Sakamakon masu yin zalunci bijirewa!
Komai ya yi tsanani maganinsa ya zo daf da shi.
Idan masu mulki suka zama azzalumai sakamakon abin shi ne wasu daga cikin wadanda aka zalunta za su bijire masu, wani lokacin hakan kan kai ga yin juyin mulkin soji.
Allah (SWT) Ya haramta wa kansa yin zalunci, kuma Ya ce mu ma kada mu yi zalunci. Idan zalunci ya yi tsanani a tsakanin al’umma musamman a tsakanin masu mulki da wadanda ake mulka (talakawa), canjin mulkin yana daf da faruwa!
- Tsadar kudin rajista ya kusa korar rabin daliban jami’a —ASUU
- An rufe Masallacin Juma’a kan rikicin limanci a Legas
Komai ya yi tsanani maganinsa ya zo daf da shi “Fa inna ma’al usri yusra. In nama al’usri yusra!” Gaskiya da adalci su ne suke tabbata!
Tarihi ya nuna, da can sarakuna ne masu mulki, sojoji da ’yan sanda da kotuna da alkalai da kurkuku da duk wasu ma’aikatan hukumomi duka suna karkashinsu ne.
Haka ikon bayar da kasa (filaye) da izinin ginawa da karbar haraji da jangali duk suna a karkashin kulawar sarakunan har zuwa wani lokaci da suka fara yin zalunci sai Allah Ya kau da su, ya kwace mulkin daga hannun azzaluman sarakunan, Ya mai da mulkin gaba daya a hannun talakawa.
Aka wayi gari kusan ko’ina a duniya ’ya’yan talakawa ne talak suke yin mulkin musamman a Afirka bayan Turawan mulkin mallaka sun yi nasu mulkin zaluncin Allah Ya kau da su.
Bayan sarakunan sun rasa mulki suka ci baya ana kiran su sarakunan gargajiya maimakon na addini.
Sai kuma ga shi su ma talakawan da suka samu gindin zama a mulkin sun saki layi, sun bar Allah sun shiga yin tsafe-tsafe da camfe-camfe suna yin irin nasu zaluncin, su ma Allah Ya kau da su daga mulkin.
Sojojin da suke cikin daji suka yi musu juyin mulki. Wasu daga cikin ’yan siyasa da sojoji suka yi wa juyin mulki suka zama tamkar yaran sojojin, wulakantattun yaran sojoji kawalai da duk abin da ba za a rasa ba. Allah (SWT) Ya tsare mu, Ya tsare mana imaninmu da mutuncinmu ya kiyaye mu daga tabewa.
Sai su ma sojojin da suka yi wa farar hula juyin mulki suka zama barayi, suka jefa talakawa a cikin shaye- shayen miyagun abubuwa masu sa maye da hauka. Suka shiga yin fyade da kisa da sata. Har suna yi wa junansu juyin mulki daga soja zuwa soja.
Komai ya fara rikice wa masu mulkin, sojoji da farar hular da sarakunan.
Ashe duk sun hada baki ne da Turawan mulkin mallaka suna ta sace mana arzikin kasa (gurbataccen mai da gwal da lu’ulu’u da sauran albarkatun kasa da Allah Ya arzuta mu da su domin bukatun dukkan al’ummar kasashen namu.
An rasa wanda zai binciki wani daga cikinsu har a kai ga kwato wa kowa da kowa hakkinsa, a hukunta barayin shugabannin namu a bainar jama’a.
Kamar yadda Allah Ya yi umarni a hukunta dukkan masu fasadi a bayan kasa irin su ’yan fashi da makami da ’yan fashi da mukami da aka samu da aikata laifi, bayan an kwato dukiyar da barayin shugabanni suka sace, an bai wa kowa hakkinsa, an biya diyyar rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini da aka lalatar a kasa.
Allah ba zai taba barin bayinsa kacokan a karkashin azzalumai, fajirai, barayi, ’yan kungiyar asiri da kabal, matsafa, munafukai, makiya Allah, makiya bayin Allah ba.
Duk lalacewar duniya ba a rasa na Allah. Idan mu da aka yi wa sata da zaluncin mun farka sai mu fara da tuba ga Allah Mahaliccin kowa da komai kan Ya gafarta mana dukkan zunuban da muka yi na fili da na boye.
Mu kuma daina aikata alfasha da munkari da zalunci da sharri da sauran laifuffukan da suke jawo fushin Allah, har Ya jarrabe mu da irin wadannan miyagun shugabanni.
Mu roke Shi Ya gafarta mana, Ya zama gatanmu, Ya ba mu ikon canjawa da hannayenmu, Ya yi mana jagoranci, har mu samar da adalan shugabanni masu imani da tsoron Allah da tausayin bayin Allah da mutunci, ba irin wadanda muke da su da babu wata ta alama ta yin imani da Allah da Annabi (SAW) da ranar Lahira da hisabi da wuta da Aljanna a tare da su ba.
Ba abin da suka sani sai sata da kisa da fyade da yin garkuwa da mutane da shaye-shayen hodar Iblis da ganyen wiwi da miyagun kwayoyi da fasikanci.
Shugabannin da suke wasa da nauyin da aka dora musu na tsaron rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini su farga, domin ko iyayen gidansu da suka yi mana mulkin mallaka ba haka suke yi a kasashensu ba.
Allah Ya tsare mu daga sharrin dukkan makiya Allah da bayin Allah na kwarai. Amin summa amin.
Alhaji Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Noma ta Jihar Kano, za a iya samun sat a: 08023106666, 08060116666.