Sake fasalin kananan bankuna don ci gaban sashin na gaskiya
Kananan bankuna a duniya wata dabara ce ta rage talauci ta hanyar bayar da karamin bashi da samar da hanyoyin samun kudi ga magidanta da daidaikun mutane ko gungun jama’a don tallafa musu su kara kudin shigarsu ko gudanar da wani kasuwanci ko rage radadin talauci ko kuma samar da ayyukan yi. Lamarin kananan bankuna […]
Kananan bankuna a duniya wata dabara ce ta rage talauci ta hanyar bayar da karamin bashi da samar da hanyoyin samun kudi ga magidanta da daidaikun mutane ko gungun jama’a don tallafa musu su kara kudin shigarsu ko gudanar da wani kasuwanci ko rage radadin talauci ko kuma samar da ayyukan yi.
Lamarin kananan bankuna batu ne wanda ya samo asali shekaru aru-aru. Kananan bankuna suna bayar da dama ta samun bashi ga magidanta da masu karamin karfi da ke birane da karkara.
Saboda haka masu fashin baki suka bayyana cewa dalilin da suka sanya kafa kananan bankuna shi ne tallafa wa talakawa su rage radadin talauci da kuma kasawar cibiyoyin kudi na magance matsalar bukatar kudi ga talakawa da gungun masu karamin karfi. Amma har yanzu kananan bankuna kimanin 903 da ke Najeriya ba su cimma wannan buri ba saboda tsadar kudi da kuma rashin tsarin kasuwanci na zamani wanda ya sanya suke gudanar da ayyuka da tsada wanda hakan yake janyo kudin ruwa mai yawa ga abokanen huldar da suka karbi bashi wanda ya kai kashi 30 cikin dari.
Da yake jawabi a bitar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shirya karo na 21 ga manema labarai kan hada-hadar kudi da Editoci a Jihar Gombe, Daraktar Bangarorin Sanya Ido Kan Hada-Hadar Kudi na Bankin CBN, Misis Agnes Tokumbo Marthins ta nuna karara cewa kananan bankuna ba su nuna za su iya tallafa wa ci gaban tattalin arziki ba.
Da take tantance dokokin kananan bankuna ta ce “Akwai abokan hulda na kananan bankuna kimanin miliyan takwas.”
Ta bayyana cewa cikin kanana da matsakaitan kasuwanci miliyan 37 da Cibiyar Kididdiga ta Kasa da Hukumar Bunkasa Kanana da Matsakaitan Sana’o’i da Masana’antu (SMEDAN) suka tantance kimanin miliyan 36 masu kananan kasuwanci ne kuma kimanin miliyan daya ne suka samu damar samun bashi.
Saboda haka ne Gwamnan Bankin CBN, Mista Godwin Emefiele kwanan nan ya ce sabon karamin bankin NIRSAL da aka kafa zai samar da bashi ga kananan ’yan kasuwa da tsarin kudin ruwa mai taki daya na kashi biyar cikin dari.
Karamin banki na kasa wani tsari ne da kwamitin bankuna suka bullo da shi, da Tsarin Raba Asara da Hukumar Aika Wasiku ta Kasa.
Kwamitin Bankuna sun samar da su ne suka samar da jari kuma su ne suke da kashi 50 cikin dari na bankin yayin da Tsarin Bankin NIRSAL da Hukumar Aika Wasiku suke da kashi 40 cikin dari da kuma kashi 10 cikin dari.
Babban Bankin CBN ne ya kafa Bankin NIRSAL don ya taimaka wajen samar da kudi da harkokin kasuwanci a bangaren noma ta hanyar dakile asarar kasuwancin amfanin gona.
Da yake karin bayani kan Karamin Banki na Kasa, Gwamnan Bankin CBN ya bayyana cewa ana sa ran sabon karamin bankin na kasa zai fadada duk wata damarmaki da karfafa kananan kasuwanci a Najeriya.
Ya bayyana cewa abin da ake son a cimmawa shi ne a kafa rassansa a kananan hukumomi 774 a kasa baki daya, ya kara da cewa a yanzu an kafa rassa bakwai kacal tare da kafa rassa hamsin a nan gaba.
Gwamnana ya ce za a bayar da bashin ne ga kasuwanci kamfanin gona da kanana da matsakaitan kamfanoni a kashi biyar cikin dari na kudin ruwa inda za a biya cikin shekaru bakwai da kuma shekaru biyu.
Kwamitin Bankuna ne suka ware kudin a taronsu na karo 331 a ranar 9 ga watan fabarairun shekarar 2019 don bunkasa samar da kudi ga kanana da matsakaitan kamfanoni musamman wadanda suke masu zaman kansu.
Don a cimma samun nasarar aiwatar da shirin dukkanin bankunan ajiyar kudi sun amince su ware kashi biyar cikin dari na ribar da suka samu bayan ware haraji na shekara don tallafawa wani aiki da ke karkashin shirin.
Emefiele ya ce “Babban kalubalen da kananan ’yan kasuwa suke fuskanta shi ne samun bashi kuma ina farin ciki da kafa wannan karamin bankin wanda zai kasance mai reshe daya akalla a kowace karamar hukuma 774 na kasa baki daya. Za mu samu cibiyar kudi wacce za ta taimaka wajen zurfafa harkokin kudi ta baidaya tare da sanya ta mai sauki ga jama’a wajen samun bashi musamman kanana da mutanen da ba sa harkoki da bankuna saboda kodayaushe muna cewa wadannan ne suke da rauni. Za mu yi amfani da wannan don bunkasa samun bashi inda kudin ruwan zai kasance na kashi biyar cikin dari inda bashin zai kasance na tsawon shekaru bakwai da kuma shekaru biyu”.
Dangane da batun jingina, Emefiele ya ce za a bayar da basuka ba tare da jingina ba.
Ya ce “Mun san wadanda suke da rauni kamar wadanda ba su iya samun bashi babban batun shi ne saboda sun kasa bayar da jingina”.
Da yake bayani kan irin shirin da aka yi, Shugaban Hukumar Aika Sakonni na Kasa, Adebisi Adegbuyi ya bayyana cewa ana gudanar da gyare-gyare a wurare hamsin wadanda za a bude kafin karshen watan Afrilu.
Da yake bayyana rawar da Hukumar NIPOST za ta dauka a sabon tsarin ya ce “Har yanzu ba a fahimci muhimmancin ofishin aiki sakonni ba dangane da bunkasar tattalin arzikin kasa. Muna kokarin yin amfani da wurarenmu guda dubu daya da dari takwas wajen wannan tsari don samar da ragin kashi kudi da kuma rage yawan kudi”.
Da yake jawabi dangane da batun, Shugaban Bankin NIRSAL, Mista Aliyu Abdulhameed ya bayyana cewa miliyoyin ’yan kasuwa ne da kananan manoma za su amfana da bankin a kasa baki daya.
“Wannan manufa da wannan dabara ta Karamin Banki na Kasa za su mayar da hankali wajen amfanar mutane da dorewar tallafawa kananan ’yan kasuwa a kasa baki daya da rayukan miliyoyin ’yan Najeriya da suka dogara da su,” inji shi.
Ya bayyana cewa akwai rassa 37 masu daraja ta ‘A’ a jihohi 36 har da Abuja. Rassa 73 suna daraja da ‘B’ dillalai ne za su gudanar da su a fiye da wurare 664.
Bankin NIRSAL yana son cimma abokan hulda dubu 500 tare da tsammanin damawa da abokan hulda miliyan biyu a shekara daya daga watan Janairu na shekarar 2019.
Wani babban kwararre kan tattalin arziki, Paul Alaje ya bayyana wasu daga cikin alfanun tsarin. “Abin da kanana da matsakaitan ’yan kasuwa za su samu jari don bunkasa kasuwancinsu zai magance matsalar jari ga kasuwancin da suke da samun ciniki mai yawa amma ga ’yan kasuwar da ba sa samun ciniki mai yawa ba abu ne mai kyau ba”.
Ya bayyana cewa “Tunda ba jingina a cikinsa kuma za a biya cikin shekaru biyu ya sanya shi zama mai sauki. Zai bunkasa kanana da matsakaitan kamfanoni da yawa. Za a samu riba mai yawa wajen riba da bunkasa da samar da ayyukan yi. Abun alheri ne. Ya zama wajibi Bankin CBN ya gaggauta daukan matakan aiwatar da wannan shiri”.
Darakta Janar na Cibiyar Bunkasa Al’umma da Kasuwanci ta GLOCHEED, Misis Rose D.S Gyar ta ce “Kudi ne mai arha ga kanana da matsakaitan kamfanoni amma kuma yaushe za a same shi, yaushe za a kai ga shi, wane lokaci, kuma ta yaya zai dore? Kamar yadda suka kafa banki muna neman a sanya mata a ciki da wadanda ke fama da nakasa da masu cutar zabiya don daidaitawa da damawa da kowa da kowa da samun bashi baki daya,” inji shi
Da take karin bayani Misis Marthins ta ce “Za mu yi aiki tukuru don cike gibi idan ba haka ba duk yadda muka yi kokarin bunkasa bangaren masu zamankansu ba za samu sakamakon da ake bukata ba”.
Da take yi wa manema labarai karin bayani ta ce “Ya zama wajibi mu yi amfani da damarmu wajen hada kai don kara kaimi kan wannan shiri, inji ta.