Sakamakon rashin godiya
An yi wani dan kasuwa sunansa Bala Yana da mata da ’ya’ya biyu. Suna da rufin asiri daidai gwargwado. Sannan kuma Allah Ya ba su wata kaza wacce take yin kwai kullum. Wani abin mamaki da burgewa da daukar hankali shi ne kazar tana yin kwan gwal ne. Bala sai ya rika ganin kazar na […]
An yi wani dan kasuwa sunansa Bala Yana da mata da ’ya’ya biyu. Suna da rufin asiri daidai gwargwado. Sannan kuma Allah Ya ba su wata kaza wacce take yin kwai kullum. Wani abin mamaki da burgewa da daukar hankali shi ne kazar tana yin kwan gwal ne. Bala sai ya rika ganin kazar na bata masa lokaci, yana so ya samu dukkan kwayayen da take yi.
Ran nan sai ya yanke shawarar yanka kazar don ya kwashe dukkan kwayayen da ke jikinta. Washegari, kazar ta yi kwai kamar yadda ta saba. Don rashin godiya da hadama da kuma gaggawa, sai Bala ya samu wuka mai kaifi, ya yanka ta, ya fede ta zai kwashe kwayayen. Amma sai ya yi mamaki da ya ga jini ne cike a cikin kazar, kuma babu ko kwai daya.
Sai aka wayi gari, kwayayen da yake samu kullum a rana ya rasa su. Sakamakon rashin godiya da hadama da rashin tawakkali ya sa shi ya fada wani hali na talauci. Kullum talaucin sai karuwa yake yi har ya tsiyace. To kun ga in mutum ya kasance mai hadama da kuma rashin godiya zai wayi gari kadan din ma da yake samu sai ya rasa.
Ina fatan Manyan Gobe za su yi amfani da wannan labarin don su zama masu godiya musamman ma ga iyaye. Saboda duk wanda yake da dogon buri idan bai yi hattara ba zai fada cikin halaka. Sai makon gobe in Allah Ya kaimu.