Sake Fasalin Najeriya: Tsokaci, kalubale da al’amuran dubawa (3)
An samu lokaci mai tsawo, masana da ma gama-garin mutane suna ta kai-kawo game da batun sake fasalin Najeriya. Dangane da wannan batu, kwararre kan al’amuran mulki, masanin al’adu da zamantakewar al’umma, marubuci, DOKTA BUKAR USMAN OON ya yi nazari, sannan ya gabatar da bunkasasshen tsokaci. Ga kashi na uku kuma na karshe, kamar haka: […]
An samu lokaci mai tsawo, masana da ma gama-garin mutane suna ta kai-kawo game da batun sake fasalin Najeriya. Dangane da wannan batu, kwararre kan al’amuran mulki, masanin al’adu da zamantakewar al’umma, marubuci, DOKTA BUKAR USMAN OON ya yi nazari, sannan ya gabatar da bunkasasshen tsokaci. Ga kashi na uku kuma na karshe, kamar haka:
Wani abin lura kuma dangane da wannan kururuwa ta sake fasalin kasa shi ne, duk da cewa akwai jihohi da yawa a kasar nan, wadanda ba su iya rike kansu ta fannin tattalin arzki, amma akwai wasu mutane ko kuma kungiyoyin mutane da ke ta hankoron ganin an sake yanka masu yankunansu, an ba su jihohi. A yayin Taron Tattauna Batun Tsarin Mulki da aka gudanar a 2014, an samar da sunayen sabbin jihohi 18 da aka bukaci kirkirowa, kuma masu neman sabbin jihohin nan da gaske suke wannan hankoro, ba tare da gajiyawa ba. Bisa lura da wannan yanayi, akwai bukatar bangarorin nan biyu su samu daidaito bisa abin da suke muradi – masu bukatar ganin an sake karkasa Najeriya zuwa jihohi da kuma masu muradin ganin an ba Lardi-Lardi cin gashin kai a Gwamnatin Tsakiya.
Babu shakka an samu tambayoyi da dama da ke bukatar amsa, dangane da wannan batu na sake fasalin kasa, amma abin takaici, amsoshin na da wuyar samuwa. Don haka, idan dai batun ci gaba ake bukata ga kasa, to bai kamata a koma tsarin mulki irin na baya ba, wato wanda ya yi tashe a shekarun 1960. Irin wannan batu ba zai taba tasiri ba a yanzu, sai dai a bar shi kawai a matsayin tunanin jiya, domin kuwa ba za a iya dawo da tsarin jiya a yau ba. Kawai abin da ya kamata a yi dangane da batun sake fasalin kasa shi ne, a tsaya a yi nazarin yanayinmu, da halayenmu, mu kawo canji a kawunanmu dangane da abin da ya shafi al’amuran mulki, sannan masu tafiyar da mulki su gudanar da abin da ya dace da ci gaban al’umma da rayuwarsu. Za mu iya cewa an kusa shiga birni, ba a yi hangen dala kadai ba dangane da wannan kiraye-kiraye na sake fasalin kasa. Albishirin nasarar haka ya bayyana ne, ganin cewa mutane sun fahimta da muhimmancin kasancewar Najeriya kasa daya, maimakon daidaicewar bangarorinta. Don haka duk wani korafi na neman wani hakki daga al’ummar kasar daban-daban, za a fi tattauna shi da kawo fa’ida a matsayin kasa daya mai ’yanci.
Najeriya dai kasa ce hamshakiya, wacce Allah Ya kaga, Ya yi mata albarkar arziki iri daban-daban kuma za a iya gudanar da mulkinta cikin adalci da tsafta tun daga sama har kasa. Akwai tsananin bukatar a kula da al’ummar kasa, a daukaka hanyoyin bunkasa rayuwarsu. Hakan ba zai samu ba, dole sai an ririta arzikin da Allah Ya ba mu ta hanyoyin da suka dace.
A yayin da ake da bukatar shugabannin yanzu su mike tsaye wajen samar da nagartattun ayyuka da halayyar mulki abin koyi da adalci, akwai kuma bukatar a shiga aikin fadakar da matasa da kimsa masu halayyar kishin kasa, a nuna masu illar son kai da hadama. Ta haka za a samar da zaman lafiya da raba-daidai a tafiyar da mulki sannan kuma kasar ta bunkasa cikin hadin kai da ci gaban al’umma.
Madamar aka samu canjin halayya zuwa nagartatta daga al’ummar kasa, Tsarin Mulkin 1999 zai iya samar da abin da ake so na ci gaban kasa. Ba kamar yadda ake kushe shi ba, wannan kundin fa ba aikin mutum daya ba ne. Aiki ne na hada-ka, wanda ya tattaro ilimi da nazarin masana da suka bi zaryar tarihin gudanarwar kasar nan tun daga 1914, lokacin da aka hade sassan kasar nan zuwa dunkulalliyar kasa guda daya. Akalla idan mun duba, akwai kundayen tsarin mulki guda bakwai da aka samar a kasar nan kafin na 1999. ’Yan Najeriya da dama da suke raye a yau shaida ne yadda aka yi ta saka su cikin kwamitocin tattaunawa don samarwa ko sake fasalin tsarin mulki a zamanin mulkin soja.
Wani dalili da ya haddasa ake ta batun sake fasalin kasa shi ne yadda wasu ke ganin cewa Gwamnatin Tsakiya iko ya yi mata yawa, don haka ake ganin akwai bukatar rage mata iko zuwa jihohi, musamman ma ta fannin rarraba dukiyar kasa. Sai dai kuma kada a mance abin da ya haddasa Gwamnatin Tsakiya ta samu wannan karfi da iko, wanda ba zai rasa nasaba da kiraye-kirayen ’yan Najeriya ba a shekarun 1960, inda suka rika cewa Lardi-Lardi sun kasance masu karfin iko fiye da Gwamnatin Tsakiya, don haka ya kamata a rarraba su. An saurari wadannan kiraye-kiraye, inda aka biya bukatun yankunan, domin tabbatar da hadin kan Najeriya.
Akwai bukatar Najeriya ta ci gaba kuma hakan ba zai samu ba idan aka tsaya kullum ana waiwayen baya, ana sukar tsare-tsaren mulki da kuma gwamnatoci. Bisa wannan batu, babu makawa a yarda da nazarin Mista Simon Kolawole, wanda kamar a harzuke ya bayyana cewa: “…Mun kasa cin ma matsaya ta yadda za a lalubo hanyar ciyar da kasar nan gaba, an kasa samun hadin kai saboda dalilai daban-daban. Wasu kawai saboda jahilci, sun yanki hanya marar bullewa, wasu saboda rudewa, wasu saboda muradin kansu na siyasa, wasu kuma saboda neman suna a saukake, wasu saboda halayyarsu ta tsattsauran ra’ayi, wasu kuma haka nan kawai ba tare da wani dalili ba.” (Jaridar Thisday, Nuwamba 12, 2017, shafi na 88). Babu shakka bai kamata a dora wa tsarin mulki laifin matsalolin kasar nan ba. Koda ’yan Najeriya sun samar da sabon Kundin Tsarin Mulki kuma suka zabi a ci gaba da tafiyar da shi a irin yanayin da kasar take, babu abin da zai canja.
Ga wani batun kuma, shin bahallatsar cin hanci da rashawa da almundahana da satar dukiyar gwamnati da son kai da hadama da danniya da babakere da suka yi katutu a kasar nan da dadewa, shin suna daga cikin kundin tsarin mulkin kasar nan ne? Ko kadan, babu abin da ya haifar da su sai kasawar dan Adam na kin bin doka da oda. Haka kuma, yadda ake jinkirin aiwatar da shari’a a kotuna, shi ma ba tsari ne da ke cikin kundin mulki ba, haka ma batun munakisha da ojoro ko aringizon kuri’a a lokacin zabe, duk ba su cikin tsarin mulki. Suna faruwa ne a sanadiyyar karya dokokin kasa. Kamar ma’aikacin da ya sana’anta kayansa ne marasa inganci, idan an yi magana sai ya ce laifin kayan aikinsa ne, ba shi ba. Don haka duk inda aka je za a dawo, matsalolin kasar nan ba za su kau ba, dole sai an samu canjin halayya daga shugabanni da mabiya. Don haka matsalar ba ta sake fasalin kasa ko tsarin mulki ba ce.
Mun kammala