Sakacin shugabannin Arewa ne ya kashe kamfanin jaridun New Nigerian – Sheikh Jingir
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikmatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce masu sakaci ne suka kashe kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke Kaduna. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin cika […]
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikmatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce masu sakaci ne suka kashe kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke Kaduna.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin cika shekara daya tare da karrama wasu fitattun mutane da kamfanin buga mujallar Sahlan ya shirya a garin Jos.
Ya ce abin da takaici ganin irin kokarin da marigayi Sardauna Ahmadu Bello ya yi wajen kafa kamfanin buga jaridun domin kare muradun al’ummar Arewa, amma a yanzu shugabanin Arewa suna ganin wannan kamfani a rufe, sun kasa yin wani kokari don ganin ya farfado.
Ya ce babu shakka an cutar da talakawan Arewa kan dakatar da buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo, sakamakon rufe kamfanin. “Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ita ce jarida ta farko ko mafi dadewa a Arewa amma abin takaici an kashe wannan jarida,” inji shi.
Ya ce da yardar Allah jaridun kamfanin New Nigerian za su dawo ko wadannan masu sakaci sun so ko ba su so ba.
Sheikh Jingir ya yi kira ga al’ummar Arewa su natsu su san irin matsayin da Allah Ya ba su na yawan al’umma a Najeriya. Ya ce “Ya kamata mu san matsayin da Allah Ya ba mu. Mutumin da Allah Ya bai wa dan Adam, ya fi mutumin da Allah Ya ba wai man fetur. Don haka mu mutanen Arewa, Allah Ya ba mu baiwar da babu wanda da ya isa ya taka mu matukar muka fahimci kanmu.”
Sheikh Jingir ya yaba wa mujallar Sahlan, inda ya ce babu shakka a shekara daya da mujallar ta yi ta samu gagarumar nasara. Ya yi kira ga al’ummar Arewa musamman masu hannu da shuni da ’yan Boko su bude kamfanonin watsa labarai don kare mutunci da muradunsu.
Tun da farko a jawabin shugaban mujallar Malam Muhammad Shafi’u Yukub ya ce sun shirya taron ne don karrama fitattun mutanen da suka hada da Sheikh Sani Yahya Jingir da Mai Fune Alhaji Saleh Idris Bin Usman da Daraktan ’Yan agajin Izala na kasa, Alhaji Isah Waziri Muhammad Gombe da Khadi Abdulmumin da Honarabul Idris Ahmed Maje kan gudunmawar da suke bayarwa a bangarori daban-daban na ci gaban al’ummar kasar nan.
Ya ce a shekara daya da fara buga mujallar sun samu nasarar wayar da kan jama’a game da harkokin addinin Musulunci tare da sanya wa mutane son karance-karance musamman kan abin da ya shafi labarai.
Har’ila yau ya ce kamfanin ya samu nasarar samar wa jama’a makarantar koyar da ilimin kwanfuta, inda ya yi kira ga jama’a su tallafa wa kamfanin da kayan aiki da abubuwan hawa tare da ba shi tallace-tallace domin ya tsaya da kafafunsa ya ci gaba gudanar da ayyukan da ya sanya a gaba.