Sakamakon zaben shugaban kasar Laberiya

Shugaban Hukumar Zaven Laberiya (NEC) Jerome Korkoya ya fara sanar da sakamakon zaven shugabancin qasar da ya wakana a ranar Talata da ta gabata Ya zuwa yanzu, shugaban hukumar ya sanar da samakon mazava 1,232 cikin 5,390 daga shiyyoyi 14. Sakamakon da aka sanar ya nuna cewa tsohon xan wasan qwallon qafa George Weah ne […]

Sakamakon zaben shugaban kasar Laberiya

Shugaban Hukumar Zaven Laberiya (NEC) Jerome Korkoya ya fara sanar da sakamakon zaven shugabancin qasar da ya wakana a ranar Talata da ta gabata

Ya zuwa yanzu, shugaban hukumar ya sanar da samakon mazava 1,232 cikin 5,390 daga shiyyoyi 14.

Sakamakon da aka sanar ya nuna cewa tsohon xan wasan qwallon qafa George Weah ne ke kan gaba a shiyyoyi 11 cikin shiyyoyi 15 na qasar. Shiyyoyin da George Weah ke gaba sun haxa da Grand Kru, Sinoe, River Gee da Grand Gedeh.

Na kusa da George Weah shi ne mataimakin shugaban qasar na yanzu, Joseph Boakai, wanda ke kan gaba a shiya xaya kacal.

A tsarin zaven qasar, ana buqata mutum ya samu kashi 50 cikin xari na quri’u kafin ya lashe zaven. Idan babu wanda ya samu wannan kason, sai a sake zave a karo na biyu.

Shugaban hukumar ya yi kira ga jama’a da su guji yaxa jita-jita, inda ya buqai a jira su kammala haxa sakamakon zaven, sannan su sanar da kansu.