan kasashe.
Ya ce daga tabbatar musu da mukaman manyan hafsoshin tsaron kasa ne suka yanke shawarar kai ziyara wuraren da rikicin ya fi shafa kai-tsaye don neman goyon baya.
Ya roki Gwamnan da al’ummar jihar su basu goyon baya dangane da kudirinsu na ganin an kai ga nasarar kawo karshen rikicin kungiyar Boko Haram.
Janar Monguno ya ce ya kamata a sani cewar wannan yaki daban yake da irin yakin da suka sani domin suna fuskantar yaki ne da wadanda ba a sansu ba amma da yardar Allah dakarun kasar nan za su samu nasara a kansu.