Sakamako, jadawali da wainar da ake toyawa a Carabao Cup

Manchester United ta kai zagaye na hudu, bayan cin Crystal Palace 3-0 a Old Trafford ranar Talata.

Sakamako, jadawali da wainar da ake toyawa a Carabao Cup

A shekaranjiya Talata da kuma jiya Laraba ce aka fafata wasannin zagaye na uku na gasar Kofin Carabao Cup wanda kungiyoyin Ingila 92 masu buga (Firimiya, Championship, League One da League Two) ke kece-raini.

Ita dai wannan gasa wadda aka soma ta shekaru 63 da suka gabata wato a shekarar 1960, tana daya daga cikin manyan gasannin Ingila uku bayan Kofin Firimiyar da Kofin FA.

Ana gudanar da gasar ce a sama da zagaye bakwai, a tsarin siri-daya-kwale, wato wasa guda-guda ke nan a kowane zagaye inda duk kungiyar da ta bari dama ta subuce mata sai dai ta tara kakar wasanni ta gaba.

A bisa wannan tsari, duk wasan da aka tashi kunnen doki, dole ne a yi bugun fanareti domin kungiya daya ta zarce zagaye na gaba. Sai dai a kan bai wa kungiyoyin da suka kai zagayen daf da na karshe damar buga wasanni biyu gida da waje.

Ana kuma buga wasan karshe ne na Carabao Cup a filin wasa na Wembley a karshen mako (ranar Lahadi).

Tukwicin lashe Carabao Cup

Duk kungiyar da ta lashe gasar tana karbar kyautar fam dubu 100, (£100,000) yayin da wadda ta zo ta biyu ke samun fam 50,000, wanda ake ganin kudin bai taka kara ya karya ba ga kungiyoyin da ke kan gaba, idan aka kwatanta da kyautar fam miliyan 2 na gasar cin Kofin FA, uwa uba kuma idan an kalli lagwadar da ake samu ta lashe Kofin Firimiya.

Wainar da aka toya a bayan nan

A halin yanzu, mai rike da kofin, Manchester United ta kai zagaye na hudu, bayan cin Crystal Palace 3-0 a Old Trafford ranar Talata.

Tun kan hutu United ta ci kwallo biyu ta hannun Alejandro Garnacho da kuma Casemiro a wasan zagaye na uku a kofin.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Anthony Martial ya kara na uku da ya kara tabbatar da United zuwa zagayen gaba.

Wannan nasarar kwarin gwiwa ce ga kungiyar Old Trafford, wadda ta fara kakar nan da kasa taka rawar ganin da take fata tun farko.

Bayan fitar da jawalin zagaye na hudu na Carabao Cup a daren Laraba, Manchester United za ta kara da Newcastle, wato ke nan za a maimaita fito-na-fiton da suka yi a wasan karshe na bara.

Ga dai yadda sakamakon wasannin zagaye na uku na Carabao Cup ya kaya:

Salford City (0 — 4) Burnley

Exeter City (1 — 0) Luton Town

Ipswich Town (3 — 2) Wolves

Mansfield Town [2 (3) — 2 (1)] Peterborough (fenareti)

Bradford (0 — 2) Middlesbrough

Port Vale (2 — 1) Sutton United

Man United (3 — 0) Crystal Palace

Liverpool (3 — 1) Leicester City

Blackburn Rovers (5 — 2) Cardiff City

Lincoln City (0 — 1) West Ham

Chelsea (1 — 0) Brighton

Bournemouth (2 — 0) Stoke City

Brentford (0 — 1) Arsenal

Aston Villa (1 — 2) Everton

Fulham (2 — 1) Norwich City

Newcastle (1 — 0) Man City

Ga jadawalin zagaye na hudu na Carabao Cup:

Jadawalin zagaye na hudu na Carabao Cup

A yayin da rage kungiyoyin 16, Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila FA ta ce za a yi gumurzun fidda gwanayen zagaye na biyar a ranar 30 ga watan Oktoba mai kamawa.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja