Sake Fasalin Kasa: Sakkwato da Kebbi da Zamfara sun goyi bayan tsarin raba iko
’Yan Jam’iyyar APC na jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara sun amince su goyi bayan tsarin raba iko tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin kasar nan. Sun bayyana cewa kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta bar wa jihohi bangaren lafiya da sufuri da kashe gobara ita kuma ta mayar da hankali kan tsaro da harkokin kasashen […]

’Yan Jam’iyyar APC na jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara sun amince su goyi bayan tsarin raba iko tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin kasar nan.
Sun bayyana cewa kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta bar wa jihohi bangaren lafiya da sufuri da kashe gobara ita kuma ta mayar da hankali kan tsaro da harkokin kasashen waje da kudi.
Wannan shi ne matsayar da jihohi uku na jam’iyyar APC da ke Arewa maso Yamma suka cimma a taron jin ra’ayin jama’a da aka yi a jihar Sakkwato.