Sake Fasalin Najeriya: Tsokaci, qalubale da al’amuran dubawa (2)

An samu lokaci mai tsawo, masana da ma gama-garin mutane suna ta kai-kawo game da batun sake fasalin Najeriya. Dangane da wannan batu, qwararre kan al’amuran mulki, masanin al’adu da zamantakewar al’umma, marubuci, DOKTA BUBAR USMAN OON ya yi nazari, sannan ya gabatar da bunqassashen tsokaci. Ga kashi na biyu, kamar haka:   A qoqarinsu […]

Sake Fasalin Najeriya: Tsokaci, qalubale da al’amuran dubawa (2)

An samu lokaci mai tsawo, masana da ma gama-garin mutane suna ta kai-kawo game da batun sake fasalin Najeriya. Dangane da wannan batu, qwararre kan al’amuran mulki, masanin al’adu da zamantakewar al’umma, marubuci, DOKTA BUBAR USMAN OON ya yi nazari, sannan ya gabatar da bunqassashen tsokaci. Ga kashi na biyu, kamar haka:

 

A qoqarinsu na ganin cewa an mance da tsarin mulkin Lardi-Lardi kuma ba a samu damar dawo da shi ba, masu adawa da tsarin sun kai matuqa wajen nuna rashin amincewa da duk wani tsari da ake ganin yana qunshe da shi. Duk wata kadara da tsohon tsarin ya samar sai da aka yi rabon gadonta, duk da cewa a wajen rabon wasu lokutan sai da aka kai ruwa rana, tsakanin jihohin da aka qirqiro. Wasu kamfanoni ko cibiyoyin kasuwanci mallakar tsoffin lardunan, kamar Kamfanin Zuba Jari Da Bayar Da Lamuni (IICC), Kamfanin Bunqasa Gabashin Najeriya (ENDC) da Kamfanin Bunqasa Arewacin Najeriya (NNDC) da jihohi suka gada sai aka murqushe su, aka hana su kudaden gudanarwa, don haka aka bar su suka mutu, wasu kuma suka zama a daidaice.

Mutanen da ke hayagagar cewa a qirqiro “Hukumomin kula da tattalin arzikin larduna,” a yayin sake fasalin Najeriya, ya kamata su waiga baya su tantance makomar irin wadannan hukumomi da aka samar a baya, wato irin su IICC, ENDC, NNDC, Hukumar Bunqasa Yankuna Masu Arzikin Mai Da Albarkatun Qarqashin Qasa (OMPADEC) da sauransu, sannan kuma su tantance abin da ke faruwa a Hukumar Bunqasa Yankin Neja-Delta (NDDC). Haka kuma ya dace a duba yadda Hukumomin Raya Koguna suka riqa gudanar da al’amuransu. A kwankin baya ma an amince da kafa sabuwar hukuma domin bunqasa Arewa Maso Gabas. Don haka idan ta fara aiki kuma aka ga ta samu nasara, kila al’umma su aminta da alfanun kafa hukumomi irinta. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko mutanen da ke son sake fasalin qasa za su yi jimirin jiran tabbatuwar haka?

Abu ne mai kyau kuma ya dace daga lokaci zuwa lokaci a riqa waiwayar yadda ake tafiyar da al’amuran mulkin qasa, domin gane ko ana kan daidai ko akasin haka, amma tabbas babu dacewa ko kadan a ce a yau za a dawo da tsarin mulkin Najriya zuwa irin na 1963, kai har nan gaba ma bai dace a yi haka ba. Tabbas, Najeriya ta jima wajen fuskantar sauye-sauye daga wannan tsarin mulki zuwa wancan, tun daga 1963 zuwa yau. Na farko dai yawan al’umma ya qaru, kayayyakin gona da hanyoyin samun kudin shiga duk sun canja fasali. Abin da kawai bai canja ba sosai shi ne adadin fadin qasa, idan ka cire dan bangaren da aka miqa wa Jamhuriyyar Kamaru (Bakassi). A bangaren rayuwar al’umma da hauma-haumar siyasa kuwa, su ma sun fuskanci gagaruman canje-canje. Idan aka yi la’akari da wadannan sauye-sauye, matsattsun takalman da Najeriya ta saka a 1963 ba za su shiga qafarta ba a yanzu, balle kuma Najeriyar gobe. Idan ka debe shauqin da masu yekuwar neman sake fasalin qasa ke da shi a kan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1963, duk wasu abubuwa da suka shafi tsarin gudanarwar qasa ba za su iya dacewa da wancan fasali na 1963 ba a yau. 

Babu mamaki, kila la’akari da cewa ba zai yiwu a maida Najeriya zuwa tsarin gudanarwar 1963 ba, kuma da lura da cewa tsarin da ake kai bai da tasiri, su suka sanya masu son sake wa qasar nan fasali suka ba da shawarar a bi tafarkin qirqirar Yankuna Shida a qarqashin Gwamnatin Tarayya, tsarin da ake da shi a yanzu. A yayin shirya Kundin Tsarin Mulkin 1999, an bijiro da wannan batu na komawa tsarin Lardi-Lardi, amma aka yi watsi da shi. Haka kuma, an bijiro da shawarar cewa a mayar da shiyyoyin qasar nan shida zuwa wasu Qananan Gwamnatocin Tarayya, a yayin da sauran jihohi za su zama a qarqashin kulawarsu, su kuma shiyyoyin za su zama suna da jakadu a qasashen waje, kamar dai yadda tsarin yake a lokacin Mulkin Turawa. Wannan tsarin yana da matsala, akwai wata manaqisa a tattare da shi, don haka ya kamata a wancakalar da tunaninsa.

Idan za mu iya tunawa, lokacin da aka qirqiro sabbin jihohi daga Lardi-Lardi, ’yan Najeriya sun amince kuma sun yi ta murna da haka, don haka ba zai yiwu ba ma mutum ya yi tunanin al’umma za su amince kai tsaye da a qwace masu ’yancin jihohinsu su koma qarqashin kulawar larduna. Idan kuwa haka ta faru, to za a haifar da sabbin rikice-rikice, musamman ma kowace jiha za ta riqa kokowar ganin cewa an zabe ta a matsayin babban birnin lardin shiyyarta. Shin anya kuwa qasar nan ta shirya daukar wannan dawainiya, ta gina sabbin hedikwatoci da sauransu?

Za mu kammala makon gobe