Sakar gizo-gizo ta lalata tankunan motocin Suzuki dubu 19
Kamfanin kera motocin Suzuki na kasar Japan, sakar gizo-gizo ta toshe tankunan man motocin Sedan da ya kera, al’amarin da ya tursasa kamfanin yi wa motoci dubu 19 kiranye, a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2013. Wannan amtsala da ta auku ta haifar da bulewar tankuna, tare da haifar da gobara, a cewar kamfnain.Bisa la’akari da […]
Kamfanin kera motocin Suzuki na kasar Japan, sakar gizo-gizo ta toshe tankunan man motocin Sedan da ya kera, al’amarin da ya tursasa kamfanin yi wa motoci dubu 19 kiranye, a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2013. Wannan amtsala da ta auku ta haifar da bulewar tankuna, tare da haifar da gobara, a cewar kamfnain.
Bisa la’akari da wannan al’amari da ya auku, kamfanin ya yi alkawarin sake ankunan da gizo-gizon ya lalata ko ma ya sake bututun zukar mai ya kewaya da su dungurungum.
Sai dai kamfanin na Suzuki bai bayyana irin gizo-gizon da ya haifar musu da matsalar ba, amma a shekarun baya an taba samun irin matsalar dorawan gizo-gio, wanda gubarsa ke hura wuta a tankunan ababen hawa.
Shigen irin wannan matsala da Kamfanin Suzuki ke fama da ita, taba aukuwa ga Kamfnain Mazada a shekarar 2011, inda kamfanin ya yi wa motoci dubu 65 kiranye a Amurka da Kanada da Mekziko.