Sakataren Ilimi ya kalubalanci iyaye kan tura ’ya’ya makaranta

Sakataren Ilimi na karamar Hukumar Birnin Kebbi Alhaji Umaru Suru, ya jawo hankalin iyayen yara su daina yaudarar kansu, su tashi tsaye wajen ganin ’ya’yansu suna zuwa makaranta kodayaushe.Sakataren ya bayar da wannan shawarar ce a lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa bayan ya gama rangadin gani-da-ido a makarantun firamare da ke karamar […]

Sakataren Ilimi ya kalubalanci iyaye kan tura ’ya’ya makaranta
Sakataren Ilimi ya kalubalanci iyaye kan tura ’ya’ya makaranta

Sakataren Ilimi na karamar Hukumar Birnin Kebbi Alhaji Umaru Suru, ya jawo hankalin iyayen yara su daina yaudarar kansu, su tashi tsaye wajen ganin ’ya’yansu suna zuwa makaranta kodayaushe.
Sakataren ya bayar da wannan shawarar ce a lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa bayan ya gama rangadin gani-da-ido a makarantun firamare da ke karamar hukumar.
Alhaji Garba Suru ya ce, lokaci ya yi da iyayen yara za su daina nuna halin ko-in-kula da ilimin ’ya’yansu.
Ya ce idan haka ya ci gaba, babbar matsala ce iyaye suka sanya kasar nan, domin a nan gaba ba za a samu ingantattun masu jagoranci ba ke nan.  Ya ce, ya zama wajibi iyaye su rika bincikar takardun karatun ’ya’yansu domin su san irin kokarin da suke yi a makaranta.
Sai ya yi kira ga malaman makarantun firamare na yankinsa su ji tsoron Allah su gudanar da aikinsu na koyarwa, kamar yadda suka dauki alkawari. “Domin malami ba ya da wata hujja na rashin zuwa wurin aiki, saboda gwamnati tana biya su dukkan hakkokinsu ga kuma albashi mai tsoka,” inji shi.