Sakacin Ma’aikatar Ilimi ya jawo kotu ta kori wata malama daga gidanta

Rashin daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta yanke game da mallakar wani gida da wata malamar makarantar sakandaren Jibril Aminu da ke Bauchi, mai suna Nene G. Pineda wadda ’yar kasar Filifins ce ya jawo an kore ta daga gidan bayan ta shekara 25 a cikinsa.Malamar wadda ta shafe fiye da shekara 30 […]

Sakacin Ma’aikatar Ilimi ya jawo kotu ta kori wata malama daga gidanta

Nene tana gyara kayanta da aka watso daga gidan da kotu ta fitar da ita. Rashin daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta yanke game da mallakar wani gida da wata malamar makarantar sakandaren Jibril Aminu da ke Bauchi, mai suna Nene G. Pineda wadda ’yar kasar Filifins ce ya jawo an kore ta daga gidan bayan ta shekara 25 a cikinsa.
Malamar wadda ta shafe fiye da shekara 30 tana koyarwa a makarantu daban-daban na Gwamnatin Jihar Bauchi an sayar da gidan da take zaune ne ga wani malami mai suna Ahmed Umar Madara.
Daraktan Hukumar Kula da Makarantun Musamman na Jihar Bauchi Malam Ibrahim Bunu ya ce an samu kuskure wajen jinkirin daukaka kara game da umarnin da Babbar Kotu ta Biyu mai lamba CRC No. 0377285 ta ranar 15 ga watan Yuli, 2013 mai dauke da sa hannun Mataimakin Babban Magatakarda Ibrahim Yusuf inda ta umarci Nene G. Pineda ta bar gidan da take zaune mai lamba 23 a rukunin gidaje na Ibrahim Bako da ke Bauchi cikin kwanaki 30.
Ya ce an samu jinkiri daukaka karar kuma ba a samar mata da wani gida da za ta komaba, saboda sun sakankance kan an sake rubuta wa Ahmed Madara wasika mai lamba MHE/OFF/42 daga ofishin Shugaban Ma’aikata wacce Mukhtari Hamidu Alhaji ya sanya hannu a madadin Shugaban Ma’aikata a ranar 23 ga Janairu 2009, wadda ke bayanin an janye ba shi wannan gida da aka yi a shekarar 2008 cikin wasika mai lamba GO/GA/S/EST/4/T.12.
Ya ce tsarin aikinta shekara uku ne aka rika kara mata da haka har ta shekara 32 tana aiki, kuma lokacin da aka zo sayar da gidajen ba a yi la’akari da tana zaune a ciki ba, sai aka sayar ga wani amma daga bisani aka janye sayar masa shi kuma ya kai kotu.
Ya ce sakacin hukumar da take yi wa aiki ne ya jawo har aka sayar da gidan ga wani, inda ya ce ya kamata sai idan ba ta so ne za a sayar ga wani mutum ko kuma idan ba za ta iya saye ba ko kuma an sama mata wani gida.
Alhaji Bunu ya ce lokacin da aka watsar da kayanta a waje, Hukumar Makarantun Musamman ta yanke shawarar kama mata daki a wani otel amma aka ga sun fi karfin dakin otel din, amma yanzu tana kokarin neman gida a wuri mai kyau da ke da tsaro don a sanya ta a biya haya na shekara biyu ko uku.
Ya ce saboda babu gidajen gwamnati a halin yanzu, makarantunsu na Kafin Madaki da Azare da Toro da firamare uku da ke cikin garin Bauchi da ba su da gidajen malamai.
Nene ta ce tun watan Oktoban 1981 aka dauke ta aiki a jihar inda ta fara da koyarwa a Nafada, a 1992 aka dawo da ita Bauchi aka ba ta gidan da ake magana. Ta ce tun a shekarar 2005 aka ce an ba Umar Madara gidan ta fita ba tare da an ba ta wani ba, amma da ta koka Shugaban Ma’aikata ya janye bayar da gidan aka dawo mata da shi ta ci gaba da zama, amma ba ta san me ke faruwa ba sai a 2013 bayan ta dawo hutu sai aka ba ta takardar cewa ta fita ta bar wannan gida alhali ta yi aikin da ya dace idan sayarwa ne a ce an sayar mata gidan. Ta roki hukumomin da za su iya bi mata hakki su taimaka don ceto ta daga wannan abin takaici.