Sakar wa ’yan kasuwa mara ne mafita a Najeriya – Aliyu Mustapha

Me ya ba ku sha’awa kuka shirya wannan fim kan matsalar Boko Haram? Na farko dai Najeriya ba kanwar lasa ba ce babbar kasa ce, ba kasar da mutanen duniya za su zauna su manta da ita ba ce, Najeriya muhimmiyar kasa ce da kasashen duniya suke da sha’awa ainun a kan abin da ke […]

Sakar wa ’yan kasuwa mara ne mafita a Najeriya – Aliyu Mustapha

Me ya ba ku sha’awa kuka shirya wannan fim kan matsalar Boko Haram?

Na farko dai Najeriya ba kanwar lasa ba ce babbar kasa ce, ba kasar da mutanen duniya za su zauna su manta da ita ba ce, Najeriya muhimmiyar kasa ce da kasashen duniya suke da sha’awa ainun a kan abin da ke faruwa a cikinta. Sha’anin Boko Haram abu ne da aka yi shekara da shekaru ana fama da shi, kuma sha’ani ne da ya jawo wa kasar nan asara ta rayuka da ba sa ma kirguwa. Duk da ana cewa mutum dubu 20 dubu meye, Allah kadai Ya san rayukan da aka rasa. 

To Muryar Amurka ta dauki kudiri a kanta yanzu wajen shekara biyu tana kokari ta shirya wannan shiri na musamman, ta nuna wa duniya halin da mutane suka shiga. Ba wai shi kansa yaki ba gadan-gadan, amma hali da kuma tasirin wannan lamari a kan mutanen da ya shafa, musamman mutanen sashin Arewa maso Gabas. Shiri ne da ake kira “Boko Haram: Tattakin Bakar Akida,” da Ingilishi kuma ana kiransa “Boko Haram: Journey for Ebils.”  Shiri ne da Muryar Amurka ta shirya ta kawo domin ta nuna wa mutane wannan hali da mutane suka shiga da kuma nuna cewa mutanen Najeriya suna da jajircewa. Sau da yawa akan ga Najeriya sai ta yi kamar za ta auka cikin masifa, cikin rami, sai ta dawo. To, shi ne babban darasin wannan shirin.

Ku ’yan Najeriya da ke sashin Hausa ne kuka yi tunanin haka ko mahukuntan gidan rediyon?

A’a, mahukuntan  ne, ai wannan shirin ba na Hausa ba ne na Ingilishi ne aka zo aka fasasara shi da Hausa. Saboda shiri ne na Muryar Amurka bakin dayanta, yanzu haka ma ana fassara shi a harsunan duniya kamar Faransanci da Larabci da Swahili da Hindu da sauransu za a rarraba. Ko bayan nan Najeriya da na zo, zan je Jamhuriyyar Nijar insha Allahu domin mu je mu yi wa mutane bayani game da shi.

Bayan ’yan Najeriya sun kalli wannan fim wane mataki kuke so su dauka ko wane darasi kuke son isarwa?

Darasin da muke so mutane su samu shi ne na farko su jinjina wa jajircewar ’yan kasar da lamarin ya shafa. Saboda mun ga tarihin kasashen da dama da suka shiga irin wannan hali na yaki da ta’addanci, mun ga yadda suka karkare. Kuma mun san inda aka fito, saboda haka yanzu Allah Ya kawo sauki, ba a gama da shi ba, har yanzu yana nan. Kuma muna so mu nuna wa ’yan Najeriya cewa kafofin watsa labarai irinsu Muryar Amurka sun damu da halin da suke ciki. Kuma duk da cewa mu ’yan Najeriya ne, galibin wannan aiki wadanda ba ’yan Najeriya ba ne suka yi basirar cewa ya kamata a yi shi. Babban darasin, muna so mu nuna wa duniya cewa Najeriya dai, wallahi ta wahala da wannan hali da ta shiga. Mutane ko sun rayu, suna rayuwa a cikin wahala, saboda haka ya kamata a fahimci Najeriya, a kyautata wa Najeriya, a kuma a taya ta yakin baki daya, shi ne babbar manufarmu.

Wadansu suna ganin kamar cewa kila ko bidiyon nan ya yi sauri ganin cewa har yanzu yakin nan bai kare ba, me za ka ce?

Ai kamar yadda na ce, ba a kan yaki ba ne aka yi fim din, wahalar kuma ba a fita cikinta ba. Yanzu in ka dauki dubbai ko in ce miliyoyin mutane na yankin Tafkin Chadi, wajen mutane miliyan 70 ba ’yan Najeriya kadai ba, ’yan Chadi, ’yan Kamaru ’yan Nijar, duk sun dogara ne a kan noma da kamun kifi. To harkar Boko Haram ta zo ta sanya wa wannan birki, ba a iya yi. Ai kuwa in ka ce mutum bai iya sana’a, ma’ana bai iya ciyar da iyalinsa ke nan, in kuwa bai iya cin abinci ka san wahala ta zo ke nan, sun rasa rayuka. To ba yakin ba ne, yakin kowa ya san bai kare ba, ana nan ana yi, amma an san an ci karfin yakin. Amma kafin a ci karfin yakin sai da aka wahala, amma mutane sun jure wa wannan wahala, shi ne ake son fitowa da shi fili.

Mu koma kan kungiyarku ta Zumunta da ke Amurka, wace rawa ta taka a kan wannan lamari na Boko Haram?

Ka san kungiyar nan ni ne shugabanta na farko na kasa baki daya. Ni ne shugabanta na farko na Washington DC. Mu ne muka fara dauko manyan shugabannin Najeriya irin su Allah Ya jikansa Sarkin Kano Ado Bayero, su Allah Ya jikansa Maitama Sule da sauran manyan shugabannin Najeriya. Tun wadancan shekaru har yanzu ba mu daina wannan ba. Na biyu fiye da shekara 20, cikin natsuwa ba da ma mutane sun sani ba, har kwanan gobe ’ya’yan wannan kungiya suna bayar da tallafin karo ilimi kyauta ga ’yan Arewa. Duk jihohin 19 har rokon jihohi muke yi su ba mu yaran da za mu ba su sukolaship kuma yana nan har yanzu ba mu daina ba. Na uku, har yanzu mutanenmu suna zuwa Najeriya su haka rijiyoyin burtsatse, ina ba ka ’yan ayyukan da suke yi ne tukuna. 

Ta fannin wannan yakin da ake yi, ka san duk sana’ar da za ka yi tunani a kanta a duniyar nan, akwai dan Najeriya da ke yi a Amurka, kuma ga tarin yawan da suke da shi a Amurka, saboda yawan ’yan Najeriya, har siyasa suke shiga a Amurka. Na san Magajin Gari dan Najeriya da aka taba yi a wajejen Jihar Oregon. Kuma zaben nan da aka yi na su Donald Trump, ’yan Najeriya da yawa sun tsaya takara, musamman ma mata, wajejen su New York da sauransu. Suna ba da tarbace na wajen rubuce-rubuce, suna ba da tarbace na kudade, suna ba da tarbace na hada tarurruka, suna ba da tarbace wajen bayar da shawarwari da sauransu. Duk abin da ka ga ’yan gida suna yi gwargwado, su ma a can suna yi. Kuma wallahi abin yana ci musu rai cewa kasar tana cikin wannan hali.

Kasancewa bayar da tallafin karo ilimi na cikin ayyukanku, wane yunkuri kuke yi don tallafa wa marayun da yakin Boko Haram ya samar?

Wato in muka tashi bayar da sukolaship din nan mukan tuntubi jihohi ne alal misali mu ce su kawo mana mutum goma-goma, ba lallai sai wadanda wannan lamari ya shafa ba. Kamar yadda na fada maka su wadannan yankuna ba mu tsaya kan tallafin ilimi ba, muna bayar da taimako na kudi, muna bayar da taimako na magunguna, muna ba da kwamfutoci da yawa na karatu. Ni kaina na taba zuwa da kwamfutoci da yawa aka rarraba wa jami’o’i da yawa a Kaduna. Saboda haka kokarin da muke yi tare da sauran kungiyoyi na ’yan Najeriya da suke Amurka shi ne iya gwargwadon abin da za mu iya yi, kuma muna ci gaba da yi.

Zuwa yanzu yaya girman nasarar da kuka samu daga lokacin da ka shugabanci kungiyar?

Na fa daina shugabancin.

Amma kana halartar tarurrukanta ko?

kwarai kuwa.

To wasu nasarori kake tsammanin kun samu?

Na farko a wurina nasara ta farko ita ce,har yanzu muna nan tare a kungiyar. Ka san yadda kungiyoyi ba su dadewa musamman na ’yan Najeriya. Bai wai ba mu da kalubale irin na sauran kungiyoyi ba ne, amma abin alfahari a wurina shi ne cewa kungiyar nan ta Zumunta ita kadai ce kungiya da take wakiltar dukan Arewacin Najeriya. Amma in ka taba kungiyoyin ’yan Kudu suna da kungiya sun fi 500. Kowane kauye yana da kungiya, amma ta Arewar nan daya ce. Kuma ka san yadda tsarinta yake ita ma tana da kabilu da yawa. Wannan ita ce nasara ta farko.

Ta biyu, kulawar da aka bai wa sha’anin ilimi.

Ta uku, mun fuskanci wahalhalu, kuma abin takaic ne muna fuskantar wahalhalu, shi ne kokarin da muka yi na dibar ’yan kasuwarmu mu kai su Amurka mu hada su da na can, domin tarurrukan da muka shirya irin wadannan ba sa da iyaka. Ko kafin in taso, tunanin da ake yi shi ne a kira ’yan kasuwa na Najeriya ba ma na Arewa ba. Don an sha daukar dawainiyar haka, saboda abin na Najeriya ne gaba daya. Saboda duk lokacin da ake bikin samun ’yancin kai kungiyarnu tana taka rawa. 

Sannsn wata nasarar da muke samu ita ce ta bunkasa al’adunmu na gida. Kafin in so a Jihar Maryland an yi wani taro saboda sun san mu duk wanda zai yi wani taro zai zo ya ce, suna gayyatarmu, musamman in taro ne na kasashe, saboda so su ga abincinmu su ga kayanmu na sawa, suturarmu, musamman na mata. Kade-kadenmu da wakokinmu da sauransu, kuma a zo a yi su a burge. Mutanen Amurka suna son al’ada kwarai da gaske, komai tsadar kwat da za ka sa, rigar jamfa mafi araha ta fi ta kima a idonsu. Wa za ka burge da kwat? Kuma in ka sa kwat ba a sani ina ka fito.

A karshe wane sako kake da shi ga al’ummar Najeriya kan yadda za su bunkasa ilimi, ganin ku da kuke waje kun damu da shi?

Wato bari in gaya maka matsalarmu ta kasar nan tamu, komai ya doru a kan gwamnati ce. Gwamnati ce ke dauke da kashi 99 cikin 100 na lalurorin rayuwar yau da kullum ta Najeriya. In ba ka sha’ani da gwamnati ma a Najeriya ba kai ko’ina. Yanzu dubi rigimar da ake yi a Kaduna kan malaman makaranta, wai ba sa iya cin jarrabawar da ’yan firamare ma suke yi. Ina abin kunyar da ya kai haka. Kuma gwamnatin da ake cewa za ta kore sui ta ce za ta sake daukar wadansu.  A Turai, cinka da shanka da ruwanka ba ruwan gwamnatin da su, kai ko a harkar watsa labarai in baya ga gidan rediyonmu duk Amurka gwamnatin ba ta rediyo ba ta da talabijin ba ta da jarida ko daya. Duk abin da ka gani mutum yana ci yana sha yana karantawa yana hawa yana meye na wani kamfani ne na masu zaman kansu. 

Mai kamfanin wutar nan in ka biya shi ya ba ka wutar, in ba ka ba shi ba, ya yanke. Shi kuma idan bai ba ka wuta isasshiya sai ya bar ka ya tafi wani wuri. To kowa yana da inda zai je kuma kowa yana da kishiya. Amma mu nan sha’anin ilimin nan yanzu makarantar da ka yi da wadda na yi, lokacin da muka yi su sun fi inganci da yanayin yau. Wane irin lalaci ne wannan? Gada nawa ka sani a kasar nan wadda har yanzu tana nan irin wadda in mota daya ta zo sai ta jira wata ta wuce? Amma ka ji irin kudaden da ake wabta na da lokacin kasafin kudade. 

Lokaci ya yi da ya kamata a karfafa wa mutane masu zaman kansu su samu dama su gudanar da wasu daga cikin ayyukan nan. Harkar wutar nan tun shekara nawa ake batunta amma har yanzu, abin kunya ne ga Najeriya a ce har yanzu wuta matsala ce. Na je Burkina Faso, wadda in ka duba jerin gwanon kasashe a harkar tattalin arziki ita ce kusan ta karshe, wallahi har na bar ta sau daya na ga wuta ta yi dil-dil, ita ta tsaya ba a dauke ba. Don haka a ba mutane dama a yi jari-hujja shi ke nan.