Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota
Har yanzu gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da rasuwar ba.
Sakataren Gwamnatin Jihar Ondo, Temitayo Oluwatuyi, ya rasu a ranar Asabar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ya rasu ne sakamakon matsalolin da suka biyo bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi makonni biyu da suka wuce.
- An kashe mutum 9 an jikkata 4 saboda biskit a Jigawa
- Shugabannin Arewa na haifar da rabuwar kai wajen zaɓen ’yan takara – Kwankwaso
Duk da haka, har yanzu gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa kan rasuwar ba.
Wata majiya mai tushe ya shaida wa Aminiya cewa, Oluwatuyi ya rasu a wani asibiti a ranar Asabar.
“Abin baƙin ciki ne, mun rasa shi yau. Likitoci sun yi iyakar ƙoƙarinsu don ceto shi amma ya rasu,” in ji majiyar.
Gwamna Lucky Ayedatiwa ya naɗa Mista Oluwatuyi a matsayin sakataren gwamnati a ranar 24 ga watan Janairun 2024, bayan yin sauye-sauye a gwamnatinsa.
Mamacin ya taka muhimmiyar rawa wajen sake zaɓar Aiyedatiwa a zaɓen gwamnan jihar na ranar 16 ga watan Nuwamban 2024.
Rasuwarsa ta girgiza ɗaukin Akure, yayin da mutanen suka dinga ɗaura alama a gidajensu don alhinin rasuwarsa.