Sakacin malamai ke jawo zalunci a Najeriya – Sheikh Adamu Tsoho

Sheikh Adamu Tsoho Ahmad shi ne jagoran magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky a shiyyar Jos, a ranar Asabar da ta gabata ya halarci taron maulidin da suka shirya a garinn Saminka a Jihar Kaduna, kuma ya tattauna da wakilinmu inda ya ce matsalar Boko Haram makirci ne aka kulla wa Najeriya. Kuma ya ce malamai […]

Sakacin malamai ke jawo zalunci a Najeriya – Sheikh Adamu Tsoho
Sakacin malamai ke jawo zalunci a Najeriya – Sheikh Adamu Tsoho

Sheikh Adamu Tsoho Ahmad shi ne jagoran magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky a shiyyar Jos, a ranar Asabar da ta gabata ya halarci taron maulidin da suka shirya a garinn Saminka a Jihar Kaduna, kuma ya tattauna da wakilinmu inda ya ce matsalar Boko Haram makirci ne aka kulla wa Najeriya. Kuma ya ce malamai ne ba su sauke nauyin da ke kansu ba, shi ya sa ake zalunci da danniya a Najeriya:

Aminiya: Me Malam zai ce kan yakin da gwamnati ke yi da kungiyar Boko Haram a halin yanzu?
Sheikh Adamu Tsoho: To, mu dai gaskiya a matsayinmu babu wata kungiya wai ita Boko Haram wadda take son tabbatar da shari’a a Najeriya kamar yadda suke fada. Domin addinin Musulunci bai yarda a yi ta kashe rayukan mutane ba tare da hakkinsu ba. Mu abin da muka sani kan wannan al’amari shi ne wannan abu na Boko Haram da ke faruwa na daya daga cikin makircin Yahudawa da suke amfani da gwamnatin kasar nan wajen aiwatarwa. Tunda a nan Arewacin Najeriya akwai arziki kuma nan ne cibiyar addinin Musulunci a Najeriya kuma a nan ne mutane suka fi yawa. Don haka suka yanke shawarar bari su yi amfani da wannan yanki wajen cimma burinsu na kwasar arzikin da ke wannan yanki da dakushe yunkurin addinin Musulunci da yake tasowa a yankin. Don haka suka fito da sunan addini domin su yaki Musulunci da sunan Musulunci. Kuma kamar yadda na fada dangane da arzikin da muke da shi a wannan yanki, tun daga Sakkwato har zuwa Maiduguri da Yola arzikin man fetur da zinare da sauran ma’adanai ne kwance a kasa. Da ma Amurka da sauran kasashen Turai idan suna son su kwashi arzikin da ke cikin wata kasa sukan shiga kasar ne ta hanyar hada rikici, su tafi kasar a matsayin masu raba rikicin, daga nan sai su yi amfani da wannan dama su rika kwasar arzikin kasar. Misalin irin wannan abu ya faru a kasashen Iraki da Afghanistan da Libya, kuma haka suke son su yi a Najeriya don haka suka kulla wannan makirci na Boko Haram da gwamnatin Najeriya. Tuntuni suka so su yi haka sauran gwamnatocin da suka gabata amma suka ki yarda. Sai a lokacin wannan gwamnati ta Goodluck Jonathan ya yarda suka samu wannan dama. Irin wannan al’amari na Boko Haram shi ne yake faruwa a kasashen Siriya da Yemen da Afghanistan da Libya da Somaliya, don haka wannan al’amari na Boko Haram makirci ne aka kulla wa Najeriya. Dangane da yakin da gwamnatin Najeriya take yi da wannan kungiya ta Boko Haram a halin yanzu, yau shekarar wannan masifa ta Boko Haram ya kai biyar, amma tunda farko gwamnati ba ta yi wani abu ba. An kashe dubban mutane tare da tayar da garuruwa da lalata dukiyar jama’a da sace mutane maza da mata da yara kanana a jihohin Barno da Yobe da Adamawa. Amma duk ba a yi wani abu ba, sai yanzu ne za su ce za su yi wani abu? Wannan siyasa ce kawai saboda an ga lokacin zabe ya zo, ana son a yi amfani da wannan al’amari domin a samu kuru’un ’yan Najeriya.
Aminiya: Me za ka ce kan taron da aka shirya wa wasu malaman Musulunci kwanakin baya a Kaduna inda aka yi zargin an ba su kudi don su goyi bayan gwamnati mai ci a zabe mai zuwa?
Sheikh Adamu Tsoho: Wannan taro yana daga cikin abubuwan bakin ciki da duk Musulmi mai kishin addini zai yi bakin ciki da shi. Saboda a kullum idan ka ga mutane suna cikin zalunci da danniya idan ka duba za ka ga malamai ne ba su sauke hakkokin da suka rataya a wuyansu ba. Idan ka ga haka ta faru za ka samu malamai ko sun zama ’yan kallo ko kuma sun zamo ’yan rakiya kan zaluncin da ake yi wa al’umma. Don haka wannan taro wani babban abin takaici ne, domin an shirya shi ne don raba wa malaman kudi a yi amfani da su wajen ci gaba da mulkin zaluncin da ake yi a kasar nan.
Aminiya: To, mene ne mafita kan wannan hali da ake ciki?
Sheikh Adamu Tsoho: Mafita kan wannan hali da muka shiga shi ne mu koma zuwa ga addinin Musulunci. Domin addinin Musulunci ya ba mu sharudda kan shugabanci, ba kowa ne zai zamo shugaba ba. Dole ne a samu shugaba mutum ne mai imani da tausayi da sadaukar da kai da lokaci wajen yi wa al’umma hidima. Don haka babban abin da zai fitar da mu daga halin da muke ciki a kasar shi ne komawa zuwa ga addinin Musulunci. Domin mu samu shugabanni masu gaskiya da tsoron Allah wadanda za su yi adalci a cikin al’ummar kasar nan.