Sakacin ’yan sanda ne ya jawo kashe-kashe a Zamfara -Sanata dansadau

Sanata Sa’idu dansadau ya bayyana dalilan da yake ganin su ne suka jawo yawan kashe-kashen da ke faruwa a jihar Zamfara a yayin da yake hira da wakilinmu. Ga yadda hirar ta kasance. Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau Aminiya: A ganinka  me yake sanyawa  ake samun asarar rayukan mutane a wannan jihar ta hanyar kashe su […]

Sakacin ’yan sanda ne ya jawo kashe-kashe a Zamfara -Sanata dansadau
Sakacin ’yan sanda ne ya jawo kashe-kashe a Zamfara -Sanata dansadau

Sanata Sa’idu dansadauSanata Sa’idu dansadau ya bayyana dalilan da yake ganin su ne suka jawo yawan kashe-kashen da ke faruwa a jihar Zamfara a yayin da yake hira da wakilinmu. Ga yadda hirar ta kasance.

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Aminiya: A ganinka  me yake sanyawa  ake samun asarar rayukan mutane a wannan jihar ta hanyar kashe su da sunan fashi da makami?
dansadau: Nafarko shi ne idan ka lura kashe-kashen mutane da ake yi da asarar rayuka suna faruwa ne a wuraren da ke makwabta da gandun daji, su masu wannan ta’asan  nan ne kawai za su samu maboya su yi kwana da kwanaki ko shekaru a ciki don za a sha wahala wajen gane su ko  kama su, kuma duk inda ake kashe-kashen nan a shekara biyu da suka wuce duk suna makwabtaka da inda manyan dazuzuka suke ne.
Abu na biyu shi ne, kusan kashi saba’in  na wadanda aka kama a fashi da makami ko wadanda suke wannan ta’asa za ka samu  fulani ne.
Aminiya: Me ya sa ka ce Fulani ne ?  
dansadau: Abin da ya kawo wannan shi ne, akasarin fulani yanzu wadanda a da suna da garken shanu ashirin ko talatin,yanzu ko bindi ba su da shi, shanun sun kare, wadansu saboda fari, wadansu
 babu sana’ar da suka iya sai kiwo,kuma dama  a cikin daji suke idan ka ganshi a cikin gari wani abu zai saida. Yayin da suka rasa sana’ar kiwo baragurbinsu sai suka shiga muguwar  sana’ar ta fashi da makami. Wannan ne ya sanya mutanen kowane kauye suka dauki matakin kare kansu da kansu don hukuma ta gaza kare su, sau da yawa mutane a kauyuka za su kama barawo da hannunsu su ba ‘yansanda, bayan kwana uku sai ka ga barawon nan ya dawo,sai shi wannan barawo ya gayyato mutane ‘yan uwansu ‘yanfashi su zo su bi dare su karkashe mutane .
Aminiya: Kana ganin rundunar ‘yansanda ta kasa yin aikinsu ke nan ?
dansadau: Eh mana! Jama’a na ganin cewa rundanar ‘yansanda da alkalai sun kasa bin diddigin abin da yake faruwa ko ya faru a lokacin da suke binciken mai laifi su hukunta su,shi ne ya sa mutane suke yi wa kansu kariya tun da hukuma ta kasa kare su. Don barayi suna samun kariya daga ‘yansanda da kuma sauki ta bangaren hukuma,shi ne su ke bin kauyuka suna kashe mutane, musamman masu hannu da shuni, don sune abokan gabarsu, su kashe su su kwashe dokiyoyinsu,don yanzu noman da ake yi da shanu ya gagara, don babu kashi casa’in cikin dari na shanun da muke noma da su wadansu an sace, wadansu kuma masu su sun saida, don idan ba ka saida ba cikin gidanka za a zo da bindiga a tayar da kai ka kora shanunka har sai sun fita wajen gari su barka ka dawo. Babban dalilin wannan kashe-kashen shi ne kasawar hukumar ‘yansanda wajen kama su ta gurfanar da su gaban kotu, ita kuma kotu ta bi didigin yadda ya kamata a hukunta mai laifi yadda ya kamata,wadannan abubuwan su suka gagara,ya sanya yau a kashe mutum biyu, gobe biyar. Yau gashi an wayi gari sai a kashe sama da mutum hamsin ko a sanya wa  garin wuta baki daya, sai wanda Allah Ya tsirar ya gudu, wanda kwanan shi kuma suka kare ya mutu, kamar yadda ya faru a Kizara a kwanan nan.
Aminiya: Ko  kuna da labarin an kama wadanda suka kashe mutane a dansadau, kuma ko  an hukunta su?
dansadau: Bincike ya nuna a wannan kashe-kashen na dansadau bayan lokacin Ali kwara ya zo kun buga a jaridunku na  Hausa da ta turanci da wadansu Jaridu cewa, barayin nan matar wani dansanda ce  take dafa musu abinci,  babu wani abu da ake nema na hujjar cewa akwai kasawar ‘yansanda a cikin wannan al’amari, don haka akwai hadin baki da miyagun ‘yansanda wadanda ba sa kishin kasa, ba su da imani a cikin wannan ta’asa da ake yi a Zamfara. Wani abun al’ajabi shi ne, lokacin da Ali kwara ya zo ya bayyana cewa,  makaman da bararayin ke amfani da su ana dauko su ne daga cikin runbun ajiye makaman ‘yansandan Jihar Zamfara ake ba ‘yan fashi da makaman, kuma an kama wanda ke kula da wannan runbun,  amma har yanzu babu wanda ya ji hukuncin da aka yi, ba a kai shi kotu ba, ballantana a ce an yanke masa hukunci.  Irin wannan abu da hukumar ‘yansanda take yi shi ya sa wannan ta’asa ta ki ci, taki cinyewa. Idan da gaske ne ya kamata duk jami’in tsaron da  aka kama a hukunta shi a gaban Jama’a kowa ya gani,wannan shine zai sa idan akwai irinsa a cikin ‘yansandan ya razana.
Muna da labarin cewa idan yau aka tona dansanda wanda ke tare da barayi sai mu ji an yi masa canjin wurin aiki, kuma duk kauyen da aka kai shi sai mu ji an ce abun ya tashi a can, don haka hukumomin tsaro su ji tsoran Allah su yi iyakar iyawarsu wajen yin adalci yadda doka ta kasa ta ba su.
Aminiya: Gwamantocin jihohi suna ba rundunar ‘yansanda tallafi na kudade, meye ra’ayinka a kan wannan?
dansadau:  Babu shakka gwamnatocin jahohi na ba rundunar ‘yansanda kudade wanda gwamnati tarayya ba ta iya ba su, amma kwaliya ta ki biyan kudin sabulu, don haka ni shawara ta ga gwamnoni su daina ba ‘yansanda kudi, idan matsalarsu ta fetur ce ko Gas ta samar da inda za a rika ba su, haka shi ne maslaha, tunda suna karkashin gwamnatin tarayya ne, sai ita ta ba su,ita kuma jiha ta yi ayyukan ci gaban al’ummarta.
Aminiya: A matsayin ku na mutanen kauyen da ake wannan ta’asa ko hukuma da jami’an ‘yansanda sun taba tuntubarku don neman yadda za a kawo karshen wannan annobar?
dansadau: A’a, tunda nake babu wata hukuma ko ‘yansanda ko ta karamar hukuma  ko Jiha da gwamnatin tarayya da ta taba neman wani taimako ko shawara wajenmu don kawo karshen wannan al’amari, sai dai mu mu nemi taimako wajensu, amma idan da gaske ne cewa gwamnati na son ta kawo karshen wannan ta’asar, mu muna da mutane da za su iya kawo mana labarin hanyoyin da za a bi wajan magance wannan matsalar.
Aminiya: Mene ne shawararka ga gwamnatoci da jami’an tsaro?
dansadau: Shawarata ita ce, shugabanin  kananan hukumomi da na Jiha da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su ji tsoron Allah su kare rayukan al’umma, kuma su daina yawo da hankalin mutane, don bai yiwuwa a ce yau shekaru biyu ana kashe mutane a Jihar Filato da Kaduna da nan Zamfara da wadansu jahohin a ce an gaza gano wadanda suke wannan ta’asar, hankali ba zai dauki wannan ba. don haka alhakin wadannan hukumomin ne da jami’an tsaro su gano masu ta’addancin nan a hukunta s u a bainar  jama’a.